Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,197 words 0 views Progress saved
Download Book

lokacin. Sanda ta shiga cikin gari aka fara kiran sallah a babban masallacin garin, hakan yasa kaikawon mutane ya ƙaru, kowa na shirin tafiya masallaci. Kuma hakan kyakkyawar dama ce a gareta, wadda za ta yi amfani da ita wurin isa ga abin da take burin cimmawa. Can ƙarshen ganuwar garin ta bangaren yamma ta yi, har sai da ta fara nisa da gidaje, sannan ne ta fara hango shi a jikin wata bishiya ya jingina. Matashin saurayin SA'EID ALI, na sanye cikin tufafin Dishdasha, wasu nau'in kayan larabawa na wancan ƙarnin, wanda ake saƙa shi da zaren lilin, kayan ba masu tsada ba ne, hakan ya sa kowa kan iya saka shi a rayuwar yau da kullum. Rigar Dishdasha doguwa ce, haka ma wandon rigar. Kansa babu rawani, hakan yasa kyakkywan gashin kansa kalar (brown) bayyana. Mujiyarsa da ya yi wa laƙabi da Aafa na a kan kafaɗarsa ta dama. Tun da ya hangota ya fara murmushi, ya gyara tsaiwarsa har ta iso gabansa, suka tsaya kallon juna, duk da shi kwarmin idanunta kawai yake gani, dan gaba ɗaya ta rufe fuskarta, bayan idanuwanta ba ka ganin komai. Hannunta na dama ta saka ta buɗe fuskarta, hakan ya bayyanar da kyakkyawar hallitar fuskarta gare shi. “Tsawon lokacin da na ɗauka ba tare da na ganki ba ya sanya na ji kamar duniyar nan ba ta juyawa sarauniyar kyawawa, da fatan kina cikin ƙoshin lafiya” Cewar Eid cikin muryarsa me sanyi. Murmushi Iqrah ta yi, sannan ta jinjina kanta, domin ba ta ji tana da amsar maganar tasa ba, dan haka kai tsaye ta tafi kan maganar da ta haɗasu a wurin. “Ban sani ba ko labarin auren da Abbu yake son haɗawa tsakanina da yarima ɗan sarkin Mamlakatul Azad ya riskeka!” Lokacin da ta kai ga ƙarshen maganar tata fuskar Eid ta sauya launi, daga farin cikin ganin abar begen zuciyarsa zuwa baƙin ciki mabayyani. “Gimbiyata me ya sa za ki bari su fara ƙoƙarin rabani da ke?” Ya tambaya a dugunzume, Iqrah ta girgiza kanta, sannan ya yi taku biyu zuwa gareshi, sannan ta saka hannunta ta kamo hannayensa. “Ko da numfashina zai rabu da gangar jikina ba zan taɓa bari wani ya rabani da kai ba Eid, domin kai nake so, ba na son wani bayan kai, kuma kai kaɗai nake so a matsayin ABOKIN RAYUWA!” (Anty Candy's new book, lolz). Eid ya girgiza kansa, tare da ƙwace hannayensa da ta riƙe, ya juya bayansa yana kallon birnin Jiyad, murya ɗauke da damuwa ya furta. “Ba haka ba ne Mehbuba. Ƙoƙarin haɗa aurenki da wani bayan ni na nufin zan rasaki har abada, kuma rasaki a rayuwata na nufin zuwan ƙarshen numfashina!” Iqrah ta sake girgiza kanta, sannan ta zagayo ta sake tsayawa a gabansa. “Da ace ka mutu kai kaɗai gara ace tare muka mutu, mu mutu ba tare da mun mallaki juna ba na nufin ba mu cimma burin soyayyarmu ba, dan haka ni na yanke shawarar mu guda kawai mu je domin a ɗaura mana aure!” Eid ya mata wani irin kallo, sannan ya girgiza kansa. “Ba na so Malik ya cutar dake Mehbuba ba zan iya zuba ido ina kallo a cutar min da ke ba” “A'a Eid, zan iya yin komai a kan soyayyarmu, dan haka na yanke shawarar za mu gudu tare da kai a ranar da za'a ɗaura mana aure da wancan yariman, kuma a wannan ranar nake so a ɗaura mana aure ni da kai masoyina” Eid ya tsaida dubansa a kanta. “Kin tabbata abar sona?” Ta gyaɗa kai. Daga haka suka shiga tsara yanda shirinsu na guduwa daga birnin Jiyad zai kansace. Ba tare da sanin abin da hakan ka iya jawowa ba. Sai da suka gama tsara shirin nasu, sannan ta masa sallama ta tafi. Sai da ta ɓace masa da gani, sannan Eid ya sheƙe da dariya, har da hawaye, kafin lokaci guda ya haɗe rai. Ya saka ɗan yatsansa ya ɗauke hawayen da ya zubo masa. “Dole ne Malik Cangaz ya biya bashin da ya ci... Kuma wannan kyakkyawar dama ce da zan yi amfani da ita wurin rama abin da ka min!” Lokaci guda kalar zaluncin da Malik Cangaz ya aikata masa ya shiga dawo masa, amma sai ya yi saurin ture komai, ya sauƙo da mujiyarsa dake kan kafaɗarsa, bayanta kawai ya shafa, ta rikiɗa ta zama ƙatuwa. Ya kama bayanta ya ɗale, sannan ta buɗe fukafukanta ta tashi sama da shi. Salma Ahmad Isah ✍️. _____________ _Ta ko ina littafin nan ya kama da wuta, dan ƙiri ya rage papers ɗin book ɗin su ƙone!🤣._ _Na ce muku tafiyar bana ta sha bamban da sauran_ _Dan haka sai ku sake shiryawa, domin jarumanmu na cikin tuƙeƙiyar matsala._ _Sannan kar a manta da biyan kuɗin book, regular group ₦400, VIP ₦800._ _Ku tura kuɗinku ta account details ɗin da zan rubuta a ƙasa_ 5487270431 Salma Isah Monie point A tura shaidar biya ta 08130172702. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-12 ADVENTURERS. Tafiyarsu ta miƙa a cikin dajika da tsaunika, sun yi tafiya irin wadda ba su taɓa yi ba a rayuwarsu, hatta shi kansa Uwais bai taɓa yin doguwar tafiya irin wannan ba, dan ko shi kansa ba sanin hanyoyin ya yi ba, ta hanyar wannan taswirar da suke ɗauke da ita ne kaɗai suke iya gane hanyoyi. Batun abinci kuwa tun kafin su ji yunwa Uwais yake kawo musu abin da za su ci, tun abincin ba ya musu daɗi har ya zamto sun fara sabawa da abincin. Ranar da suka cika kwanaki biyar da barin ƙauyen Askar cif, suka shiga wani daji me yawan dogayen duwatsu. Su huɗun cif suna tafe a tare, Arman da Adam na kan gaba, yayin da camera ɗin Adam ke rataye a wuyansa, dan ba ya rabo da ita, daga zarar ya ga abin ɗauka zai ɗauke shi a hoto. Ivana da Uwais kuma na daga baya suna hirar da suka saba yi a lokuta irin wannan. “Me yasa kake yawan kallona?” Ivana ta jefa masa tambayar, dan za ta iya cewa daga zarar tana wuri Uwais ba shi da abin kallon da ya wuce ita. “Saboda irin shigar da kike, da farko na ɗauka cewa ke ba musulma ba ce, sai da na ga yanda kike suturta jikinki lokacin da za ki yi sallah, amma kuma bayan kin idar sai ki yaye ki koma shigarki mai nuna tsaraici!... Sai na cewa kaina, idan har za'a suturta jiki yayin yin ibadar Allah, me zai hana a ci gaba da suturta jiki ko ba lokacin da za'a bauta masa ba, domin zamanki da irin wannan shigar na cikin saɓa masa!” Hatta Adam da Arman sai da suka tsaya suna dubansa, saboda ya yi magana ta hankali. Ganin suna kallonsa yasa yace. “Ku yi haƙuri fa, na fuskanci kamar hakan ba komai ha ne a zamaninku... Amma ni gani na yi ya kamata ace na faɗa mata gaskiya” Ivana ta dubi shigar dake jikinta ta slacks trouser peach color, da farar blouse, wandon sam bai kai idon sawunta ba, har gwanda ma rigar na da ɗan tsayi, kuma duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san cewa

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35