Chapter 33
Chapter 33
a ko ina na wurin, sannan akwai iska me daɗi dake busawa a ko ina. Hadimanta na zaune a ƙasa, yayin da suke bata labaran nishaɗi, ita kuma sai murmushi take. Domin duka wasu tsare-tsare da suke ita da Eid na guduwarsu a ranar da za'a ɗaura aurenta ya kamalla, hatta da ƙauyen da za'a ɗaura musu aure Eid ya zaɓa musu. Yanzu ranar ɗaurin auren kaɗai suke jira, domin sun yanke cewa ba za su gudu ba sai a ranar da za'a ɗaura auren. Buɗe ƙofar shiga sashen da aka yi ya sa hankulansu ya koma zuwa wurin, Asra tare da wasu bayi har uku ne suka shigo wurin. Ko wacce baiwa na ɗauke da wani (tray) da aka rufe da ƙyalle. Asra na sanye da wata Thawb kalar ruwan zuma, ta ɗora Muƙawar a kanta, wanda bai ɓoye dogon gashin kanta ba, tana tafiyarta irin ta jarumai, dan sam ba ta tafiya irin ta sauran mata. Da hannu ta yi wa hadiman Iqrah alama da su basu wuri, hakan ya sa duk suka fice daga wurin, Iqrah ta miƙe tsaye tana kallon 'yar uwarta. “Barka da zuwa Ukti!” Cewar Iqrah tana murmushi. Ita kuma Asra sai ta murtuke fuska tana binta da kallon tuhuma, dan haka kawai take jin ba ta yarda da ita ba. Da farko tace mata ba ta son wannan haɗin auren, ya za'ayi yanzu kuma ta zo tana murmushi?... Dole dai da akwai abin da take ƙullawa. “Sarƙoƙi ne Darvesh ya aikoni da su, yace a kawo miki ki zaɓi wanda kike so” Cewar Asra, tana yi wa bayin alama da su nunawa gimbiya kayan da suka zo da su. Iqrah ta nufi wurin bayin, ta ci gaba da duba sarƙoƙin, sai fara'a take abinta. “Wannan sun fi kyau” Ta nuna wadda ta fi burgeta. Hakan ya sa Asra ta duba wadda ta zaɓa, ba tare da ta furta komai ba ta sallami bayin, sai da suka fita sannan ta dubi 'yar uwarta da kyau. “Ina mai fatan Allah yasa ba wani abin kike shiryawa ba” Cewar Asra, Iqrah ta kuma yin murmushi. “Kada ki damu 'yar uwa, ba zan aikata abin da yake ba dai-dai ba!” “Ni ma haka nake fata” Cewar Asra tana jinjina kai, da haka ta fita ta bar Iqrah a wurin. Salma Ahmad Isah ✍️ _Pages ɗaya ya rage book 1 ya ƙare, idan regular group kike so za ki tura ₦400 through account details ɗin da zan rubuta a ƙasa. Idan kuma VIP ne sai a tura ₦800._ 5487270431 Salma Isah Monie point Shaidar biya kuma ta 08130172704. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-14 MAMLAKATUL AFSAH. Zaune a gaban Malik Safraz Natila ce, sanye cikin baƙaƙen kaya, amma yau fuskarta ba a rufe take ba. Ta nutsu tana sauraron buƙatar Malik da yake so ta biya masa. “Idan dan ta wannan ne kada ka damu Shugabana. Zan tattaro sauran yarana, za mu bisu har zuwa cikin dajin da suke, kuma zan tabbatar da na ƙwato maka takobinka!...” Malik Safraz ya yi murmushi, dan ya san aikin Natila, idan tace za ta yi to za ta aikata. Ya sha sakata ayyuka makamantan wannan, kuma cikin sa'a tana nasara. Miƙewa tsaye ya yi, yana goya hannayensa a baya, sannan ya ƙarewa katafaren falon da suke ciki kallo, kana ya juya bayansa yana faɗin. “Idan kuwa har kika kawo min wannan takobin, zan miki gagarumar kyautar da ban taɓa miki irinta ba!” Natila ta miƙe tsaye, sannan ta amsa da. “Zan kasance me cika alƙawari kan abin da na alƙauranta maka shugaba, ba zan taɓa baka kunya ba!” Malik Safraz ya sake murmusawa, sannan ya juyo ya dubeta. “Ki je domin ƙwato min takobina!” Ta risina alamun ta amsa. Kana ta ɗaga kai, kafin kace me har ta ɓace. A lokacin kuma Anser mahaifin Safraz ya iso falon shaƙatawar sarkin tare da masu take masa baya. Sai da ya isa falon sannan ya yi musu izini da su jira shi a waje, sai da suka fita sannan ya dubi ɗansa. “Wata magana nake ji haka Safraz?...” “Wata magana kuma?” Safraz ya mayar masa da tambayar. “Magana nake a kan ƙwatar takobi daga hannun Uwais!” “Shin laifi ne dan na karɓi abin da yake nawa?” Safraz ya tambaya cikin halin ko in kula. “Abin da nake so ka fahimta a nan shi ne, yanzu kai ne sarkin Afsah, wannan takobin ba zai kareka da komai ba, tun da ko a da rashinsa bai sa ka kasa zama sarki ba” Safraz ya girgiza kai. “Ba wai mallakar takobin ne kaɗai abin da ya tsaye min a rai ba. Kasancewar Uwais da Feroza a raye shi ne babban abin da yake damuna... Idan har Uwais ya ci gaba da kasancewa a raye ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin mulkina zai kasance cikin haɗari, wanda ni kuma ba zan lamunci hakan ba!” Anser ya sake matsawa kusa da ɗansa, sannan ya dafa kafaɗunsa. “Rabuwarka da Uwais shi ne abu mafi alkairi, idan har ka ce za ka ci gaba da bibiyar rayuwarsa to fa ni da kai duka ba za mu ji daɗi ba. Dan haka a shawarce ka ƙyale shi zai fi!” Safraz ya ture hannayen mahafinsa dake kan kafaɗunsa, sannan ya tashi sama ya fara yawo a iska yana faɗin. “Ba zan ƙyale shi ba, dole cikin biyu a yi ɗaya, ko dai shi ya mutu, ko Feroza ta mutu!...” Yana gama faɗin hakan ya ratsa rufin falon ya fice ta wurin. MALIK CANGAZ. Kallon kallo aka shiga yi tsakaninsa da Boka Jalis dake sanar masa da wurin da matasan da yake naima suke. Can kuma sai ya kwashe da dariya yana cilla kansa baya. “Tabbas zan taƙaita musu kwanakin tafiyar dake gabansu!” Ya faɗa bayan ya gama ƙyaƙyata dariyar tasa. Cikin rashin fahimta boka Jalis yace. “Ban fahimceka ba shugabana!” “Tun a daren yau zan shirya dakaru, sannan na turasu suje su tarbesu kafin su samu isowa nan!” Malik Cangaz ya bawa Boka Jalis amsa. Shi dai boka bai cce ƙala ba, dan shi ya hango abin da ya hango. Har suka gama tattaunawa da bokan bai sanar da shi wani abu bayan nasara ba. Da wannan farin cikin ya koma fada, duk da akwai manyan baƙi dake zuwa domin halartar bikin gimbiya bai sa ya fasa sawa a shirya dakaru domin turasu ƙwatar mukullin dake hannun baƙin matasa uku ba. Sai da ya gama da wannan fannin, sannan ya dawo cikin fada ya fuskanci lamarin baƙinsa, a gefe guda kuma shirye-shiryen bikin gimbiya na ci gaba da wanzuwa a fadar, domin duk mutanen gari sun san cewa za'ayi biki a gidan sarki. EID. Hannu ya miƙa ya karɓi sabbin tufafin da ya siya a wurin wani mutum dake cikin kasuwar ƙauyen Aban, domin ƙauye aban shi ne ƙauyen da ya zaɓa domin gudanar da ɗaurin aurensa da gimbiya Iqrah. Auren da zai yi amfani da shi wurin tarwatsa zuciyar Iqrah, auren da zai yi amfani da shi wurin rama kwatankwacin abin da Malik Cangaz ya aikata masa. Sai dai kuma ta wata hanyar wannan auren ya taɓa rayuwarsa, tun farko shi ba son gaskiya yake yi wa Iqrah ba, hasali ma komai yake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35