Chapter 2
Chapter 2
hanci da madaidaicin baki me ɗauke da farar fata me haske. Murmushi ne kwance a kan fuskarta, yayin da take kallon ɗalibanta da take koyawa kiɗan guitar zaune a gabanta. Dukansu sun nutsu suna sauraron daddaɗan kiɗan guitar ɗin da take... Wayarta dake aje a gefenta ce ta kaste musu darasin, ta hanyar ringing ɗin da ta fara. Hakan yasa ta dakata da kaɗa guita ɗin, ta kalli wayarta dake ruri, alamun shigowar kira ‘Rafiƙi’ (Abokina) shi ne rubuce tare da heart emoji a gaban sunan, kuma kaf duniya mutum ɗaya ne ta yi saving numbernsa da hakan. “A'aziruni lahza! (Excuse me please)” Ta faɗi cikin harshen larabci tana duban yaran ɗabilan nata. Sannan ta juya ta ɗauki wayarta, ta ɗaga kiran Arman dake shigowa. “Shu wainak halla? (Yanzu kana ina?)” Ta tambaya ba tare da ta bari ya yi magana ba, dan ta san sun yi da shi a kan yau yana da gasa tsakaninsa da abokan koyon wasan fencing ɗinsa. “Ai dai kya bari mu gaisa ko?” Arman ya faɗa daga ɗayan ɓangaren, sai ta yi murmushi, tana cire handle ɗin guitar ɗin daga wuyanta, sai da suka gaisa, sannan ya sanar mata da dalilin kiranta. “Na kira Adam Maama ta ɗaga, ta sanar min da tun jiya ya kulle kansa a ɗaki, ya ƙi fitowa. Da alama ya kalli wani horror film ɗin ne” Ivana ta kwashe da dariya tana rufe bakinta, dan ita ma ta sa halin abokin nasu. “Yanzu kana ina?” “Na baro business bay a motata” “Mashi (Okay) ka biyo ta nan sai ka ɗaukeni” “Ɗayib (Okay)” Ya amsa, sannan ya aje wayar. * Arman ya kwashe da dariya yana kallon Adam da yay tsuru-tsuru da shi, saboda yanda yake a tsorace. Ivana ta ɗan yi guntun tsaki tana dafa kafaɗun Adam dake basu labarin film ɗin ban tsoron da ya kalla daren jiya, wanda ya hana shi sukuni har zuwa yau ɗin nan. “Shifti? Huwa am yadhak alaiyyi” (Kin ga ba? Dariya mayake min) Adam ya faɗi yanayinsa na nuna damuwar da yake ciki, dan har yanzu a firguce yake. “Armaan la ad tadhak!” (Armaan kada ka sake dariya) Ivana ta gargaɗe shi, sai ya ɗora hannunsa a kan bakinsa, yana son toshe dariyar dake cinsa, amma ya kasa. Ivana ta girgiza kanta, sanan ta tura Adam suka fara tafiya tana kwantar masa da hankali. Arman ya biyosu yana ci gaba da ƙyaƙyatawa Adam dariyar mugunta. Da haka har suka shiga Cavo Espresso Bar dake kusa da inda suke, har suka zauna Arman bai daina dariya ba, ko ya so ya danne daga sun haɗa ido da Adam zai ji dariyar da taso masa. “Ivana kalli yaskut! Wa illa rah irja'a ala bait” (Ivana ki saka shi ya yi shiru, idan ba haka ba zan koma gida). Ya faɗa yana kallon Ivana. Ivana ta ɗakawa Armaan duka a baya tana faɗin. “Da ƙyar muka saka shi ya fito daga gida, yanzu kuma idan ka ci gaba da masa dariya ko zai koma gida ba zan yi ƙoƙarin hana shi ba” “Asif (Ku yi haƙuri)” Faɗin Arman yana toshe bakinsa. Ivana ta sake dafa kafaɗar Adam da har yanzu yake a dame. “Laik Adam! Shabah mu haƙiƙi! Killu mazah! Wa ma bi kaffu!” (Ka ga Adam, fatalwa ba gaskiya ba ce, duka shiri ne, kuma ba su da ban tsoro). “Me ya sa za ki faɗi haka? Bayan ni na ganta da idona, wata doguwa, me dogayen farata, idonta ja... Wayyo Maama” Ya ƙarashe yana rufe fuskarsa, saboda fuskar fatalwar da ya hango. Ivana ta sake dafa shi. “Ihda! Halla rah jiblak shai. Biddak shai mu?” (Ka nutsu, yanzu zan kawo maka shayi, kana son shayi ko?) Ya jinjina mata kai yana kallon Arman dake ta ƙoƙarin danne dariyar da ke ciyo shi. Ivana ta gyaɗa kai, sannan ta miƙe ta zagaya ta nufi wurin da zata yi order. Cup uku na shayin ta karɓa, sai dai a yayin da take shirin juyawa ta yi karo da wani mutum da shi ma yake ƙoƙarin zuwa wurin. Farko kofunan shayin dake jere a kan tray ta fara kalla, da ta ga ba su zube ba sai ta kalli mutumin da ta yi karo da shi. Wani kyakkyawan matashin balarabe ne, wanda ke sanye da baƙar suit, kalar farar fatar jikinsa me ɗaukar hankali ce, haka ma kammaninsa, dogo ne, kuma me matsakaicin jiki, yana da faffaɗan ƙirji, sannan sumar kansa na cikin asken high pade. Yana da buɗaɗɗen ido, wanda yake ɗauke da shuɗiyar ƙwaya, sannan hancinsa dogo ne sosai, ga bakinsa dai-dai wa dai-dai, yana da saje da kuma gemu, wanda suka ƙara masa kyau. “Ana ba'atazir! Ma intabahat!” (Ki yi haƙuri ban lura da ke ba ne). Ta ji muryasa me daɗi ta furta, sai kawai ta jinjina kanta, alamun ba komai, sannan ta raɓa shi ta wuce, har ta koma table ɗin da su Armaan suke bai daina kallonta ba. “Rifaƙ (Guys) ko kun san cewa yau Chris Brown zai yi live performance a Coca-cola Arena?” Faɗin Arman yana nuna musu takardar sanarwa a cikin wayarsa. Adam da Ivana suka dubi juna. “Wai yau?” Adam ya tambaya yana aje cup ɗin dake hannunsa. “Eh yau, duba ka gani” Ya miƙa masa wayar , Adam da Ivana suka haɗa kai suna karantawa. “Za mu je ne?” Cewar Ivana. “Akid! (Of course)” Arman ya bata amsa. Domin duk inda za su je ko za su fita shi ne ke biyan duk kuɗin da za'a kashe, ko cinema za su je shi zai sai musu ticket. Saboda kaf cikin su ukun babu wanda ya kai mahaifinsa kuɗi. Dan mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, wanda yake da kamfanunuwa masa masu zaman kansu. Shi Adam photographer ne, yana aiki tare da wani kanfanin magazine, ita kuma Ivana musician ce, tana koyar da kiɗan guitar a Repton school Dubai. Sannan tana aikin kiɗa a waƙoƙi idan har an buƙata, duk cikinsu shi Arman ɗin ne ba shi da aikin yi, ba wai dan ba'a naima masa a gidansu ba. Sai dan shi a rayuwarsa ya tsani duk wata harka da ta shafi kasuwanci. Duk da ya taso a gidan da ake kasuwanci, kuma hakan ya samu asali ne daga nakasar gani da yake fama da ita tun lokacin yarinta. Tun a tasowarsa kawunsa, yayan mahaifinsa ya saka masa ƙin harkar kasuwanci, dan a ko da yaushe abin da yake faɗa masashi ne. “Harkar jagorancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ba na makafi ba ne” Ya sha faɗa masa hakan tun ba shi da wayo har ya taso ya yi wayo, tun ba ya gane abin da kalaman ke nufi har ya zo ya gane abin da kalaman ke nufi. Sannan tsangwamar da ake yi wa mahaifiyarsa a halinsu ya ƙara cusa masa ƙiyayyar kasancewa ɗaya daga cikin ahalin Alhadi a ransa. Kuma suna nunawa mahaifiyarsu wariyar launin fata saboda ita 'yar Pakistan ce, su kuma ahalin mahaifinsa larabawan Qatar ne. Shi da ƙanwarsa Gulzar kaɗai iyayensu suka haifa, kuma bayan shi babu wani wanda zai iya gadon kasuwancin mahaifinsa sai Faisal!. Ɗan yayan mahaifinsa da shi ma ya bada tasa gudummawar wurin cusa ƙiyayyar son karɓar jagorancin Majmu'at Shirkat Alhadi (Alhadi Group of Companies). Zama shugaban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35