Skip to content

Chapter 10

Chapter 10

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

a kan cinyarta. “Main neend mehsoos nahi kar raha, isi liye Immi” (Bana jin baccin ne, shi yasa Immi) Shi ma ya amsa mata da Urdu ɗin. Ta shafa sumar kansa da take a nannaɗe, saboda style ɗin curl ɗin da aka mata, dan babu wani aski da yakewa sumar tasa bayan top curly, kuma iyaka tsakiyar kan ne yake tara gashi, gefe da gefen da kuma ta baya aske shi ake. “Laish manak na'asan?” (Me yasa ba ka jin bacci?) Wannan karon da larabci ta tambaye shi. Dan duka yaren biyu babu wanda ba sa ji shi da Gulzar, kasancewar Urdu shi ne yaran ƙasarta Pakistan, duk da yana kamanceceniya da Hindi. Amma asalin yarenta Urdu ne, larabci kuma shi ne yaren mahaifinsu, hakan yasa duka yarikan biyu sun iyasu. “Bas haik Immi” (Haka kawai Immi) Ya bata amsa da larabcin shi ma. “Arman!” Ta kira sunansa tare da sumbatar sumar kansa, sai ya lumshe idonsa yana amsawa. “Umm” “Me yasa ba ka son faranta mana ta hanyar yin abin da muke so ni da Abby?” Tambayar tata tasa ya buɗe idonsa. “Immi ba zan iya yin shugabanci ba. Saboda ina da nakasa...” “Shiiiiii!” Immi ta yi saurin dakatar da shi, sannan ta sa hannu ta tura sumar kanta bata. “Na san cewa kana da halayen da kai kanka ba lalle ace ka san kana da su ba... A ƙalla ma'aikata ashirin ne ke aiki a gidan nan. Amma cikin mutum ashirin ɗin nan ba na jin akwai guda ɗaya da ka taɓa tozartawa, kuma ban taɓa gani ko jin sanda ka saka wani cikinsu aikin da ba za su iya ba. A wasu lokutan ma kana yin ayyukan da ya kamata ace su ne suke yi, kuma kana ɗaukansu a matsayin abokai. Duk da a ƙasanka suke aiki, ko ni da Gulzar sukan koka damu a wasu lokutan, amma ban da kai Arman. Hakan yasa na gane cewa ɗana shugaba ne, shugaba ne da zai iya jan ragamar masarauta ba iyaka Majmu'at Shirkat Alhadi kaɗai ba. (Alhadi Group of Companies)...” Kamar yanda ya saba shiru a kan maganar da ba shi da amsarta haka yau ma ya yi shiru, dan ba ya jin zai iya ce mata wani abin kuma... *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai* IVANA POV. Zaune take a kan kujerar falo, ta lanƙwashe ƙafarta ɗaya a kan kujerar da take zaune, ɗayar ƙafar tata kuma na ƙasa, sanye take da casual palazzo trouser, me ɗauke da zanen dogayen layin baƙi da kore, sai baƙar tube top. Gashin kanta na cikin style ɗin halp up- halp down. Idonta a kan Tv, tana kallon wani show da ake haskawa a Wanash tv. Yayarta Hala mahaifiyar Imran na zaune a gefenta suna kallon shirin tare. “Ivana waye saurayin da Imran yace min kuna tare da shi a Miracle garden?.” Ta ji tambayar a bazata, dan sam ba ta yi zaton tambayar ba, kanta ta juyo ta kalli Hala, sannan ta ɗage kafaɗunta tana barbaza gashin kanta dake kwance a gadon bayanta. “Uwais Fazil! Haka yace min sunansa” Hala ta gwalalo ido tana kallonta. “Kada ki ce min jinin masu kamfanin Al Aida ne?” Ivana ta tattare naman goshinta cikin mamakin saiyawar yanayin Hala lokaci guda. “Eh shi ne. Mi ye wani abu na musamman a kasancewarsa jinin ahalin?” Ta tambaya. Hala ta yi dariya. “To idan ba ki sani ba na sanar da ke. Kin ga girman kamfanin baban abokinki Arman? To da kaɗan zai faɗawa Al Aida girma. Kuma idan har kamfanin Iƙbal Alhadi zai zama na farko cikin jerin manya-manyan kamfanunuwa a Dubai to Al Aida zai zamo na biyu!” “Waye bai san wannan ba to?... Ni ban ga wani abin birgewa a nan ba!” Ba ta kai ga rufe bakinta ba wayarta ta shiga ruri. Da ta duba kuma sai ta ga lambace babu suna, ta ɗauka da niyyar ba za ta ɗaga ba. “Ya kamata ki ɗaga, dan ba ki san wani alkairi ne yake shirin faruwa da ke sanadiyyar kiran ba” Cewar Hala, kuma a lokacin Yumma da ta tafi sama wankewa Imran rigarsa da ya ɓata suka sauƙo ƙasa tare da Imran ɗin. Dan haka Ivana ta ɗauki wayar ta yi sama, har Yumma da Ivanan ta raɓa ta wuce na binta da kallo, saboda saurin da take. Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar, sannan ta kalli screen ɗin wayar, lokacin da kiran yake shigowa a karo na biyu. Sai da ta tsaya nazari na wasu sakanni, kafin ta ɗaga kiran. “Marhaba (Hello)” Ta faɗa tana lasar lips ɗinta, a lokaci guda kuma ta ɗora hannunta a kan ƙugunta. “Ahalain (Hii)” Tun da ta ji muryar ta gane waye. Amma abin mamakin shi ne, a ina ya samu lambarta?. Wa ya ba shi? Me yasa ya kirata. “Uwais Fazil ke magana” Ya sake faɗa daga ɗayan ɓangaren, jin ta yi shiru, Ivana ta zauna a bakin gadonta tana faɗin. “Na gane ai” “Good to ya kike?” “Ina lafiya, da fatan kai ma haka” “Ni ma ina cikin ƙoshin lafiya da amincin rai da zuciya!” Amsar da ya bata ta sa ta yi murmushi. “Na kiraki ne mu gaisa... Saboda tun bayan waccan ranar da muka rabu nake ta tunani da burin sake haɗuwa dake” “Wani abu ne na musamman haka da ya faru a haɗuwarmu ta farko da har zai sa ka yi marmarin sake haɗuwa da ni?” Ta tambaya. “Ke kanki ta musamman ce, ballantana kuma aje ga kalamanki na nutsuwa, yanayin yanda kike magana, yanayin da kike tafiya, da duk wani abu da ya shafeki na musamman ne” A wannan karon murmushi ta yi me faɗi, har haƙwaranta na bayyana. “Kin yarda ke nan? Tun ga shi har kina murmushi” Sai ta rufe bakinta, tana mamakin yanda aka yi ya san ta yi murmushi, tun da murmushin ba me sauti ta yi ba. “Zan sauƙa daga kan layi. Ina fatan sake haɗuwa da ke” “Sai anjima” “Na gode da lokacinki” Uwais ya sauƙe wayar, a lokacin da mahaifiyarsa ta shigo katafaren falon gidansu. Murmushi ta yi tana kallon ɗanta, tana zama kusa da shi ya kama hannunta ya sumbata. Ita kuma ta shafa kansa tana sanya masa albarka. “Da wa kake waya? Ko yarinyar da zata zama sirikata ce?” Ya faɗaɗa murmushinsa yana kallon mahaifinsa da shi ma ya shigo falon. “Ai da gani ba sai an faɗa ba. Tun da kika ga yana yin irin wannan murmushin.” Mahaifinsa Inayat Fazil ya faɗa yana nasa murmushin. Ƙudsiyya mahaifiyarsa tace. “Wace ce?” “Wata ce” Ya basu gajeriyar amsar yana kwasar wayoyinsa, sannan ya bar living arean yana murmushi me kama da dariya. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. Tsaki ya ja yana ci gaba da danna system ɗinsa, sakamakon binciken wurin da ya kamata ace ya je ya ɗauki hotunan da aka saka shi da yake. Amma ya shafe sama da awa uku bai samu wurin da ya kwanta masa ba. Arman dake zaune a gefensa yana cin tuwon da Maama ta ba shi ya ce. “To wai duk wannan tsakin da kake wa mutane na miye?” Adam ya juyo ya kalle shi, sai lomar tuwon shikafa miyar kuka yake, kamar wani bahaushe,

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35