Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

sokawa ɗan fashin, sannan ya tura shi wurin 'yan uwansa. Da sauri suka ɗauki ɗan uwansu suka ruga cikin dajin da gudu. “Hooooo! Abokina wai da ma haka ka iya sarrafa takobi!?” Cewar Adam baki buɗe, dan bai taɓa ganin Arman ɗin na wasan takobi ba sai yau. Ita kuma Ivana takan je ta ga wasan nasa idan suna yi a Fencing Academy ɗinsu, amma duk da haka abin ya bata mamaki. Shi kansa Arman mamakin abin yake ji, takobin dake ɗigar jini ya ɗaga yana kallo, kafin ya mayar da shi cikin gidansa. “Ya kamata mu yi saurin barin wurin nan, kafin wasu mugayen mutanen su zo” Da wannan maganar tasa suka ci gaba da tafiya, kuma ba su yada zango ba har sai da suka fara hango gidan da tsoho yace musu shi za su fara gani kafin su kai ga shiga ƙauyen Askar. Duk da haka Arman bai tabbatar ba sai da ya buɗe taswirar da tsoho ya ba su, sannan ya ga waɗannan hasken ukun suna tsaye a kan ƙauyen Askar da aka masa alama, kansa ya ɗaga ya dubi su Adam. “Wancan shi ne gidan da tsoho yace za mu fara gani kafin mu shiga ƙauyen Askar...” Suka sake kallon gidan. “To mu je mana” Cewar Adam shi ne kan gaba, su ma bayansa suka bi zuwa gidan da aka gidan da ƙasa. Kasancewarsu 'ya'yan musulmai yasa sai da suka gabatar da sallama, kafin su kutsa kai gidan. Su ukun duka suka jeru a tsakar gidan. Suna kallon kallo da matar dake tsakar gidan. Farar dattijuwa ce, wadda a ƙiyasin shekaru za ta kai hamsin da ɗori, sanye take da wasu tufafin da aka saƙa da zaren audiga, wanda aka rina shi zuwa kalar shuɗi. Ƙafafunta na cikin takalman fata irin na zamaninsu, hannunta riƙe da wata ƙwarya. Kamar yanda su ma suke kallonta, haka ita ma take kallonsu. Dan sam ba su mata kama da mutanen da ta sani ba. “Barka! Mu baƙi ne a nan, akwai wani tsoho da ya ba mu wannan yace mu baki” Cewar Arman yana nuna mata taswirar dake hannunsa. Nan take tsohuwar ta saki fuska, sannan ta musu alama da su shiga cikin ɗakinta. “Anya za mu iya yarda da wannan tsohuwar me kamar yamusasshen ganye?” Cewar Adam murya ƙasa yana duban abokansa. Arman ya bugi cikinsa da bayan hannunsa. “Ka mana shiru, a wannan halin da muke ciki ba mu da ikon zargin kowa, mu dai kawai abin yin mu shi ne kare kai a lokacin da aka kawo mana farmaki” Cewar Arman. “Haka ne Adam, tun da har muka yarda da tsohon can ita ma babu dalilin da zai sa mu ƙi yarda da ita” Cewar Ivana. “Ku shiga mana” Tsohuwar ta sake faɗa tana nuna musu ɗakinta da shi ma aka gina shi da ƙasa. Sai da suka gama ƙarewa gidan kallo, sannan suka shiga ɗakin nata da babu komai ciki sai wani gadon katako. Sai wasu jakukkunan fata dake gefe guda. A kan gadon dake ɗakin suka jeru su uku, Adam har da fitar da camera ya fara ɗaukan ɗakin a hoto. A lokacin kuma matar ta shigo ɗakin, hannunta tiƙe da wani abu me kamar kofi, ta aje musu tana faɗin su sha abin ciki, dai suka girgiza mata kai a tare, alamun ba sa sha. Suna ganin sanda matar ta yi murmushi, sannan ta juya kanta tana kallon ƙofar ɗakin, cikin muryarta ta tsufa ta ƙwala ƙiran. “UWAIS!” Cikin abin da ya zarce mamaki Arman, Adam da Ivana suka dubi juna, sannan suka kalli farar dattijuwar, idan dai har ɗan rakiyar da za su tafi da shi ya kasance UWAIS ke nan wannan matar ita ce gimbiya FEROZA, wato mahaifiyar Amir UWAIS BIN DHAAKIR?. _____•••____ UWAIS. A hankali daddaɗar iskar dake busawa a dajin take kaɗa ganyayyakin bishiyun da suka ƙawata shi. Yayin da wani daddaɗan busar sarewa ke tashi a cikin dajin, da daɗin da yake naiman zarce na iskar da ake. Daga can kan reshen wata doguwar bishirya yake zaune, ya harɗe ƙafafunsa, yayin da iskar wurin ke ɗaga dogon gashin kansa, idanuwansa kuma a lumshe, domin shi kansa yana jin daɗin busar. Sanye yake da Sirwal, wani nau'in tufafi irin na wancan zamanin, wanda ake yinsa da zare lilin. Takalman ƙafarsa na fata ne, wanda suke da zaren ɗauri, akwai ɗan siririn rawani a kansa, wanda bai ɓoye dogon gashin kansa ba. Wasu kyawawan tsuntsaye dake kan bishirya da yake zaune ne ke ta kukansu me daɗin saurare, waɗan da suka ƙarawa busar tasa ta yau armashi. Cak busar sarewar ta tsaya, sannan a hankali ya buɗe kyawawan idanuwansa masu ɗauke da shuɗiyar ƙwaya. Ya motsa kunnensa na ɓarin hagu, domin jiyo abin da yake dajin dake gaban wanda yake ciki. Gurnanin damusa haɗi da kukan barewa ya jiyo lokaci guda. Hakan tasa ya yi saurin miƙewa a kan reshen bishirya, sannan ya sofare zarewar hannunsa a cikin ma'ajiyarta dake saƙale a ƙugunsa. Tsalle ya daka ya iyo ƙasa, sai dai kafin ya kai ƙasa ya buɗe fukafukansa da ba su bayyana sai idan har shi ya bayyanar da su ya tashi sama. Cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba ya isa dajin dake kusa da wanda ya baro. A kusa da inda yake jin gurnanin damusar ya sauƙa, kuma yana sauƙa ya sake ɓoye fukafukansa guda biyu, ya tsaya yana kallon wata baƙar damisa da take shirin farmakar wata barewa. A hankali ya miƙe tsaye, sannan ya zaro sarewarsa dake maƙale a ƙugunsa, ya juyata a hannunsa, nan take ta rikiɗa zuwa bakar da aka ƙera da ɗanyar azurfa, sannan a hankali ya riƙeta da hannunsa na hagu, ya ɗagata sama, tare da saitata a kan damisar, yatsun hannunsa na dama ya motsa, wata farar siririyar kibiya ta faɗo hannun nasa, a hankali ya saita kibiyar a jikin bakar, sannan ya sakata cikin yatsun hannunsa biyu. Ya kanne idonsa tare da karkatar da kansa gefe, sai da ya saita damisar sosai, sannan ya saki kibiyar, babu kuskure ko kauce hanya kai tsaye kibiyar ta soki damisar a gefen cikinta, kukan da damisar ta saka ya sa barewar da take hari da farko ta razana ta falla cikin dajin da gudu. Murmushi ya yi kawai, sannan ya juya bakar ta rikiɗe zuwa sarewa, ya sake saƙalata a cikin ma'ajiyarta me kama da gidan takobi, sannan ya yi wurin da damisar ta faɗi tana numfashi da ƙyar, tsuggunawa ya yi a kanta, ya kalli wurin da ya harbeta na ta zubar jini. “Idan aka ce ku koma cin ciyawa ba iyawa za ku yi ba, kuma idan aka ce kada ku cutar da dabbobin da ba su ji ba ba su gani ba ƙi kuke, ya za mu yi da ku ne?” Ya tambaya yana ɗora hannunsa a kan kibiyar, sannan a hankali ya zareta daga cikinta, ya shafa wurin da ya harbeta, sannan ya miƙe yana kallonta. “Allah ya baki lafiya” Yana gama faɗar hakan ya buɗe fukafukansa ya tashi sama. Yana shawagi a iska kiran mahaifiyarsa ya riske shi, hakan yasa bai sauƙa a ko ina ba sai a cikin gidansu. IQRAH. Ƙuri ta yi da ido tana bin yariman da aka ce shi ne wanda za'a

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35