Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

shafa sumar kansa, tare da ƙifta idonsa a hankali, kuma bai bari ya kallesu ba. “Arman” Ivana ta kira tana zauna a gefensa. Dubanta kawai ya yi yana aje wayarsa dake riƙe a hannunsa, dan ba amfanin komai yake da ita ba, hasalima a kashe take, domin ba ya so wani na gida ya kirashi. “Kamar akwai abin da yake damunka?” Ta tambaya tana son su haɗa ido, amma ya ƙi bata damar hakan. Tun jiya da suka baro Dubai har zuwa yau ɗin nan ba ya jin daɗi sam, duk tsayin awa shidan da suka kwashe a jirgi kafin su iso Regen sam bai ji daɗinsu ba, hatta yanzu haka da yake zaune ba ya jin daɗi. Kuma jinyar ba a jikinsa take ba, a zuciyarsa take. “Ka ga Arman! Idan har kana jin hukuncin da ka yanke bai maka ba muna tare da kai. Idan kana jin cewa ka yi nadamar abin da ka aikata za mu kasance tare da kai, wannan rayuwarka ce, kuma lokacinka ne, ka yi abin da ya dace a lokacin da ya dace, ka yi tunani me zurfi a kan wannan hukuncin, duk abin da ka yanke za mu amince da shi. Ko da kuwa kana so mu koma Dubai a ranar yau ne za mu koma, mu dai burinmu shi ne ka yi farin ciki!” Cewar Adam yana dafa shi, ya ɗaga kai ya kalli Adam, sannan ya kalli Ivana dake jinjina masa kai, alamun abin da Adam ya faɗa haka ne. Ya sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, sannan ya shafa kansa yana rinte ido. “Mu za mu tafi siyayya. Ka tabbatar ka yanke hukunci kafin mu dawo” Cewar Ivana tana miƙewa, tare da ɗaukan bag ɗinta, ta bubbuga kafaɗarsa sau biyu, sannan tace da Adam su tafi, suka tafi suka bar shi cikin tunani me zurfi. Ivana da Adam sun zaga sosai a cikin garin Regen, kuma tun a cikin garin ma Adam ya samu ya ɗauki wasu hotuna. Sun shiga manyan kantuna da gidajen abinci, domin sun ɗauki alƙawarin shiryawa abokinsu babban bikin ƙarin shekara. Ta hanyar siya masa kyautuka da dama. Yayin da suke siyayya a cikin wani shagon da ake saida kayan tarihi irin na da can. Adam ya yi arba da wata sarƙa a cikin wani kit, zaren sarƙar baƙi ne, pendant ɗinta kuma wani abu ne me kama da key, kuma daga ganinsa an ƙera shi ne da gold. Tsabar muhimmanci da darajar sarƙar a keɓe take a cikin shagon, an sanyata cikin wani glass me ɗaukar ido. “Wannan ta kai kimanin nawa?” Ya tambaya yana ɗaukan glass ɗin da aka sakata a ciki, me kantin ya yanko maƙudan kuɗaɗe ya faɗa, duk da sarƙar ta yi tsada hakan bai sa Adam ya fasa siyawa Arman ita ba, domin ko da zai ƙarar da kuɗin da yake da shi zai yi domin faranta ran Arman. Ita kuma Ivana sabon takobin fencing ta sai masa, da wasu ƙanun kyautuka da ta san za su burgeshi. *Dubai...* “Ina zuwa!” Faɗin Maama dake wanke hannu a sink, yayin da take kallon ƙofar gidan da ake ƙwanƙwasawa. Hannunta ta goge, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, mamaki ya kamata, ganin Sayyid Iƙbal Alhadi da matarsa Zahra, da kuma 'yarsu Gulzar. “Barkanku da zuwa... Ku shigo ciki mana” Ta faɗa tana murmushi, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Abby ya ɗan yi murmushin yaƙe yana mata sallama, ta amsa yayin da yake shiga falon, ita kam Immi babu wata alamar walwala tare da ita, ta yi sallamar kamar da aka mata dole, sannan ta shiga falon ita ma, Gulzar kuwa bayan ta yi sallamar sai da ta gaida Maama sannan ta shiga. Su duka ukun a falo suka zauna, yayin da Maama ta koma flat kitchen ɗinta ta ɗauko abin sha, ta aje musu a center table suna sake gaisawa. “Shin Adam yana nan?” Abby ya tambaya, mamaki ya sa Maama ta kallesu, kafin cikin kokwanto tace. “Adam? Ai jiya suka tafi Regen, Germany, kuma yace min tare da Arman za su tafi, ko dai Arman ɗin bai samu zuwa ba?” Abby ya dafe kansa. Yayin da hawaye ya zubowa Immi. “Arman guduwa ya yi ya bar gida ba tare da saninmu ba, yanzu haka ba dan kin faɗa ba da ba mu san inda yake ba” Maama ta yi shiru, ta san irin haka sam ba daɗi. Da ace ita ce a matsayinsu da yanzu ita ma nata hankalin a tashe yake. “Sayyid Iƙbal ka yi haƙuri, haƙiƙa abu irin wannan babu daɗi, amma su yaran yanzu idan har suka yanke hukunci babu wanda ya isa ya tablnƙwarasu, dan za su iya aikata abin da suke so a ɓoye ba tare da sun sanar da kai ba, ku yi haƙuri ku ci gaba da masa addu'a” Abby ya dubi Maama, sannan ya yi murmushi kawai. Dan shi tun da har ya san inda yake matsala ta kau, Arman ba ƙaramin yaro ba ne da zai ɓata, ya sha yin tafiye-tafiye irin wannan, kuma shi kaɗai, dan haka yanzu hankalinsa ya kwanta, domin ko ba komai idan ya gama kwanakin nasa a Regen dole zai dawo gida!... “Allah ya kareka shugaba!” Shi ne kawai abin da ya furta. Dan ba ya jin yana da wani abin cewar bayan wannan. *Regen, Germany.* Adam ya ja tsaki a karo na barkatai, yayin da suke duban ƙofar hotel ɗin da suka kwana ciki, tsaye suke shi da Ivana da kuma Arman, a jikin motar da suka yo hayarta yau, domin yau ne za su shiga Bavarian forest. Ga shi rana ta kusa faɗuwa, amma har yanzu Hans bai zo ba. Ivana na sanye cikin purple crop top, me ɗauke da ratsin baƙi-baƙi, da kuma wideleg bleach jeans, takalminta farin orthopedic sneakers ne. Gashinta ya sha gyara cikin style ɗin side braid pony tail, ta saka wani purple hair clip a karshen side braid ɗin. Yayin da ta ɗora baƙar wide brim hat a kanta, wadda za ya sauƙaƙa mata zafin ranar da ake, idonta manne da shade. Adam kuma na sanye da maroon chinos trouser, da farar shirt, wadda ya ɗora mata ash hoodie a sama. Shi ma ya saka shade, saboda duk da rana ta kusa faɗuwa akwai zafinta har yanzu. Ƙafafunsa kuma na cikin farin huaraches. Yayin da Arman ke sanye da gray khaki trouser, da farar shirt, wadda ya ɗorawa black bomber jacket a sama. Saɓanin sauran da suka saka shade shi glasses ɗinsa na kullum ne a idonsa. Ƙafafunsa na cikin farin canvas. Shi ma tsakin ya ja yana shafa sumar kansa, sannan ya dubi su Adam. “Ya kamata mu tafi fa, dan da alama wannan ba shi da niyyar zuwa.” “To da kake cewa mu tafi mun san hanyar ne?” Cewar Adam, ya musu banza ya buɗe driver seat na motar ya shiga, har ya tada motar Ivana da Adam na kallonsa. Ganin ba su da niyyar shigowa motar yasa ya kallesu. “Dare ne yake shirin yi, da dare ya mana a hanya mu ɓata, gara daren ya mana a cikin dajin. Matambayi ba ya ɓata, kuma Bavarian forest sannanne ne a ko ina, ba za mu rasa wani ɗan rakiyar ba a hanya... Dan haka ku zo mu

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35