Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kafaɗunta tare da taɓe bakinta. “Da ace Arman zai karɓi shugabancin nan Yumma da an yi shugaban da ba'a taɓa yin irinsa ba” Yumma ta girgiza kanta. “Allah ya karkato da zuciyarsa kan kamfanin, su kuma Allah ya musu abin da suka masa” “Amin” Ta amsa dai-dai lokacin da wayarta dake chaji a kan side drawer ta fara ringing, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar, ganin lambar Uwais Fazil ya sa ta ɗaga wayar, tare da karawa a kunnenta. “Marhaba” Muryarsa me sanyi ta faɗa daga ɗayan ɓangaren. “Alo” Ta faɗa tana murmushi. “Shin zan iya ganinki?” Sai ta kalli Yumma da ke shirya mata kaya, da alama sam ba ta lura da wayar da take ba. Sai ta sauƙa daga kan gadon tana saka toe wrap shoes ɗinta dake kusa da gadon, sannan ta fita daga ɗakin. Sai a sanda take sauƙa downstairs sannan ta amsa. “Zan so hakan, domin ina sa ran zan yi tafiya nan da gobe...” “Yanzu haka ina ƙofar gida me lamba 27, titi na 45, a tsakiyar unguwar Mirdif.” Ido ta zaro tana rufe baki, sannan cikin sanɗa ta isa jikin windown dake kusa da ƙofa, ta ture curtain ɗin dake jikin windown ta leƙa. Daga nan inda take ta samu damar ganinsa, jingine a jikin motar da ya zo da ita. Yana sanye da baƙin sweat blazer trouser, me ratsin ja a gefe, da farar crew-neck sweater, wadda ya saka baƙar shirt a ƙasanta. Ƙafafunsa cikin garin sneakers. Gashin kansa na cikin askin high pade, sannan wayarsa kare a kunnensa, kuma suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu, sai ta yi saurin sakin curtain ɗin tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ina jiranki” Ba tare da tace komai ba ta sauƙe wayar, sannan ta koma sama da gudu. Har Yumma na tambayarta shin lafiya, ta amsa mata da tana zuwa. Guitar ɗinta kawai ta saka a cikin jakarta, sannan ta ɗauki canvas ɗinta ta saka a ƙafarta, ta tsaya a jikin mirror ta gyara gashin kanta. Sannan ta goya jakar guitar ɗin a bayanta, ta fita ba tare da mayafi ba, dan ta saba yin hakan kullum. Ba ma ita kaɗai ba, a muslman 'yan matan larabawa ba kowacce ce ke saka mayafi lokacin da za ya fita ba. Mafiya yawan waɗan da za ka ga da mayafi a waje to matan aure ne, dan 'yan matan ba su cika yin hakan ba, shi ya sa idan aka gansu a waje za a ɗauka cewa ba musulmai ba ne, dan duk wasu ɗabi'u na turawa sun ɗauka sun yafa a jikinsu. “Ina ya kamata mu je?” Uwais ya tambaya yana duban Ivana dake zaune a kujerar gefensa. Yayin da yake tuƙa motarsa cikin nutsuwa, kuma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana kan bakinsa. Ivana ta kalli hanya tana murmushi. “Duk inda kake ganin zai yi kyau da zama a lokaci irin wannan” Ya sake dubanta, sannan ya ɗauke kai yana dariya, bluewaters island shi ne wurin da ya fara zuwa ransa. Dan haka ya nufi wurin, a gefe ya samu wuri ya faka motarsa, sannan suka fito daga motar, yana riƙe da bag ɗin guitar ɗinta. Yayin da suka jera suna tafiya a cikin yammacin. Daddaɗar iskar da ruwan wurin ke badawa tana busawa a ko ina, akwai kaikawon mutane a wurin, kowa yana harkar da ta kawo shi. Da haka suka samu wani bench suka zauna. Kafin Uwais yace bari ya siyo musu abin sha, tana zaune a wurin har ya siyo ya dawo, ya bata drink ɗin, ta masa godiya tana kallonsa yayin da yake zama, a lokaci guda ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar wurin dake kaɗa gashin nata. “Ina za ki je?” Uwais ya tambaya. Sai ta kalle shi tana shan drink ɗin da ya bata, sannan ta jinjina kanta. “Akwai abokina da zamu taya murnar ƙarin shekara. Dan haka muka shirya tafiya zuwa Germany” Ta ba shi amsa tana kallon wheel ɗin dake wurin. Uwais ya jinjina kansa. “Kamar kwana nawa kike ganin za ki yi?” Ta ɗan juya idonta, sannan ta tura gashinta baya tana faɗin. “A ƙalla sati ɗaya... Da wani abu ne?” Sai ya girgiza kansa yana kallon bottle ɗin drink ɗin dake riƙe a hannunsa, sannan ya sake dubanta. “Idan kin dawo akwai wani abu da nake so na sanar dake” Ivana ta yi murmushi me faɗi. “Me ya sa ba yanzu ba?” “Saboda ba na so wani abu ya katse ƙudirina a kanki, na fi so sai kin je kin dawo...” Ta yi shiru kawai, dan ba ta san me za ta sake cewa ba kuma. “Ina son kiɗan guitar, ko za ki kaɗa min?” Ya katse shirun yana ɗaukan bag ɗin guitar ɗinta. “Akid (of course)” Ta aje bottle ɗin hannunta a tsakiyarsu, sannan ta karɓi guitar ɗin, ta cireta daga cikin jakar, ta ɗorata a kan cinyarta, sannan ta riƙe neck ɗin guitar ɗin tare da ɗora hannunta a kan frets dake jikin neck ɗin. Ɗayan hannun nata kuma na kan body ɗin guitar ɗin, yayin da yatsun hannun ke kan sound hole na guitar ɗin, sai da ta dube shi, sannan cike da ƙwarewa ta soma kaɗa guitar ɗin. Cikin wani irin sauti me daɗin gaske, me sanyayawa tare da kwantar da hankalin mai sauraronsa. Ko daga nesa ka jiyo kiɗan dole ya ɗauki hankalinka. Dan ba ta daɗe da farawa ba masu wucewa suka fara tsayawa kallonta, har da wasu yara da suka tsaya a gabanta suna rawa, ba ita kaɗai ba, hatta Uwais abin ya ba shi nishaɗi. Salma Ahmad Isah ✍️ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-6 *MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.* ARMAN POV. Tun yana cikin hall ɗin horar da wasan takobin Gulzar ke kiran wayarsa, amma bai ɗaga ba, har sai da ya je office ɗin shugaban wurin, ya ɗauki izinin hutu na sati ɗaya, dan sati ɗaya shi ne tsawon lokacin da suka tsara za su yi a tafiyar tasu, ba tare da sanin abin da zai biyo baya ba. Sai da aka lamince masa, sannan ya yi godiya ya fito daga office ɗin yana jan tsaki, saboda wani kiran Gulzar ɗin dake shigowa wayarsa. Tafiya ya fara a cikin business Bay, yana gyara zaman glasses ɗinsa. Sanye yake da plain hoodie ash color, da kuma baƙar denim jacket da ya ɗora a saman hoodie ɗin. Sai ligh blue baggy jeans, ƙafafunsa na cikin farin huaraches, ya saka baƙar p-cap a kansa, wadda ta taimaka wurin rufe sumar kansa da a kullum take cikin curly top, amma duk da haka sai da gashin ya fito ta jikin hular, kasancewar ya juya rumfar hular ƙeyarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya ɗaga kiran Gulzar. “A ƙalla na maka kira ya kai ashirin! Amma sai yanzu ka ga damar ɗagawa?” Ta soma da ƙorafi, Arman ya rufe motarsa ƙirar Rimac C_two, jar kala, dan yau da ita ya fito. “Ina class ne, ni ba na son ƙorafi, faɗi me zan miki?” “Shopping za ka zo ka kaini” Ta amsa daga cikin wayar, Arman ya saki baki. “Duk direbobin gidan nan a rasa wanda zai kaiki shopping sai Arman?” Ya tambaya yana

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35