Chapter 4
Chapter 4
ta soma cin abincin tana bata labarin yadda live performance ɗin da suka je suka kalla yau ya kasance. Bayan ta gama cin abinci ta nufi upstairs, dan gaba ɗaya ta gaji bacci take ji, ƙofar ƙaramin ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki tana kallonsa kamar baƙonta. Ɗakin sam ba shi da girma, amma ya ɗauki duka kayanta da take ajewa a ɗakin, akwai gadonta ɗan siriri na kwanciyar mutum ɗaya. Wanda ke ɗauke da baby pink duvet, sannan akwai pillows manya da ƙanana, sannan akwai wardrobe da ba ta cika faɗi ba, akwai kuma desk ɗinta, sannan dressing mirror. Mafiya yawan abubuwan dake ɗakin pink cokor ne, hatta da stikern dake jikin bango pink ne. Miƙa ta yi tana rataya jakar guitar ɗinta a sama, inda ta saba ajeta, sannan ta nufi bathroom, ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, wardrobe ɗinta ta buɗe, ta ɗauki mayafi a ciki, ta yafa a kanta, sannan ta tada sallah a kan center carpet. Sai da ta gabatar da sallahr isha, sannan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa night wear. Tana hamma ta bi lafiyar gado ta kwanta, tana rayawa ranta cewa me ake da rayuwar da babu gadon bacci, ita a duniyarta babu abin da ya fi birgeta sama da lallausan gado, dan ko a kan sofa ba ta iya bacci. _________________ _Ehem! Ehem! Ehem!_ _Salmanians! Ga wata sabuwar tafiya! Me ɗauke da abubuwan ban al'ajabi._ _Tafiyar ba me sauƙi ba ce kamar yanda za ku ɗauka!. Dan haka sai ku shirya da kyau._ _JUYIN KWAƊO zai zo a Book 1 and 2. Book 1 shi ne free, book 2 ne zai kasance paid a kan ₦400_ _Kuma za ku iya samunsa a ArewaBooks, domin akwai complete book 1 a can_ _Sai ku shirya, ku gyara zama, domin jin yanda rayuwa za ta yi juyi da waɗannan abokai uku, kuma juyin ma irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi._ #Bahaɗejia #Candy #SalmaAhmadIsah #JuyinKwaɗo °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-2 *House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.* Gidan na ɗaya daga cikin manya manyan gidajen dake hamshaƙiyar unguwar ta Jumeirah. Dan ko a yanayin gininsa za ka san an kashe kuɗi, ballantana ace ka samu damar kutsa kai ciki. Motar Armaan da ta ɗauko hanya tun daga unguwarsu Adam da ya aje a gida ta faka a gaban gidan. Ya kashe motar, sanna ya cire seat belt ya fito yana jan jakarsa dake a wurin me zaman banza, ya goya jakar a bayansa, sannan ya juya ya fuskanci hamshaƙin gidan. Glasses ɗinsa ya gyarawa zama ta hanyar saka ɗan yatsansa manuniya ya tura bridge ɗin glasses ɗin, sannan ya nufi kyakkyawar ƙaramar ƙofar shiga gidan. Dan gidan ba shi da wani compound, wanna ƙofar ita ce da ka buɗeta za ta sadaka da gidan, hatta da garejin aje motocinsu na daga gefen ƙofar shiga gidan. Hannunsa ya kai kan inda madannan sirrin buɗe ƙofar gidan suke manne a jikin ƙofar, daga gefe kuma door bell ne, wanda aka yi shi domin baƙi, dan idan har ɗan gidan ne babu buƙatar ya danna door bell, tun da duk sun san kalaman sirrin da suke buɗe ƙofar. Lambobin ya saka, nan take ƙofar ta buɗe, ya shiga yana kallon masu aikin gidan dake kaikawo, sanye cikin uniform iri ɗaya. “Haidar!” Ya yafito ɗaya daga cikin masu aikin, Haidar ɗin ya nufo shi yana amsa masa cike da ladabi, Arman ya miƙa masa mukullin motarsa, sannan yace. “Motata tana waje, ka saka min ita a gareji, idan ka saka key ɗin kuma ka aje shi a nan” Ya nuna masa wani abu me kama da basket dake aje kan wani cupboard dake farkon gidan, wanda ya ƙunshi tarin makullan motocin da mutanen gidan ke hawaya. Kuma daga jikin cupboard ɗin ma za ka iya hangen manya manyan motocin dake garejin, dan akwai ɗan glass dake wurin da zai baka damar hakan. Haidar ya karɓi key ɗin, sannan ya nufi ƙofar fita, yayin da shi kuma ya kutsa kai cikin kyakkyawan gidan, bayan wani ɗan gajeren corridorn dake bakin ƙofar shigowa, za ka iske hanyoyi uku, ɗaya ita ce wadda zata sadaka da upstairs, kuma duka ɗakunan kwanan gidan suna sama. Ɗaya kuma ita ce wadda za ta sadaka da living room, wanda yake ƙunshe da sitting areas guda biyu, tare da dinning area, sannan akwai kitchen ta kusa da dinning area. Kuma ta cikin falon za ka fita harabar garden ɗin gidan, dake ƙunshe da swimming pool. A kusa da swimming pool ɗin kuma akwai kujerun zama, wanda aka saka su a ƙasa, kamar dai zurfin swimming pool ɗin, kuma tsakanin wurin da suke da swimming pool ɗin glass ne kawai ya raba, ta yanda kana iya ganin ruwan cikinsa idan kana zaune a wurin. Da farko hanyar da za ta sada shi da upstairs ya nufa, amma sai ya juyo ya fasa bi ta nan, dan ta cikin living room ɗin ma akwai wani stairs ɗin da zai kaika sama. Ya bi ɗayar hanyar da za ta kai shi living room, komai dake cikin living room ɗin gray color ne, daga can dinning area ya hangi mahaifinsa Iƙbal Alhadi, tare da mahaifiyarsa Zahra Ali, zaune suna dinner. Wurin ya nufa yana kallon Imminsu, wadda ita ma ta ankara da shi, yana isa inda take ya sunkuya ya sumbaci kanta, sannan ya kama hannayenta ya sumbata. “Masa'ul khair ya Immi (Barka da yammaci Immi)” Zahra ta yi murmushi tana kallon ɗanta, ta shafa kansa tana amsawa. “Shu wa aina Gulzar?” (Ina Gulzar ne?) Ya tambaya ganin bai ganta tana dinner tare da su ba, Immi ta amsa masa da. “Ab us ne khaana khtm krte dekha aur kamre mein waaps chla gaya” (Yanzu ta gama cin abincinta ta koma ɗaki) “Ɗayib ana rayih (Okay ni ma na tafi)” ya bata amsa cikin harshen larabci, saɓanin ita da ta masa magana da harshen Urdu, ba wai dan bai iya mayar da amsa cikin yaren ba, sai dan ya san ita ma Immin tana jin larabcin. A wasu lokutan ma idan za su yi magana tsakanin su uku sai su dinga haɗa larabci da Urdu, saboda Urdu shi ne harshen Zahra. Ba tare da ya yi wa Abby magana ba ya shiga ƙoƙarin barin wurin, sai dai tun da ya tsaya a wurin shi Abbyn ke binsa da kallo, ya lura da yanzu sam Arman ba ya son masa magana, saboda daga ya masa magana zai tado masa da zancen zama shugaban kamfanin Alhadi. Kuma ya lura da ɗansa ba ya son maganar kamfanin ko abin da ya shafe shi, idan zai iya tunawa ma rabon Arman da kamfaninsu tun shekaru biyar da suka wuce, lokacin da suka yi murnar cikar kamfanin shekaru 30 da kafuwa. A yanzu babban burinsa bai wuce Arman ya zama shugaban Alhadi Group of Companies ba. Domin ba ya so ya mutu ya bar gadon kujerar shugabancin kafanin a hannun ɗan ɗan uwansa Faisal. A cikin halayen arziƙi Faisal ba shi da guda uku ƙwarara, kuma sam bai yi kama da wanda zai zama shugaba na gari ga ma'aikatan kamfanin ba, sannan a ƙa'ida, idan har Arman ya ƙi amincewa da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35