Chapter 35
Chapter 35
Hatta da wannan tafiyar da muka yi ta samo asali ne daga gujewa karɓar shugabancin kamfanin!” “Abin tausayi!” Cewar Uwais. “Me ya sa yake saka wani abu a saman idonsa?” Sana ta tambaya. Adam da Ivana suka yi dariya. “Glasses ake kiransu, kuma su ne suke taimaka masa wurin gani, ba tare da su ba ba zai iya ganin ko da tafin hannunsa ba!” “Na gane!” Cewarta tana waigawa tare da kallon hanyar da ya bi. “Adam taimaka min na miƙe!” Cewar Ivana, Adam ya taimaka ya ɗagata. “Ina za ki je?” Ya tambaya ganin ta yi hanyar kogin dake gefe da su, Ivana na ɗingisa ƙafa tace. “Zan wanke fuskata ne” Da haka ta ƙarasa bakin kogin, ta tsugguna ta fara wanke fuskarta, sai da ta gama ta miƙe, tana shirin komawa inda su Uwais suke ta ga wani abu ya faɗo gabanta tim!. Razana ta yi ta ja baya tana ƙarewa budurwar da ta faɗo gabanta kallo. Kafin ta yi wani yunƙuri budurwar ta ruƙo wuyanta, sannan ta buɗe fuska-fukanta ta tashi sama da ita, hakan yasa ta ƙwala ihu domin naiman ɗaukin abokanta. Lokacin da Su Adam suka iso bakin kogin har budurwar ta yi nisa da ita a sama. “Ivana!” Cewar Adam cikin matsanancin tashin hankali. “Me ya samu Ivana?” Cewar Adam da ya ƙaraso wurin da gudu, shi ma kuma sai a lokacin ya lura da Ivana dake sama. “Wace ce waccan?” Arman ɗin ya tambaya yana kallon budurwar dake tare da Ivana. Kafin wani ya amsa masa Uwais ya buɗe nasa fukafukan zai tashi sama, Arman ya dakatar da shi. “Uwais! Zan tafi tare da kai!” “Zo mu je!” Kawai Uwais yace, sannan ya riƙe hannun Arman ɗaya, ya tashi sama da shi, suka bi bayan budurwar da ta ɗauke Ivana. ...End of book 1... ____________________ _Humm! Shin wacece wannan wadda ta sace Ivana?_ _Shin kuna ganin cewa Uwais da Arman za su iya cetonta?_ _Wata ƙiyayya ce tsakanin Eid da Malik Cangaz?_ _Wani abu ne ya samu matar Eid da ahalinsa da har ta kai ga yana son ɗaukar fansa!_ _Me Malik Safraz yake shiryawa?_ _Wani ƙudiri ne ya sa Sana matar Malik Wasimudeen shigowa cikin ADVENTURERS?_ _Shin kuna ganin dakarun Malik Cangaz za su iya riskar ADVENTURERS?_ _Mece ce makomar auren da Malik Cangaz yake shiryawa?_ _Yaushe ADVENTURERS ɗinmu za su riske ƙofar Malik Cangaz?. Shin za su iya samun nasarar buɗe ƙofar? Shin za su koma gida ko a'a?_ Domin ci gaba da karanta book 2 za ku biya ₦400 for regular group. ₦800 for VIP to. 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172702. Sannan za ku samu complete book one and 2 on Arewabooks, kada ku manta ku yi following ɗina domin samun notification da zarar na yi update. Ina me tabbatar muku da book 2 is giving 🔥🔥🔥. A har kullum, godiya ta musamman zuwa ga masoyana a duk inda kuke. I ❤️ like WUJIGA-WUJIGA 💋. See you in book 2. Best regards Salma Ahmad Isah ✍️ A.k.a Candy🦋 A.k.a Bahaɗejia🐎 2024...
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35