Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

suke kutsawa a dajin bai yi kama da mutane na yawan bi ba bai sa sun fasa shiga ciki ba. Har suka iske wani kyakkyawan dausayi dake tsakiyar dajin, akwai nau'ikan bishiyoyi da tsirrai a wurin gwanin ban sha'awa, sannan akwai kogi dake a ta gefe, a gefe guda kuma akwai wani babban dutse da yake bayar da ruwa, wurin ya haɗu matuƙa. “Wow wow wow! Amma wurin akwai ban sha'awa” Faɗin Ivana tana ɗaga kanta tare da ƙarewa wurin kallo, yayin da shi kuma Arman ke gefe ta wurin kogin yana kallon yanda ruwan wurin ke gudana, shi kuma Adam ya riga ya fara ɗaukan wurin a hoto da camera ɗinsa. “Ivana gyara na ɗaukeki hoto” Ya faɗa yana saita camera ɗin a kanta, Ivana ta gyara tana murmushi, ya ɗauki hoton yana dariya, shi ma Arman ya matso yana faɗin a ɗauki hoton da shi, ya dafa Ivana Adam ya ɗaukesu tare. Suka sauya style suna jiran Adam ya ɗaukesu hoto, a cikin camerar Adam ya hango mutuwa. Dan haka ya sanƙare yana wangale duka idanuwansa, jiki a saɓule ya sauƙe camerar yana rawar jiki kamar an jona masa lantarki. “Ka ɗauke mu mana, ka wani tsaya a nan kamar saƙago” Faɗin Arman yana gyara glasses ɗinsa, Adam ya soma ja da baya, sannan cikin karkarwar hannu ya ɗaga ɗan yatsansa, ya yi nuni da bayansu, hakan ya sa cike da mamaki Ivana da Arman suka dubi juna, kafin Ivana ta juya tana faɗin. “Wai me ka gani da ka...” Haɗiyewa sauran kalaman ta yi, tare da binsu da yawun bakinta tana zaro ido, kamar yanda ta yi kyakkyawan gani haka shi ma Arman ya yi, dan yana juyawa suka yi ido huɗu da Cheetah ɗin dake saman dutsen da yake zubar da ruwa. Ba su tsaya ɓata lokaci ba suka ce ƙafa me na ci ban baki ba? Kowa a cikinsu ya ranta a na kare, gudu suke Cheetah ɗin na binsu, Adam ya fi koea ruɗewa, dan a gudun ma shi ne a kan gaba, dan tun da ya zo duniya bai san wani abu da ya firgita shi sama da wannan ba, sanin cewa Ivana me rauni ce ya sa Arman ya ruƙo hannunta yake janta suna gudu tun ƙarfinsu. A yunƙurin ceton rayukansu suka faɗa cikin wani kogo dake bayan dutsen da Cheetah ɗin take, kuma suna shiga cikin kogon ba su tsaya wata-wata ba wurin naiman maɓoya, Arman ne ya fara ganin wata tsohuwar ƙofar katako dake cikin kogon, dan haka ya yi azamar saka duka hannayensa biyu, tare da ƙarfin da Allah ya wadata shi da shi ya buɗe ƙofar. “Ku zo ku shiga” Ya faɗa ba tare da ya tsaya duba abin da yake a bayan ƙofar ba, ya janyo hannun Ivana ya turata, an ce idan ka ga mutuwa idonka rufewa yake, tabbas idanuwansu sun rufe, domin har suka gama shigewa ƙofar sam ba su lura da ina suke shiga ba. Abin da zai biyo bayan shigarsu wannan ƙofar sai ya fiye musu su tsaya wannan Cheetah ɗin da ta biyosu ta cinye naman jikkunansu ɗanye. Domin masifa da bala'in da zai biyo baya babu hankali ko tunanin da zai iya hasaso shi... Yanzu ne labarin zai soma, sai a yanzu ne za mu kama ainahin hanyar da labarin yabi, yanzu ne muka saƙo zaren labarin, domin gane warwararsa, sai kun ji abin da ya biyo bayan shigewarsu cikin wannan ƙofa... *Wani Zamani...* Wani zamani na nufin zamanin da ya shuɗe kafin samuwarmu, ko kuma wanda zai zo bayan wanzuwarmu, zamani na zuwa ya wuce kamar wucewar damina da rani... Sannan zamani ya kan shuɗe, har a manta shi a duniya, matsawar babu masu bada labarin wannan zamanin... Sunan zamani na wakiltar shekaru 100 da suka suɗe a baya, ko waɗan da za su zo a gaba... A kan iya gane bambancin zamani ta hanyar tufafinsu, abincisu, gine-ginensu da kuma kalar yarensu... * Wani kyakkyawan daji ne, ko ina ka kalla koren ganye ne ke kaɗawa a cikin iskar Allah, dogayen bishiyu da ciyayin da suka ƙawata ƙasa su ne a ko ina. Kuma duk girman dajin babu komai cikinsa sai ginin wata bukka ƙwara ɗaya tal, wadda aka yi ta da busasshiyar ciyawa. (Budu) Daga bayan bukkar, wani farin dattijo ne durƙushe, yana tsinkar 'ya'yan itaciyar da suka nuna har suna faɗowa daga jikin bishiryarsu. Wasu kayan saƙi ne sanye a jikinsa, wanda za su shaida maka daga zamanin da yake, gashin kansa dogo ne, domin har ya sauƙa gadon bayansa, duk da rawanin da ya yi a kansa. Wata iska me matuƙar ƙarfi ce ta fara kaɗawa a dajin, hakan ya sa dattijon ya miƙe tsaye yana kallon dogayen bishiyun dake wurin, waɗan da ke kaɗawa da ƙarfi, sakamakon ƙarfin iskar da ake. Kansa ya juya ta ɓarin damansa kaɗan, nan ya ga wani jan kyalle dake ɗaure a saman bukkarsa na shirin sulmiyewa ya faɗo. Hakan ya sa ya firfito da idonsa cike da abin da ya zarce a kira shi da mamaki. Bakinsa na rawa ya juya ya shiga bin dajin da kallo, amma bayan iskar dake ƙara ƙarfi babu kowa babu komai. Mamaki bai ƙara kama shi ba sai da ya ga jan ƙyallen ya kunce ya faɗi ƙasa... A nan ne ya tabbatar da wani abu guda, lalle ranar da ya daɗe yana jiran isowarta ta zo, ranar da ya shafe sama da shekaru ashirin na rayuwarsa yana rayuwa a wannan dajin domin ta zo, ranar da za a yi wasu baƙin matasa uku, daga wani zamanin zuwa nasu... “Tabbas! Baƙin matasa uku sun samu shigowa duniyarmu. Domin zama silar kawo ƙarshen mulkin zalunci. Sun zo domin tada gagarumin yaƙi da yake dai-dai da yaƙin duniya... Ƙaddara ba ta da siffa, ta kan juya rayuwar ɗan adam ta ko wace siga, sannan ta kan iya maida sama ta dawo ƙasa cikin abin da bai fi ƙiftawar ido ba. Lalle ƙaddara ita ce ta zamto silar wanzuwar waɗannan matasa a wannan duniya tamu... Wannan ƙaddara ita ce ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwar waɗannan matasa, daga zamaninsu zuwa namu...” Kwandon kayan marmarin dake hannunsa ne ya suɓuce ya faɗi, yayin da ya ga haske ya fara mamaye dajin, saurin durƙushewa ya yi a ƙasa yana me godiya da mai duka... * Yashe suke a kan ciyayin dake kusa da wata ƙatuwar bishiya, idan ka musu kallo ɗaya sai ka ce a mace suke, amma kuma ba a macen suke ba, wani dogon bacci suke me kama da suma. Arman ne ya fara motsawa, kafin ya buɗe idonsa yana dafe kansa da ya sara lokaci guda. Idonsa ya rufe ya sake buɗewa, amma saboda glasses ɗinsa a fashe suke ya sa ba ya gani da kyau, a daddafe ya miƙe zaune yana yarfe hannu, saboda Adam da ya danne masa hannun nasa, glasses ɗin ya cire, ya kamo ƙasan rigarsa ya goge shi, sannan ya mayar idonsa, a nan ne ya gane cewa glasses ɗin ne ya fashe. Tsaki ya ja, dubansa na kaiwa kan Adam dake kwance, ya sake jan wani tsakin tare da saka hannunsa ya ɗaka masa duka. “Mun mutu... Damisa ta cinyemu!” Ya farka da wannan batu a tsorace, amma ganin Damisar

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35