Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

faruwa tsakaninta da shi duka shiri ne. Domin hatta da farkon haɗuwarsu shiri ce, shirin da ya taso shi tun daga nahiyarsu zuwa Mamlakatul Jiyad. Domin asalinsa ba ɗan garin ba ne, babu wani abu da ya haɗa alaƙarsa da ta daular Jiyad, cin burin ɗaukan fansa ya sa ya yi takekeniya ya bar nahiyarsu ya kutsa zuwa wannan gari. Lokacin da ya zo garin duka tsarukansa sun tafi dai-dai, ciki har da sawa Iqrah soyayyarsa a ranta. Kuma hakan ma ya tafi yanda yake so, sai dai kuma wa gari ya waya? Domin a ƙarshe shi aka bari da jinyar zuciya. Duk taka tsantsan ɗin da yake na gujewa soyayyar Iqrah an yi rashin sa'a shirinsa ta wannan fannin bai yi ba. Domin a halin yanzu shi kansa ya san cewa yana sonta, amma kuma ya yi rantsuwa kan ba zai bari soyayyarta ta hana shi ɗaukan fansarsa ba, ko da kuwa hakan zai sake raunata zuciyarsa ne a karo na biyu... “Eid!” Kamar kullum, kamar yanda ya saba tunaninta haka yau ma muryarta ta kutso cikin tunaninsa. A hankali ya zauna kan wata bishiya, yana kallon wasu yara dake wasa kusa da bishiryar. Hannu ya kai ya sauƙe Aafa dake kafaɗarsa, sannan ya ajeta a gefensa yana ci gaba da kallon yaran. Haka kawai murmushi ya suɓuce masa, domin ya tuna da nasa ahalin, da ace har yanzu matarsa Maryam na raye, da ita ma ta haife masa ɗan cikinta... Ɗansa, jin zuciyarsa na ɗacin tunowa da mutuwar Maryam xa ta mahaifinsa ya sa ya kawar da kai daga barin kallon yaran, gudun kada ya haɗiyi zuciya ya faɗi ya mutu ba tare da ya ɗauki fansa ba. “Daga gobe ba za ka sake kwanan farin ciki ba Cangaz! Zan tabbatar da na ƙuntata maka dai-dai da yanda ka ƙuntata zuciyata!” Ya furta yana haɗe haƙwaransa na sama da na ƙasa, zuciyarsa na tabbatar masa da cewar zai iya!. ADVENTURERS. Bayan shafe tafiyar awa uku a ƙafa, suka yanke shawarar zama su huta a wani daji. Yayin da suke hutawa Uwais yace zai je ya naimo musu abinci, amma sai Arman yace kada ya je, shi ma ya zauna ya huta, tun da shi ma zai gaji ne. “Ba lalle ba! Shi da mu akwai banbanci!” Cewar Sana da yanzu ita ma ta zama abokiyar tafiyarsu. Lokacin da suka gane cewa ita ce sun sha matuƙar mamakin ganin matar sarki 'yar saki a wuri irin wanda suka haɗu, bayan ta sanar da su cewa tafiya ce ta kamata har ta kai ga mutanen nan sun kamata, sai suka cire ko wani kokwanto, su ka ci gaba da tafiya da ita har zuwa yanzu. “Me ya sa na zama ba ɗaya da ku ba?” Uwais ya tambaya yana murmushi. “Saboda kai ka kasance ruwa biyu, aljani kuma mutum!” Sana ta amsa shi, har zuwa yau fuskarta na a rufe da mayafin da take rufe kanta da shi, domin ba ta cika buɗe fuskarta ba. “Uwais!” Adam dake yi wa Ivana tausa a ƙafa ya kira sunan. Hakan ya sa Uwais ya dube shi. “Ya ka ji lokacin da aka ƙwace mulkin mahaifinka, sannan ya kake ji idan ka tuna cewa abin da yake mallakinka na tare da wani da ba kai ba!?” Adam ya tambaya da biyu, dan lokacin da ya cilla masa tambayar sai da ya saci kallon Arman, kuma ya lura da tambayar ta sa shi cikin nazari. Ivana da ta fahimci inda ya dosa ta daki kafaɗarsa cikin gargaɗi, duk da yau a gajiye take liƙis, saboda ita ne ma suka yada zango ba dan dare ya yi ba, ga ƙafafunta dake mata mugun ciwo, shi ya sa ma ta saka Adam ya mata tausa. “Lokacin da aka sanar mana da cewa mahaifina ya mutu ji na yi kamar ni ma zan mutu na bi shi. Har ina jin kamar na samu Safraz da Ammi Anser (Kawuna Anser) na ce da su su kwashe komai da muke da shi, amma su bar min Abi. Na ji haushi sosai lokacin da na fuskanci cewar a kan kujerar mulki suka kashe min mahaifina. Bayan kuma sun fara shirin ƙwace abin da yake nawa sai na ji cewar na rasa komai, wannan kujerar ita ce kaɗai abin da nake ganin cewa Abi ya bar min... Lokacin da ya mutu ina ƙarami sosai, amma duk da haka ba na mancewa abubuwan da suka shefi shi, a ko da yaushe yana yawan cewa babu wanda ya dace da zama sarkin Mamlakatul Afsah bayan Uwais!...” Ya ɗan yi fasali yana murmushi me ciwo, ya shafa kansa sannan ya ci gaba da faɗin. “Ashe hakan ba zai zama gaskiya ba, ashe wani bayan ni ne zai zama sarkin! Ashe ba ni da rabon gadar mahaifina...” Lokacin da ya kai ƙarshe duk hankalin Adam da Ivana na kan Arman da jikinsa ya yi sanyi, ba komai yake tunowa ba face Abby. Ta wani ɓangaren zai iya cewa rayuwar Uwais na kamanceceniya da tasa rayuwar. Idan aka kwatanta Anser da Ammu Anwar, Safraz kuma da Faisal, Malik Dhaakir kuma da Abby, Uwais kuma a matsayin shi!... Ke nan son abin duniya zai iya sawa Ammu Anwar da Faisal su haɗa hannu wurin kashe Abby?... “Arman!” Kiran da Ivana ta masa ya katse masa tunani, sai ya kalleta, sannan ya gyara zaman glasses ɗinsa. “Lafiya?” Ta tambaya tana taɓa shi, ya girgiza mata kai, sannan ya miƙe ya nufi cikin daji, sai da ya yi nesa da su sosai, sannan ya jingina da jikin wata bishiya, kewar ahalinsa na mamaye masa ruhi. Wayarsa ya ɗauko, ya buɗe, sannan ya shiga gallery, ya dubo hoton da suka ɗauka shi da Immi ranar da zai gudu daga gida. Ƙwalla ya ji na taruwa a idonsa, hakan yasa ya kai hannu ya cire glasses ɗinsa, sannan ya goge idonsa, ya mayar da glasses ɗin, kana ya dubo hotonsu shi da Abby, wani tsohon hoto da aka daɗe da ɗaukansa... “In Allah ya sa ba ni da rabon dawowa gida ina fatan ka yafe min Abby, idan kuma har Allah ya nufi dawowata ina me baka tabbacin zan yi abin da kake so, zan karɓi shugabancin da ake fata da tuƙuburin na karɓa... Domin a yanzu na gane cewa kuskure ne bijire maka da na yi ta yi a baya, ka yafeni Abby!” Ya furta wani hawayen na zubo masa. A dai-dai lokacin kuma ya ji ihun Ivana, hakan tasa ya buɗe idonsa da sauri, sannan ya juya yana kallon bayansa, domin ta nan ya jiyo ihun. * “Kamar akwai abin da yake damunsa!” Cewar Uwais lokacin da Arman ya tashi daga wurin. Adam ya girgiza kansa. “Ta wani ɓangaren rayuwarka da tasa tana kamanceceniya. A zamaninmu mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, sannan yana da manyan kanfanunuwa, kuma shi mahaifin nasa yana da ɗan uwa, wanda yake da ɗa namiji, shi ma ɗan nasa yana da burin zama shugaban kamfanin. Kasancewar shi Arman na da nakasar gani ya sa kawun nasa ya yi amfani da wannan damar wurin cusa masa ƙiyayyar shugabancin kamfanin. A halin yanzu kuma mahaifinsa ya fara gazawa, tsufa ya fara masa sallama, yana buƙatar Arman ya maye gurbinsa, amma sam Arman ya ƙi aminta da hakan...

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35