Skip to content

Chapter 15

Chapter 15

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

tsareku, ya dawo da kai lafiya” “Amin Maama” Ya amsa yana ɗaukan jakar da ya aje. Sannan ya ɗaga mata hannu, ya juya zai fita, cikin raha Maama tace. “Kett!” Ya tsorata yana juyowa tare da kallonta. Maama ta kwashe da dariya, shi ma da ya gane cewa zolayarsa take sai ya yi dariya. “Ai zan daɗe ba na nan, sai na ga wanda za ki zolaya kuma” Ya faɗa yana fita daga gidan. A bayan motarsa ya saka jakarsa, domin sun yi da Ivana da kuma Arman kan a motarsa za su tafi airport. Domin shi Arman ba ya so kowa ya san cewa ba ya gida a lokacin da suke gudanar da shagalin ƙarin shekararsa. Shi ya sa ba zai ɗauki ɗaya daga cikin motocinsa ba. Kai tsaye gidansu Ivana ya nufa, da yaje gidansu ma ya daɗe, domin Ivana dake sallama da Yumma da kuma 'yar uwarta Hala. Kamar wata wadda za ta bar duniya haka ta fara hawayen bankwana da su Yumma. Sai da ban banki sannan ya samu ya ɗauketa suka tafi gidan Iƙbal Alhadi, a bayan gidan ya tsayar da motarsa, sannan ya kira Arman... ARMAN POV. Tsaye yake a balcony ɗin ɗakinsa, hannayenssa zube cikin aljihu, yana kallon masu aikin decoration na decorating garden ɗin gidan, dan daga nan inda yake yana iya ganin duk abin da ke wakana a garden da kuma wurin swimming pool ɗin gidan. Haka kawai yake jin kamar bankwana yake da kowa da komai, kamar wannan hukuncin da ya yanke ya yi tsauri da yawa, kamar idan ya aikatawa ahalinsa hakan sam ba za su ji daɗi ba, daga can ƙasan zuciyarsa kuma akwai wani abu da yake marmari da son tafi Bavarian forest, ba zai ce ga dalili ba, domin bai taɓa zuwa dajin ba, hasali ma sau ɗaya ya taɓa zuwa Germany... “Wai har yanzu ba ka shirya ba Arman?” Ya jiyo muryar Immi na faɗin hakan a bayansa, hakan ya sa ya juya ya kalleta, hannayensa zube cikin aljihu. Tsaye take a tsakiyar ɗakin nasa, hannunta riƙe da wani box me faɗi, wanda ya san cewa tufafi ne sabbi a ciki. Ta sha adonta cikin wani maroon chickankari, me ɗauke da ratsin golden. Wuyanta kunnenta da hannayenta duka ta saka jewelry masu tsada, fuskarta ta sha kwalliya, wadda ke ɓoye yawan shekarunta. “Shu? Ka'annak mu farhan ibini?” (Miye? Kamar ba ka farin ciki ɗana?). Ta tambaya ganin yanayinsa, ya girgiza kai yana nufota. Yana zuwa kusa da ita ya kama hannunta. “Kin yi kyau fiye da kullum Immi. Kamar yayata ba mahaifiyata ba” Immi ta aje box ɗin da ta shigo da shi, ta daki kafaɗarsa, ya yi dariya yana kallonta. “Sai ga shi kuma ni mahaifiyarka ce ba kakarka ba.” Ya kalleta yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya dafa kafaɗarta. “Da gaske kin yi kyau” Immi ta yi murmushin jin daɗi, Arman ya dawo gefenta yana dafa kafaɗarta ɗaya, tare da zaro wayarsa a aljihu yana faɗin. “Bari na ɗauki hoto” Ya ɗaukesu a hoton, sannan ya nuna mata. “Ya yi kyau. Ga su nan, kaya ne da na saka aka maka tun daga kamfani, ka yi maza ka shirya ka fito, masu kawowa cake sun kusa zuwa.” Ya kalli box ɗin yana jinjina kai, sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa da kiran Adam ke shigowa. Bai ɗaga kiran ba, ya jefa wayar a aljihunsa, ya samu ya lallaɓa Immi ta fice daga ɗakin, paper da pen ya ɗauka, ya yi rubutu a kai, sannan ya aje papern a kan box ɗin kayan da Immin ta kawo masa. Sannan ya ɗauki wayarsa ya kira mai aikin gidan da ya bawa ajiyar jakarsa, yace masa ya kai motar Adam, tana bayan gida. Daga haka kuma shi ma ya saɗaɗa ya fice daga gidan, ba tare da ya bari kowa ya ankara da shi ba. *11:40 na wannan daren.* Ko ina ka kalla a garden ɗin gidan Iƙbal Alhadi mutane za ka gani, cikin shigar da za ta sanar da kai tsadar kuɗin kayan da suka saka. Kuma ko ina na garden ɗin an ƙawata shi da kayan decoration wanda suka sa daren ya ƙara armashi. Daga can wajen kan wani table kuwa, cakes ne kala-kala, manya da ƙanana, ban da wasu nau'ikan drinks da snacks. Immi da Abby da kuma Gulzar ne tsaye a kusa da wurin, kowa ka kalla a cikinsu za ka ga yana cikin farin ciki. Kuma haka wasu daga cikin 'yan uwan Abby ma. Amma wasu daga cikin waɗan da suka san shirin da Abby ke yi na miƙawa ɗansa ragamar kamfanunuwan Alhadi akasin farin cikin suke. Musamman Anwar da yaransa, kai da ka kallesu ka san dole aka musu na zuwa wurin shagalin, dan Jadda ce ta kafawa kowa tsatssauran warning kan kada wanda ya kuskura wannan shagalin ya wuce shi, shi ya sa suka zo ba dan suna so ba, sai dan an musu dole. Ganin sha biyu saura ya sa Abby ya kira Gulzar gefe. “Ina ɗan uwanki ne? Tun ɗazu ban ga gilmawarsa ba. Kuma ko ɗaya daga cikin abokansa ban gani ba, duk da na turawa kowa katin gayyata, kuma shi ma na san ba zai kasa sanar da su ba” ”Yana ɗakinsa fa Abby, kuma wata ƙila su ma su Adam ɗin na tare da shi a can, bari na je na kira shi” Cewar Gulzar. “Ki yi maza ki kirashi ya sauƙo, dan sha biyu ta kusa cika” “To Abby” Ta amsa, sannan ta nufi hanyar falo, da ƙyar ta samu ya hau sama, sannan ta shiga ɗakin Arman. Tris ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakin, ganin babu kowa a ciki. “Akhi! Akhi?” Ta kira tana leƙa kanta, jin shiru yasa ta ƙarasa shiga ɗakin, ta tsaya dube-dube, kafin ta nufi bathroom ta ƙwanƙwasa, amma shiru, babu alamar ma akwai mutun ciki, sai ta buɗe ƙofar bayin ta leƙa tana kiransa. Ganin baya cikin bayin yasa hankalinta ya fara tashi. Dan haka ta dawo ɗakin da gudu, tana shirin barin ɗakin ta yi arba da box ɗin dake kan hadonsa, kuma ta lura da wata paper dake kai, dan haka ta dawo jiki a sanyaye ta ɗauki takardar ta shiga karantawa. Ai ba ta gama karantawa ba ta fashe da kuka, sannan ta fita daga ɗakin da gudu, ta koma garden. Tun da Abby ya hangeta daga nesa ya gane cewar ba lau ba, dan haka ya yi saurin isa gareta yana tambayar abin da ya faru, kuka kawai ta sake fashewa da shi ta faɗa jikinsa tana rufe bakinta, kukan da take da tambayarta da Abby ke yi na me ya faru ya janyo hankalin baƙi da 'yan uwa. “Ke Gul mi ye haka?” Immi ta tambaya tana nufo wurin da suke tsaye ita da Abby, amma sai ta kasa amsata, ta shiga girgiza kai kawai. “Gul! Gul! Ina yayanki?” Jadda ta tambaya tana ɗagota daga jikin Abby, yanzu ma bata yi magana ba, sai takardar dake hannunta da ta miƙawa Abby, Abby ya karɓa hannunsa na rawa, dan sam zuciyarsa ta kasa gaya masa abu me daɗi a kan Arman a halin da ya ga Gul ta dawo bayan ta tafi kiran shi. _“Ina da tabbacin a lokacin da za

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35