Chapter 22
Chapter 22
sa ya tsafaceta, ya sauya mata tunani da kuma alƙibila. Ya mayar da ita karen farautarsa, domin ko yaƙi zai je tare da ita yake tafiya. A cewar bokansa idan har ta ci gaba da zama a matsayin me ba shi kariya babu wani mahaluƙin da ya isa ganin bayansa. Duk da ita sam Daneen Asran ba ta so, domin yana juya mata tunani da hankali ne kawai. Ya mayar da ita jaruma, domin kaf cikin su ukun babu wanda ya kaita iya sanin salon yaƙi da kuma faɗa, Daneen Sanah ita ce kawai za ta iya kaita a wurin sanin makamar yaƙi, domin ita ma jaruma ce ta gaske. Ta ƙarshen kuma ita ce Daneen IQRAH, wadda ita ce ta kasance zinariya a 'ya'yansa, domin ita ko faɗa da koyon yaƙi bai bari an koya mata ba, a cikinsu ita ce shalele, ita ce wadda aka shagwaɓa da gata da kuma riritawa irin ta 'ya'yan Sarauta, hakan ya sa ta zamto gimbiyar ta gaske. Duka yaran Malik Changaz babu wadda bai tsaface ba, su duka ukun suna da ƙarfin tsafi a jikinsu, musanman ma Asra, domin ita nata ya fi na kowa, ita kuma Iqra ba ta da shi sosai, domin ba ta cika amfani da shi ba. Yayin da na Sanah ya zame mata alaƙaƙai, domin a halin yanzu so take ta rabu da shi, amma ta kasa, saboda ta hanyarsa Changaz yake aiko mata da jinya iri-iri. A cewarsa yana hukuntata ne a kan laifin da ta aikata na bijire masa... “...Waɗannan su ne masarautu da kuma sarakunan da suke mulkin wannan duniyar a wannan lokacin” A lokacin da ya kai ƙarshen dogon tambihin nasa Adam ya fashe da kuka yana dafe kansa, dan tun da ya fara jin labarin ya san cewa shikenan kuma, shi tasa ta ƙare, domin ba makawa sai ya mutu a cikin wannan duniyar. Ita ko Ivana hawaye ne suka soma zubo mata, na tunawa da Yumma, Hana da Imran, da kuma Uwais, dan ta fara tunanin shikenan ta yi bankwana da su. Arman ne ya daure ya sake tambayar tsohon. “Ya za'ayi mu koma gida?” Ya sake nanata tambayar da ya yi ɗazu. Tsohon ya nisa, sannan yace. “Na san abin da zan faɗa yanzu zai firgita ku fiye da zato... Wannan ƙofar dake cikin masarautar Malik Changaz ita ce ƙofar da za ta mayar da ku gida!” Arman ya rintse idonsa, domin da ma shi ne abin da yake hasashe. “Ta ya za'ayi mu buɗe ƙofar da ba'a taɓa buɗeta ba?” Ya sake yin ƙarfin halin yin tambayar, a wannan karon dattijon murmushi ya yi, sannan ya nuna Arman da ɗan yatsa. “Wannan sarƙar da ke wuyanka, ita ce makullin ƙofar!” Ivana da Adam dake kuka suka dube shi baki buɗe, shi kansa sai da ya yi mamaki, sannan ya kai hannu ya taɓa mukullin dake jikin sarƙar. “Kana nufin wannan?” Adam ya tambaya yana nuna sarƙar, datijjon ya jinjina musu kai. Cike da ƙarfin hali Arman ya miƙe tsaye. “Zan je, kuma zan fuskanci Malik Changaz, zan tabbatar da na buɗe wannan ƙofar, domin mu koma gida.” “Ka yi hauka ne Arman? Saboda kai sirikinsa ne sai ka je ka ce masa ya buɗe maka ƙofar kai da abokanka za ku koma gida, ai ku matafiya ne, kun ɓata a hanya, saboda shi kuma shashashan afirilu ne sai ya matsa ya baka ƙofar cike da girmamawa?...” Faɗin Adam yana miƙewa, sannan ya nuna shi da ɗan yatsa. “Yanzu fa ba a 21st century muke ba, mun dawo zamanin baya ne, zamanin da ake kisan wulaƙanci a kan mulki! Zamanin da uba zai kashe ɗansa a kan mulki. Mutumin da bai ƙyale 'ya'yansa na cikinsa ba shi ne zai ƙyale mu saboda mu ba daga zamaninsa muke ba? Ka yi tunani mana!” Arman ya yi shiru kawai, a idonsa yake hango wahala tare da tarin ƙalubalen da za su fuskanta kafin cimmawa komawa gida. Ya kalli Ivana. “Ivana shin kin yarda da ni? Ivana na goge hawayenta ta gyaɗa kanta har sau biyu, ya juya ya kalli Adam. “Adam ka yarda da ni?” “Na yarda da kai amm...” Ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Eh ko a'a?” Adam ya jinjina kai. “Na ɗauki alƙawarin tunkarar Malik Changaz, ko da kuwa zai kasheni, ruwa, iska sanyi ko guguwa ba za su dakatar da ni ba wurin cimma hakan. Tabbas zamu fuskance shi, idan ta kama zan yaƙe shi, domin mayarda ku gida, zan sadaukar da raina domin ku rayu, na ɗauki wannan alƙawarin, kuma babu abin da zai dakatar da ni wurin cika shi....” _The game starts now!🔥_ Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-9 “Wannan shi ne kaɗai abin da zan iya taimaka muku da shi” Cewar datijjo me ban al'ajabi yana miƙawa Arman wata takarda dake naɗe, wadda aka yi ta da fatar akuya. Kansa ya juya ya kalli Adam da Ivana dake tsaye a gefe, kowannensu goye da jakarsa, dan sun ɗauki ɗamarar tafiya yanzu ba sai anjima ba. Hannu ya sa ya karɓi takardar, kafin ya buɗe takardar tsoho ya soma faɗin. “Wannan ita ce taswirar da za ta nuna muku hanya...” Adam da Ivana suka matso suna kallon taswirar da Arman a buɗe. “Duk wata hanya ko daji da kuka ga a kan takardar nan sai kun bi shi, za ku tsallake abubuwa masu tarin yawa a hanya, ban ce babu ƙalubale ba, ban kuma ce akwai zallar wahala ba, ban ce babu farin ciki ba, kuma ban ce akwai baƙin ciki ba... Abu ɗayaa na sani, hi ne kafin ku kai ga gaci za ku sha baƙar wahala!” Su duka uku suka dubi juna, kafin Adam yace. “Mu da za mu nufi Masarautar Jiyad me ya haɗa hanyar mu da Masarautar Majdal?...” Ya tambaya domin ya ga zanen sunan masarautar a cikin taswirar cikin harshen larabci. Dattijo ya yi murmushi. “Har Mamlakatul Afsah sai kun je, babu buƙatar na faɗa muku ta yaya kuma yaushe ne hakan zai faru, wata ƙila hakan zai rage muku armashin tafiyar, na tabbatar nan da wani lokaci ku da kanku za ku bani labarin abin da ya faru daku idan Allah ya nufi saduwarmu da ku a nan gaba, sannan akwai wani abu gudu...” Ya ɗan yi fasali yana shafa farin dogon gemunsa, sannan ya ci gaba da faɗin. “Ƙauyen Askar shi ne ƙauye na farko da za ku fara shiga bayan kun bar nan, tafiyar dake tsakanin nan da garin a ƙalla ta kai kwana uku a ƙafa, idan kuma a doki ne kwana ɗaya da yini ɗaya... Abu mafi muhimmanci shi ne mutumin da za ku haɗu da shi a can. A farkon garin akwai wani ɗan ƙaramin gidan ƙasa, nan za ku fara shiga, idan har kun shiga za ku iske wata tsohuwar mata, sai ku bata wannan taswirar, daga zarar ta ga taswirar ita za ta sadaku da abokin tafiya!” Suka yi shiru, domin duk cikinsu babu me abin faɗi kuma, tun da har rayuwa ta yi JUYIN KWAƊO da su sun riga sun karɓi hakan a matsayin ƙaddara. Tsoho ya ɗauko wata jaka ya miƙawa Adam, Adam ya sa hannu ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35