Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

ku riski wannan takardar jirginmu ya tashi. Dan haka kada ku sha wahala wurin naiman inda nake. Na daɗe da sanin shirin da kake a kaina Abby, kuma kamar yanda ka yi hasashe, ba zan taɓa baka kunya ba, babu wanda ya san gaibu, amma ina me tabbatar maka da cewa da ban san da wannan maganar ba da na saka hannu a takardun da za ka bani yau a wurin shagalin ƙara shekarata. Amma kuma tun da na riga na sani ba zan bar hakan ta faru ba Abby, na rasa ta wace hanya ya kamata ace na fahimtar da ku abin da nake son ku gane, na rasa da wani yare zan muku magana dan ku fahimta. Na zaɓi barin ƙasar Dubai ne ba dan komai ba sai dan nisanta kaina daga duk wani abu da ya shafi Majmu'at Shirkat Alhadi. Kuma ina me muku albishir da zan dawo bayan sati ɗaya. Abby kada ka shiga damuwa, Immi kada ki yi kuka, ki min addu'a, Gul kada ki zagi yayanki a kan abin da ya yi na ɗauki wannan hukuncin ne bayan dogon nazari.... Arman Iƙbal Alhadi!”_ Abby na kaiwa ƙarshen karatan takardar ya dunƙuleta a hannunsa, idonsa na sauya kala nan take. “Kai Iƙbal me ya faru?” Jadda ta tambaya tana riƙe shi. Cikin wani hali me kama da abin da ya fi tashin hankali ya kalleta. “Jadda me yasa kika faɗa masa abin da muke ɓoyewa?” Tun da ta ji wannan tambayar ta tabbatar da abin da take zargi. Shi kuma Abby ya san babu wanda zai sanar da shi face Jadda, ko Anwar ko ɗaya daga cikin 'Yayansa. Jadda ta sunkuyar da kanta. “Ban yi hakan da wata manufa ba Iƙbal, sai dan na gargaɗe shi kan kada ya bijire mana” Abby ya kasa magana, ya dafe kansa da ya fara juyawa, ita kuma Immi da ta kasa gane inda zancen ya dosa ta yi saurin ɓanɓare takardar daga hannun Abby domin ta karanta. A lokacin da ta gama karantawa sakin takardar ta yi, jikinta ya shiga rawa, haka idonta ya soma zubar da ƙwalla. “Iƙbal ɗana ya gudu!” Shi ne kaɗai abin da ta faɗa tana shirin faɗuwa. Abby da Gulzar suka yi azamar riƙota, suka tsayar da ita, Gul na bata haƙuri. Jin batun guduwar Arman ba ƙaramin faranta ran Faisak da mahaifnsu ya yi ba. Kuma duk da ya ga halin da mahaifiyarsa, ƙaninsa, matar ƙaninsa da kuma 'yar ɗan uwansa suka shiga bai sa ya fasa faɗar baƙar magana ba. “Da ma me kuke tsammani daga wurin nakasasshe kamar wannan?... Nakasasshen ma wanda ya fito daga jinin Indiyawa” Wata daga cikin 'yan uwan Immi ta nufo shi a zafafe, dan ta gane cewa magana ya yada musu. “Mu ba Indiyawa ba ne. Dan haka kada ka sake cewa mu indiyawa ne” “To yanzu da kika iyo kaina dukana za ki yi? Na ce dukana za ki yi?” Nan fa cecekuce ya kaure a tsakanin dangin Abby da na Immi. “Ya isheku haka!” Faɗin Immi cikin ƙaraji. Hakan ya sa wurin ya yi tsit. “Ku barmu mu ji da ɓatan ɗanmu mana. Bayan wannan abin da ya faru da mu kuma me yasa kuke son ƙara mana wata damuwa?” Ta ƙarashe tana kwantar da kanta a kafaɗar mijinta da ta jingina da shi, sannan ta fashe da wani sabon kukan. “Ko kana ina yanzu haka ɗana?” °•°•°•°•°•°•°•°•°•°•° A hankali Arman ya leƙa windown dake a ta gefensa, ya kalli gajimare dake ƙasan jirginsu da ya tashi sama, kafin ya juyo ya kalli Ivana da Adam dake kusa da shi, dan tikitin kujeru ukun dake kusa da juna suka siye, kasancewar jirgin da suka hau babba ne. Ita Ivana kallo take a system, yayin da Adam ke cin abinci hankali kwance, amma shi sam ji yake hankalinsa ya ƙi kwanciya, da ko wani ƙarin daƙiƙa da jirginsu ke nufar birnin Regen dake ƙasar Germany, wanda ya kasanci gari mafi kusa da Bavarian forest ji yake kamar yana ƙaura daga duniyarsa zuwa wata duniyar da bai sani ba. Idonsa ne ya kai kan agogon dake tsintsinyar hannunsa, a hankali ya furzar da iska daga bakinsa, sannan ya gyara glasses ɗinsa tare da tura sumar dake kan goshinsa baya. Ya lusmhe makafin idonsa yana jin wani abu na rashin daɗi na masa yawo a zuciya. “Arman? Shu fi (Me ya faru)” Adam da ya lura da shi ya tambaya. Amma sai ya buɗe idonsa yana girgiza kai. Sannan ya ɗauke kansa ya jingina da kujera yana kallon window, kasancewar shi ne a window seat. Adam ya kira ɗaya daga cikin flight attendant. Jim kaɗan ta iso seat ɗinsu tana murmushi, kamar yanda aka saba ganinsu, cike da girmamawa ta risina tana faɗin. “Me kake buƙata yallaɓai?” “Ruwa me sanyi” Adam ya amsa. “An gama yallaɓai” “Sannan ki tafi da wannan, na kammala” Ta sake amsawa, sannan ta ɗauke trayn da ya gama cin abinci da shi, ta juya ta tafi, sai da ta kawo ruwan, sannan ya bawa Arman. “Ka sha” Arman ya kalli ruwan, sannan ya kalle shi, ya sa hannu ya karɓa, ya sha sosai, sannan ya aje yana sake ɗauke kai ba tare da yace komai ba. Hankalinsa gaba ɗaya yana kan agogon hannunsa, dan jira kawai yake 12 ta cika. Kuma a dai-dai lokacin da ta cika, ya lusmhe idonsa, a hankali ya furta. “Eid Milad sa'id ya Arman (Happy birthday Arman)!”. Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-7 *Furstlich zeil Hotel, Lower Town, 168, Regen, Germany.* *11:04 na rana.* IVANA POV. A karo na uku ta sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Arman, sannan ta janye hannunta tana jiran ya buɗe. Jiya bayan jirginsu ya sauƙa a birnin Regen kamfanin da Arman ya ɗauka musu domin su kaisu duk wasu wuraren buɗe ido ne suka aiko wakilinsu ya ɗaukesu a airport. Kuma shi ne ya kawosu wannan hotel ɗin, inda suka kama musu ɗakuna uku, kowa da ɗakinsa. Tun a daren jiya ita da Adam suka tsara cewa za su je siyayya, dan haka ne ma yanzu suka shirya domin fita, kuma wakilin kamfanin da kan zaga da masu yawon buɗe idon na tare da su, dan shi ne wanda zai zaga da su a cikin gari, kafin zuwa gobe kuma su nufi Bavarian forest, inda kaddararsu ke jiransu a cikinsa. Kallon Arman ta yi, wanda ya buɗe ƙofar a kasalance, sanye yake da sweate shirt eggplant color, da farin chinos trouser, idonsa saye cikin glasses ɗinsa, wanda rims ɗinsa ya kasance white color. Babu ko takalmi a ƙafarsa, hatta da gashin kansa a hargitse yake, alamar bai ga gyara ba. Shi ma kallonsu ya tsaya yi su duka ukun, sannan ya bar ƙofar ɗakin a buɗe, ya juya cikin ɗakin. Ivana da Adam suka shiga ɗakin, yayin da ɗan rakiyarsu me suna Hans ya tsaya a waje. Ivana da Adam kallonsa kawai suke, har ya zauna kan sofa yana ɗauke kai, ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Ivana da Adam suka dubi juna, dan sun gane cewa kamar abokinsu na cikin damuwa. “Za mu je siyayya ne, idan kana da ra'ayin zuwa” Cewar Adam. Kansa ya girgiza yana

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35