Chapter 18
Chapter 18
tafi kawai” Ivana da Adam suka haɗa ido, kamar kar su bi shawararsa su bari sai Hans ya zo, amma da yake tsautsayi ba ya wuce rana sai suka amince, suka shiga mota suka ɗauki hanyar Bavarian forest. Da ko wani taƙi da suke wucewa domin nufar dajin ƙaddararsu suke tunkara ba tare da sun sani ba. Domin da ace sun san abin da suke tunkara da sun yi tariyar zamanin baya, sun cire ranar da suka yanke shawarar zuwa Bavarian forest a cikin kwanakinsu na duniya. Kasancewar ba su san hanya ba ya sa suke tambaya, har Allah ya sa suka samu damar kutsawa cikin dajin sosai, dan ma suna tsayawa jiran Adam ya ɗauki hoton abubuwan birgewa dake dajin, da haka suka iso inda hanya ta rabu biyu. Kokwanto ya sa Arman ya tsayar da motar, dan a cikin hanyoyin biyu bai san ta ina zai bi ba, ga shi kuma babu kowa a wurin bare su yi tambaya. “Ina ya kamata mu bi?” Ya tambayi Adam dake zaune a gefensa, Adam ya ɗaga kansa ya kalli hanyoyin biyu. Kuma a lokacin abin ya faru, a lokacin ƙofofin ƙaddarorinsu suka buɗe. Domin zuciya ɗaya Adam ya ɗaga hannunsa ya nuna hanyar da ta yi dama. “Wannan hanyar ta maka kama da ana binta? Ji yanda ciyayi suka rufe hanyar fa, kuma sam babu alamar ana bin hanyar a yanzu” Cewar Ivana dake baya. Arman da Adam suka dubeta. “Ai dole hanyar ba za ta yi kama da ana bi ba, saboda an fi shigowa dajin a mota, so ba lalle ta nuna wata alama ba... Kuma ni jikina ya na bani cewar wannan ita ce hanyar” “Arman kar ka saurare shi, saboda ni dai na ce waccan ita ce hanyar.” “Ivana bari mu fara bi ta nan ɗin, idan ba ita ba ce sai mu dawo” Cewar Arman da shi ma tasa zuciyar ta raya masa cewar hanyar da Adam ya nuna ita ce wadda za su bi. Ya tada motar, sannan ya juya kan motar zuwa hanyar da za ta sauya rayuwarsu. Har motarsu ta shige hanyar, a cikinsu babu wanda ya lura da allon sanarwar dake gefen hanya, wanda aka rubuta ‘CHEETAHS AHEAD. KEEP DISTANCE!’. *Da misalin 10:22 na dare.* Tantina (tent) uku ne kafe a tsakiyar wani fili, domin wurin da babu yawan dogayen bishiyu suka samu suka kafa tent. Yayin da motarsu ke fake kusa da tents ɗin, sun aje wasu gingimen bishiya guda uku wanda suke zaune a kai, yayin da wutar da suka hura domin ƙarawa daren nasu armashi ke a ci. “Akwai sanyi sosai a wurin nan” Faɗin Ivana tana ƙara nannaɗe hannunta cikin zip hoodie ɗin dake jikinta. Arman ya yi dariya yana shan drink ɗin dake hannunsa, yayin da Adam ke duba hotunan da ya ɗauka jiya a cikin garin Regen. “Adam!” Ivana ta kira tana dubansa, shi ma ya kalleta cikin alamun ya aka yi?. Da ido ta masa alama, take ya gane abin da take nufi, dan haka suka miƙe a tare kowa ya shiga tent ɗinsa, yayin da Arman ke binsu da kallo yana tambayar abin da ya faru. Cikinsu babu wanda ya amsa masa, dan haka ya miƙe yana kallon tents ɗin nasu, har suka fito, kowa a cikinsu hannunsa riƙe da gift box. “Barka da ƙarin shekara abokina, ina tayaka murna” Faɗin Ivana tana miƙa masa box ɗin kyautukan da ta sai masa, Arman ya yi dariya yana kallonsu, sannan ya saka hannu ya karɓa yana mata godiya, shi ma Adam ya miƙa masa nasa box ɗin guda ɗaya, wanda silar ƙaddararsu ke ciki, Arman ya aje wanda Ivana ta ba shi kusa da inda yake zaune da, sannan ya karɓi na Adam, ya masa godiya yana rungume shi. “Na gode sosai abokina...” Ya kalli Ivana dake kallonsu, sannan ya mata alama da hannu tare da faɗin. “Taho mana” Ta yi dariya sannan ta shiga space ɗin da suka yi creating ma ita, su duka abokan suka rungume junansu, a lokacin kuma kunnen Adam ya jiyo wani sauti me kama da kukan damisa. Hakan ya sa ya firgita ya janye jikinsa yana waige-waige. “Hey lafiya?” Ya kasa amsawa Arman, sai bin zagayen wurin da suke yake da kallo. “Adam” Ivana ta faɗa tana dafa shi, banda bugu babu abin da ƙirjinsa ke yi, kamar mace. “Me ya faru?” “Kamar... Kamar kukan damisa” Ya amsa a tsorace. “Damisa kuma? A nan ɗin?” Arman ya tambaya, sannan ya kunna wata touch light ɗinsu me haske, ya shiga haska dajin, amma shi bai ga komai ba. “Kai babu komai fa a nan” Adam ya haɗiyi yawu yana girgiza kansa, in dai baiwar ji to Allah ya hore masa kamar maciji. Dan haka ba ya jin cewa kunnensa ne ke haihuwa, yana da tabbacin ya ji kukan damisa. Amma da su Ivana suka ƙaryata shi sai ya haƙura ya zauna yana baza ido kamar ɓera a tarko. Yayin da Ivana ta ɗauki guitar ɗinta ta soma kaɗawa, saboda Arman da ya buƙaci hakan. Duka kyautukan da suka ba shi sai da ya buɗe su a lokacin, amma duk ciki babu wanda ya fi burge shi sama da makullin ƙaddararsu, wato sarƙar da Adam ya ba shi, dan sam kasa jurewa ya yi sai da ya saka sarƙar a wuyansa yana ta jin daɗi. Sun ɗau lokaci sosai a wurin suna hira tare da cin abinci, kafin suka yanke shawarar kowa ya shiga ya kwanta, kasancewar Adam a tsorace yake yasa yace dan Allah Arman ya yarda su kwana a tent ɗaya, amma fir Arman ɗin yaƙi. “To wai kai yanzu da kake haka ta ya za ka zama jarumi? Shi fa namiji da jarumta aka san shi, kalli Ivana, ita ma ita kaɗai za ta kwanta, mi ye zai cinyeta? Da har kai da kake namiji za ka ji tsoron kwana kai kaɗai” Da wannan batu dai ya ƙwararawa kansa gwiwa ya shiga tent ɗinsa yana karanto duk addu'ar da ta gifto cikin tunaninsa, dan a tsorace yake matuƙa. A lokacin da kowannensu ya shiga tent ɗinsa, Cheetah ɗin dake laɓe a cikin daji ta juya zuwa wata hanyar!... 😳 Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-8 *Bavarian forest, Germany.* Yayin da hasken rana ya mamaye duniya, matasan uku suka shirya tsaf, domin zaga dajin da suka kwana ciki. Tun bayan da suka yi karin kumallo suka nannaɗe tents ɗinsu. Suka haɗa kaf kayansu cikin wasu dogayen backpack irin na matafiya. Arman na sanye cikin wani 3qtr milk color, da farar hoodie mara nauyi, wadda ya ɗorawa black denim jacket a samanta. ƙafafunsa cikin takalmin timberland. Adam kuma na sanye da blue jeans da baƙar shirt, ya ɗora casual Oxford shirt a saman rigar, sai bakar p-cap da ya saka. Yayin da Ivana ke sanye da Orange T-shirt, sai jeans overall (corpenta) da ta saka, gashin kanta kuma na cikin French braid. Kowanne a cikinsu na goye da jakar kayansa, yayin da suka kutsa cikin dajin cike da farin ciki da annashuwa, duk da har yanzu shi Adam a ɗarare yake, dan a tsorace yake ɗaukan hotunan wasu wuraren da suke da ban sha'awa. Duk da sam inda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35