Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,200 words 0 views Progress saved
Download Book

Kafin wata guguwa ta shigo cikin kasuwar, sannan ba ta sauƙa a ko ina ba sai kan rufin wani shago. Kaɗan-kaɗan iskar ta fara raguwa, har ta ɗauke gaba ɗaya. Yayin da wannan guguwar ta rikiɗa zuwa wata doguwar budurwa. Sanye cikin baƙaƙen kaya, ta yi kitso guda biyu a kanta, tsayin jelar kitson har cinyoyinta. Fuskanta kuma a rufe yake, a hankali ta yi tsugunnon mage a kan rufin shagon, sannan ta shiga baza idonta a kan mutanen dake kai kawo... Dan iskar da ta taso ba ta sa kasuwancin da ake gudanarwa ya dakata ba, sautin murmushin da ta yi ya fito tare da motswar ƙyallen da ta rufe fuskarta da shi, domin ta hango abin harinta, ci gaba ta yi da bin sawunsa, har ta ga sanda ya shiga wani loko da take da tabbacin babu kowa ciki. Take ta ɓace daga saman shagon, kuma ba ta bayyana a ko ina ba sai a cikin lokon, sannan a gaban mutumin da take bibiya. Shi kansa mutumin da ya ganta sai da ya razana, hakan ya sa kayan dake hannunsa suka zube a ƙasa, ya ɗaga hannayensa sama kamar me laifi. A wannan karon budurwar dariya ta yi, sannan ta buɗe fuskarta, kyakkyawar fuskarta ta bayyana gare shi, haƙika tana da kyau, amma kyawun ɗan maciji. Lokacin da ya ganeta bai san sanda ya saki fitsari a wando ba, jikinsa ya soma kyarma, domin ganin NATILA na dai-dai da ganin mutuwar mutum. “Sannunmu da sake haɗuwa, Malam Ayyaz!” Jikin Ayyaz na rawa ya shiga ja da baya yana son bata haƙuri, cikin wani irin sauri da ya ɗararma hankali ta isa gabansa, sannan ta saka hannayenta ta riƙe wuyansa. “Dole na kasheka, sannan na ciro zuciyarka na kaiwa shugabana, na masa alƙawarin sadaukar masa da zuciyarka a daren yau!...” Ta ƙarashe maganar wasu zaƙa-zaƙan fiƙoƙi na fitowa daga haƙwaranta na sama. Sannan ta kafasu a wuyansa, nan take Ayyaz ya fara shure-shure, amma Natila ba ta saki wuyansa ba sai da ta zuƙe fiye da rabin jinin jikinsa. Duk da haka ba ta ƙyale shi ba, da ta saki wuyan nasa ta ɗaga hannunta me yalwar dogayen farata, ta caka a ƙirjinsa, sannan ta ciro zuciyarsa, kana ta saki gangar jikinsa ta faɗi ƙasa. Zuciyar dake riƙe a hannunta ta kalla, bakinta duk ya ɓaci da jinin jikinsa, ta sa bayan hannunta goge bakin nata, sannan ta sake rufe fuskarta, ta tsallake gawarsa ta ɓace a iska. Salma Ahmad Isah ✍️ ___________ _😳 Akwai matsala!_ _Ko su waye suka kama ADVENTURERS ɗinmu?. Shin ya za a yi su kuɓuta?_ _Batun wannan Natilar! Ya kuke ganin haɗuwarta da ADVENTURERS ɗinmu za ta kasance?._ _Book 1 ya kusa ƙarewa, dan haka ya kamata a fara biyan kuɗin book 2 tun yanzu._ 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172704. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-13 ADVENTURERS. Kukan Adam shi ne ya cika ɗan ƙaramin akurkin da aka cusasu ciki, dan duka su huɗun tare da wata mata da ba su santa ba na cikin wani abu me kamar keji, yayin da mutanen da suka kamosu ke zaune kusa da kejin, sun yi ayari suna gabatar da bautarsu zuwa ga wutar da suka hura, domin sun lura cewa mutanen wuta sukw bautawa. Kuma bayan hasken wutar babu komai a wurin sai na farin wata da ya samu zarafin ratsowa ta jikin ganyen bishiyoyin da suke a ko ina na dajin, sai kuma na fitilun wayoyinsu da suka kunna. Tun bayan da mutanen suka kama su ba su musu komai ba, kuma ba su ce da su komai ba, sai kallonsu da suke ta yi tun ɗazu, kamar za su cinyesu. “Mi shan Allah Adam skut! (Dan Allah Adam ka yi shiru!)” Cewar Ivana cikin rarrashi, Adam ya goge hawayen da yake, yana duban Arman dake wurga masa harara, shi kuma Uwais kallonsu kawai yake yana murmushi, dan kukan da Adam ɗin ke yi dariya yake son ba shi. “Ki bar ni na yi kuka, wata ƙila wannan shi ne kukana na ƙarshe, daga shi kuma ba zan sake ba!... Saboda waɗannan abubuwan yanka mu za su yi, ko su cinye, ko su bawa dabbobinsu!...” Ya ƙarashe yana jingina kansa da jikin itatuwan da suka kafa kejin. “Idan ba ka mana shiru ba sai na maka duka!” Cewar Arman a ƙufule. Sannan ya ƙara da. “Kalli Ivana, ko ita ba ta yi kuka ba sai kai, ƙaton banza kawai!” Adam ya kame jikinsa yana ƙifƙita ido. A karo na barkatai, Arman ya sake haske matar da suka tarar a cikin kejin da fitilar wayarsa, amma har yanzu tana a yanda suka shigo kejin suka sameta. Dunƙule take a wuri guda, ta haɗa kai da gwiwa, kuma duka jikinta a rufe yake. “Uwais ka tambaya mana wannan matar ko ta san abin da mutane nan suke so!...” Cewar Arman yana gyara zaman glasses ɗinsa. “Da ace za ta faɗa da ta faɗa tuntuni, tun yaushe nake mata magana? Amma ko tari ka ji ta yi?...” Uwais ya ƙarashe da tambaya. Arman ya girgiza kansa yana ci gaba da haska matar, sannan ya ƙura mata ido. A hankali ya fara takawa zuwa inda matar take, yana daf da durƙusawa a kusa da ita, mutumin da suke sa ran shi ne shugaban mutanen da suka kamasu ya furta. “Ku je ku fito da su yanzu mu sadaukar da su ga wutar bautarmu!” Hakan ya sa Arman ya fasa durƙusawa, ya juyo ya kalli abokansa cikin tashin hankali, Ivana ta dubi Uwais, sannan ta dubi Arman, yayin da Adam ya ƙara fashewa da wani sabon kukan yana faɗin sun mutu. Har zuwa lokacin da wasu mutum biyu suka buɗe ƙofar kejin da suke ciki ba su iya taɓuka komai ba, sai da aka gama fito da su daga cikin kejin, har da matar da a yanzu suka lura da cewa fuskarta a rufe take, aka jerasu a gaban wutar dake ciki. “Dan Allah Arman ka yi wani abin!” Cewar Adam cikin kuka. Arman ya lumshe idonsa, yayin da yake lalubo takobin da datijjo ya ba shi a cikin jakar dake bayansa. A lokacin da ya riƙo takobin ya buɗe idonsa, sannan cikin zafin nama ya miƙe tsaye, ya zare takobin yana nuni da shi ga mutanen da suke riƙe abokansa da wannan matar. “Kada ku cutar da su! Ku ƙyalesu!” Ya faɗa yana nuna musu takobin. “Me kuke jira wai? Ku danna min kawunansu a cikin wuta!” Shugaban mutanen ya basu umarni cike da isa, wanda yake riƙe da Adam ne ya riƙo gashin kansa, yana shirin danna kan Adam a cikin wutar Arman ya yi tsallen albarka, ya ɗaga takobin hannunsa ya datse hannun mutumin!. Ƙarar da ya ƙwalla ce ta janyo hankalin sauran mutanen wurin. Sannan kuma ita ta razana sauran da suka ga faruwar lamarin. Sai suka yi saurin ja baya daga jikinsu Ivana, yayin da shi ma Uwais ya yi amfani da wannan dama wurin juya sarewarsa zuwa baka, sannan ya motsa hannunsa ya fito da kibiya, tare da sakata a jikin bakar, shi ma ya nuna mutanen da ita. Adam da Ivana kuma suka yi saurin ɓuya a bayansu, su kuma suka musu

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35