Skip to content

Chapter 28

Chapter 28

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

ma da jakarsa a tare da shi, alamun dai ya gama shiryawa za su ci gaba da tafiya. Tsaye suka yi suna kallon uwar da ɗanta suna sallama, da alama duk tsawon shekarun da suke rayuwa tare ba su taɓa rabuwa da juna ba sai a sannan karo. “Ka tabbatar sun isa inda suke son zuwa cikin aminci!” Faɗin Feroza tana danƙawa ɗanta taswirar da su Arman suka bata, Uwais ya karɓa yana murmushi, sannan ya sakata cikin jakar kayansa, kana ya rungumi mahaifiyarsa. “Ki min addu'a ya Umma” Ya faɗa suna sakin juna, Feroza ta shafa kansa. “Addu'ata za ta kansace tare da kai a duk inda ka sa ƙafa yarimana” Ya yi murmushi me kyau, sannan ya ɗauki jakarsa. “Sai Allah ya mana dawowa Umma” Feroza ta share ƙwallar da ta zubo mata, tana kallonsu har suka fita daga gidan, ta cikin ɗan ƙaramin ƙauyen suka bi, mutanen ƙauyen suka yi ta binsu da kallo, sakamakon yanayin shigarsu Arman, dan ba su yi kama da mutanensu ba. Shi ko Adam hotunan ginin ƙauyen da kuma na mutanen ƙauyen ya shiga ɗauka, yayin da Ivana da Uwais suka ci gaba da satar kallon juna. Har suka fita daga ƙauyen suka nausa cikin daji, sun yi tafiya me matuƙar tsayi, kafin suka samu yada zango a cikin dajin, suka zauna suna hutawa, yayin da Uwais ya tafi naima musu abin da za su ci, sai a lokacin Arman ya fasu ya tambayi Ivana abin da ke ransa. “Ivana kin san Uwais a wani wuri kafin nan?” Duk da tambayar ta zo mata a bazata sai da ta yi murmushi, yayin da take karkaɗe jakar guitar ɗinta. “A ina za ta san shi? Ita da mai tafiya a tsakanin zamani ba?” Adam ya rigata bawa Arman amsa, amma sai ta girgiza kansa. “Ko kaɗan, mun taɓa haɗuwa da wani Uwais ɗin da ban a Dubai!” Adam ya zaro ido yana kallonta. “Kun taɓa haɗuwa? Ke nan har a zamaninmu yana raye bai mutu ba? Da ma fa aljannu suna da taurin rai, shi yasa nake kaffa-kaffa da shi, dan Wallahi tsoronsa nake ji” Ivana ta yi dariya. “Ba lalle ace shi ba ne, amma wancan zai iya kasancewa me kamarsa ne” Arman ya gyara zaman glasses ɗinsa yana jinjina kai. “komai zai iya kasancewa, kuma shi ma sai kallonki yake ta yi, kamar ya sanki” Ivana ta sake darawa. “Ban sani ba” “Ga shi can ya dawo” Cewar Adam yana nuna Uwais da ya nufo wurin da suke. “Barkanku da hutawa” Cewar Uwais yana aje jakar da ya zo da ita. Su dai kallonsa suke, an ce musu rabinsa mutum ne kuma rabinsa aljani, amma su dai mutum suke gani. “'Ya 'yan itaciya ne na samu, da fatan za ku iya ci” Ya ƙarashe yana duban Ivana, Ivana ta ɗan yi gajeren murmushi tana kallonsa ita ma. “Me zai hana mu iya ci” Arman ya ja jakar yana faɗa, Uwais ya zauna a gefe yana nasa murmushin, suka fitar da kayan dake ciki, har suka fara ci amma shi Uwais sarewarsa ma yake gogewa. “Kai ba za ka ci ba?” Cewar Arman yana dubansa, sai ya kalle shi. “Ba na jin yunwa yanzu, daga zarar na ji yunwar zan naimi abinci” “A ƙalla kana iya kwana nawa ba tare da ka ci abinci ba?” Adam ya tamabaya. “Mako guda” “Mako guda sati ɗaya ke nan?” Adam ya zaro idanuwansa cike da mamaki. “Wannan fa, mi ye a hannunka?” A wannan karon Ivana ce ta yi tambayar, sai ya kalleta. “Sarewa, takobi kuma baka!” “Sarewa, takobi kuma baka duka lokaci guda?” Faɗin Arman. “Eh, na kan iya yin busa da ita a lokacin da nake bukata, na kan iya juyata ta koma baka idan ina son kare kaina, amma kuma ainahinta ta kasance takobin mahaifina!” “Ke nan wannan ita ce takobin sarautar da sarki Safraz yake naimanta?” Cewar Adam. “Ƙwarai, ita ce, kuma na san yanzu haka zai samu labarin bayyanar takobin, sannan zai iya yunkurin ƙwaceta daga hannuna ta ko wace hanya” Matasan uku suka dubi junansa, a lokacin da tunani ɗaya ya ziyarci ƙwaƙwalansu. Sun fuskanci cewa haɗuwarsu da Uwais ba sauƙi zai kawowa lamarinsu ba face ƙarin wasu ƙalubale da kuma matsaloli. Da ace Malik Cangaz kaɗai za su yaƙa abin zai iya zama da sauƙi, tun da shi bil adama ne, amma faɗa da aljani ai abin ya girmi tunanin me hankali!. MAMLAKATUL AFSAH. Fadar masarautar cike take da 'yan majalissar sarki, yayin da sarki ke zaune a kan karagarsa, ana ta gudanar da sha'anin mulki. Sarkin na bayar da wani jawabi a kan wata matsala da ta kunno kai a masarautar. Cak ya tsaya da jawabin da yake, lokacin da ɗaya daga cikin masu gadin babbar ƙofar shigowa fadar ya shigo fadar da sauri, ya zube a gaban sarki ya kwashi gaisuwa. “Sarki ya amsa bafade, faɗi abin da ke tafe da kai kanka tsaye!” Cewar waziri, Ba fade ya risinar da kai, sannan ya furta. “Ya shugabana yanzu muke samun masaniya daga dakarun ɓoye dake bibiyar lamarin takobin mulki da kuka aika... Cewar suna jin alamun an fito da takobin daga maɓoyarsa” Babu shiri sarki ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa, domin haƙiƙa batun ya girgiza tunaninsa, ba ma shi kaɗai ba, hatta da sauran fadawansa sai da batun ya saka suke miƙe tsaye. A ƙalla yanzu an kwashi shekaru sama da ashirin, babu wani batu daga masu biciken takobin sai yau... “Ina wakilan ɓoye suke? Duk inda suke a tabbatar an naimo min su, an kawosu nan” Hadimin ya miƙe a kan ƙafafunsa yana risinar da kansa a gaban shugabansa tare da faɗin. “An gama adalin sarki!” Har hadimin ya fita daga fadar idon sarki na kan ƙofar shigowa fadar, yana saƙa mabanbantan abubuwa a ransa, shin me zai sa Feroza ta fito daga maɓoyarta bayan wasu shekaru masu tsayi? Imma dai ya kasance takobin ya bayyana ne ba tare da saninta ba, ko kuma ta bayyanar da shi da gayya, domin akwai wani abu da ta taka. Ko ma dai mene ne, shi ba zai sauka a daga kan ƙudirinsa na son ganin ƙwatar takobin daga gareta ko ɗanta. IQRAH. Tun a safiyar yau ta shirya tsaf a ɗakinta, tana jiran zuwan Champa domin ta kawo mata tufafin da ta saba sakawa a duk sanda take son ta yi fitar ɓadda kama ba tare da sanin kowa a fada ba. Lokacin da Champa ta kawo mata kayan yi ta yi kamar za ta sumbaceta dan farin ciki, cikin hanzari ta saka baƙaƙen tufafin a jikinta. Sannan ta rufe fuskarta, ta jawa Champa kunne kan kada ta kuskura ta fita daga ɗakinta, kuma duk wanda ya zo ganinta ta sanar da shi ita tace ba ta buƙatar ganin kowa. Da haka ta samu ta silale ta fita daga ɗakin, ta yi ta ratsawa ta faluka da wuraren hutawa dake cikin fadar. Har ta samu ta fita harabar fadar babu wanda ya ganeta, dan kanta a ƙasa take tafiya, yayin da ta sauya salaon takunta. Duk yawan masu gadin fadar da hadimai dake kai kawo babu wanda ya iya ganeta, da haka ta kutsa cikin gari, kyakkyawan birnin Jiyad na da kyawawan gine-gine irin na waccan

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35