Chapter 27
Chapter 27
aura mata da kallo, fuskar nan a haɗe, dan sam babu alamar fara'a a tattare da ita, ta cika ta yi fam, jira take a tsikareta ta fashe tau!. Ba sai an yi wani tone-tone ba, sam ita matashin bai mata ba. Ba wai dan ba shi da kyau ba, ba kuma dan ba shi da nasaba me kyau ba, sai dan kawai Eid shi ne a zuciyarta. “... Yanzu amincewar Gimbiya kawai muke buƙata, daga zarar tace eh sai a saka ranar aure!’ Mahaifin yariman ya faɗa, Iqrah ta kalle shi, sannan ta kalli mahaifinta Malik Cangaz da shi ma ke zaune a ɗakin cin abincin. Amma shi sai ya ƙi ya kalleta, ya yi murmushi me kyau, sannan yace. “Babu buƙatar sai mun ji daga gareta, dan haka yanzu ma za mu iya saka ranar da za'a yi auren” Maganarsa ta tarwatsa duk wani fata da Iqrah ke da shi, kuma dalilin maganarsa yasa ta ƙudiri aikata abin da ba zai musu daɗi ba daga ita har shi. Ta kalli yariman tana jin kamar ta shaƙo wuyansa ta maƙure shi a bango har sai ya daina numfashi, sannan ta kalli mahaifinta, sai dai ba ta da ikon cewa uffan. Har suka gama yanke abin da za su yanke, aka sallameta. Champa da sauran hadimanta suka mata rakiya zuwa ɗakinta. Sai da suka sadata da ɗakinta, sannan ta sallami sauran hadiman, ta dakatar da Champa kawai. Sannan ta dubeta tana faɗin. “Gobe ki tabbatar kin zo min da kayan da kika saba kawo min na saka a duk lokacin da nake son na yi shigar ɓadda kama na fita, kada ki bari kowa ya san cewa gobe zan fita domin ganawa da Eid!” Kan Champa a ƙasa ta jinjina shi. “An gama gimbiyar kyawawa” Daga haka ta mata lamunim fita daga ɗakin. Tana shirin zama a bakin gadonta ASRA ta shigo ɗakin, kamar kullum, sanye ce kin shigar yaƙi, domin a ko da yaushe ita tana cikin shirinta na yaƙi. Kallon juna suka yi, kafin Iqrah ta ɗauke kai ta zauna a kan gadon cike da damuwa. Asra ta ƙarasa cikin ɗakin, sannan ta zauna kusa da 'yar uwarta me matuƙar kama da ita. “Ina kika tafi tsawon kwana uku bana ganinki?” Iqrah ta gefo mata tambayar bayan wani lokaci. Asra ta yi murmushi. “Malik ne ya tura mu yaƙar wani ƙauye dake cikin dajin Urf al-tawul... Tafiyar ta taso a bazata, shi yasa ban sanar miki ba kafin mu tafi!” Iqrah ta kalli 'yar uwarta, ita ke nan rayuwarta ba hutu, a ko da yaushe sarki na bata ayyukan da suka girmi hankali, har suna ganin kamar ya manta a mace aka haifeta ba namiji ba. Domin ya mayar da ita tamkar namiji, hatta da muryarta ta fi ta mata girma, yanayin tafiyarta da kuma shigarta ya banbantata ta mata, duk da ta kasance mace. “Darvesh (Holy man) yace min ya zaɓa miki mijin aure, hasali ma nan da mako guda za'a yi aurenki... Faɗa min kina farin ciki?” Asra ta tambaya, Iqrah ya juya idonta. “Bana farin ciki Asra, saboda bana son zaɓin Abbu, ni ina da wanda nake so, amma na san ko da na sanar masa da hakan ba zai goyi bayana ba” Asra ta dafa kafaɗar ƙanwarta. “Haka ƙaddarorinmu suke Iqrah, daga ni har ke ba za mu iya sauyasu ba, dole ne mu bi abin da Malik yake so, ko da kuwa mu ba ma ra'ayin hakan!” Iqrah ta miƙe tsaye. “Na daɗe ina bin duk wasu dokoki da zai kafa min, amma ba zan bi wannan ba...” “Me za ki yi ke nan?” Asra ta kasteta tana miƙewa ita ma. ”Zan gudu tare da wanda nake so!...” Ba ta rufe bakinta ba Asra ta sharara mata marin da ya yi sannadiyar fitar jini daga bakinta, sannan cikin zallar ɓacin rai ta nunata da yatsa. “Ki yi komai ba komai, amma yin kuskure irin wanda Sana ta tafka ba zan bari ki aikata shi ba...” Iqrah ta dafe wurin da ta mareta hawaye na bin kuncinta tace. “Tun da ke kin bari ya gurgunta miki rayuwarki sai ni ma na bari ya ruguje min rayuwa ta hanyar rabani da Eid? Duk abin da zai min sai dai ya min, amma ba zan taɓa rabuwa da Eid na auri wani ba...!” Asra ta sake ɗaga hannunta za ta sake marinta, amma sai ta fasa. “Mutuwa ce kaɗai za ta shiga tsakanin da dakatar da ke kan abinda kike son aikatawa... Zan yi komai domin ganin ban barki kin aikata irin abin da Sana ta yi ba, na gwammaci ace ni na kasheki da hannayena da na bari Malik ya saka miki ciwo irin wanda ya sakawa Sana...” Tana gama faɗin hakan ta fita daga sashin Iqra rai a ɓace. Yayin da Iqra ta kwanta a saman gadonta tana kuka. Salma Ahmad Isah ✍️ _______________ _Book one ya ɗauki hanyar ƙarewa, dan bai fi pages 5 ne suka rage a gaba ba._ _Idan kun shirya bibiyar wannan tafiyar sai ku biya ₦400 regular group. Akwai V.I.P ₦800._ _Za ku tura kuɗinku ta wannan account ɗin._ 5487270431 Salma Isah Monie point Sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar 08130172702. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-11 ƘAUYEN ASKAR. Mamaki ne yasa Ivana ta sandare a tsaye, sakamakon ganin wani mutum me kama da Uwais Fazil wanda ta sani a Dubai, kuma a zamaninsu, yanzu sai ga shi suna ganinsa a matsayin wani Uwais ɗin, amma Uwais bin Dhaakir. Banbancin wancan Uwais ɗin da wannan da take gani kawai shi ne dogon gashin dake kan wannan, sai kuma yanayin shigarsu. Amma za ta iya rantsewa da Allah kan wannan Uwais ɗin da ta sani a Dubai ne. “...Ivana!” Adam ya kira sunanta yana taɓata, a ƙokarinsa na dawo da ita zahiri, dan ya ga kamar ta lula duniyar tunani, firgigit ta yi ta kalle shi tana amsawa. “Me ya sameki?...” Ta kalli Adam, sannan ta juya ta kalli Arman, ta sake tsayar da dubanta a kan yarima Uwais dake tsaye a gabansu, shigar jikinsa ta ƙara kalla, sannan ta sake duban fuskarsa. Shi ma sai kallonta yake kamar ya santa a wani wurin, wata ƙila kuma shigar jikinta yake kallo... “Ku ci abinci” Cewar Tsohuwa Feroza tana aje musu wani tray dake ɗauke da Mujaddara, wani nau'in abinci na wancan ƙarnin, wanda ake yinsa da shinka, kayan lambu da kuma nama. Kasancewar suna jin yunwa yasa ba su musa cin abincin ba a wannan lokacin. Suka fara cin abincin a ɗarare, kamar suna cin dutse, dan sam abincin ba shi da ɗanɗano mai daɗi a baki, na kamar wanda suka sana ci ba. Shi dai Adam a ransa mamaki yake na yanda aka yi mutanen da suka rayu cikin farin ciki. Har suka ƙare cin abincin Ivana na satar kallon Uwais, kuma daga zarar ta kalle shi za ta ga shi ma kallonta yake. Har Arman ya fara lura da hakan. Amma bai mata magana a lokacin ba har suka kammala cin abincin, suka samu damar yin wanka, sannan suka sauya tufafi. Lokacin da suka gama shiryawa suka dawo 'yar farfajiyar gidan Feroza, inda suke tsaye ita da Uwais. Shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35