Chapter 7
Chapter 7
abu ɗaya yake gani. “Kana iya ganin wannan hasken?” Dr Ƙuraishi ya tambaya. “Ba na ganin komai Dr babu komai sai duhu” Dr Ƙuraishi ya kashe fitilar da ya haska idon nasa, sannan ya ɗauki glasses ɗinsa dake aje a gefe, ya mayar masa shi idonsa yana faɗin. “Za ka iya sauƙowa” Arman ya gyara zaman glashin, sannan ya sauƙe ƙafafunsa ƙasa, ya ɗauki canvas ɗinsa dake aje a ƙasa, ya saka a ƙafarsa, sannan ya dawo cikin main office ɗin Dr Ƙuraishi, inda Gulazar ke zaune tana jiransu. “Babu wani ci gaba!” Dr Ƙuraishi ya faɗa yana miƙawa Gulzar takardun lafiyar idon Arman ɗin. Gulzar ta karɓa, sannan ta kalli ɗan uwanta da shi ma yake kallonta. “Za mu iya tafiya?” Ya tambaya yana murmushi, shi sam bai ga wani abin shiga damuwa ba, dan ya san sam babu ci gaba a lafiyar idon nasa, ba dan Gulzar ɗin ta takura masa ba ma da ba zai zo ba, dan tun daren jiya ta yi booking appointment. Gulzar da gaba ɗaya take a dame ta miƙe, sannan ta ɗauki bag ɗinta ta rataya a kafaɗarta, ta bi bayansa suka bar office ɗin. Suna tafiya a hanya ya dafa kafaɗarta yana bata haƙuri, kamar ita ce marar lafiyar ba shi ba. Har suka shiga mota suka nufi hanyar gida Gulzar ba ta sauƙo ba. Sai da suka kusa kaiwa unguwarsu kiran PAn Abby ya shigo wayar Gulzar. “Alo Falak ya kike?” Ta faɗa bayan ta ɗaga kiran, daga ɗayan ɓangaren Falak ta amsa, sannan ta faɗi dalilin kiran nata. “Agha (Honorable person) Iƙlab ne yake son ganinki yanzu a kamfani” Ta tattare girarta tana ɗagawa Arman hannu alamun ya dakata, ya dakatar da motar yana kallonta. “Lafiya yake naimana?” “Eh yace yana son ganinki ne” “Ɗayib jaye! (Okay gani nan zuwa)” Ta sauƙe wayar tana kallon Arman. “Abby yana son ganina a kamfani, dan Allah ka kaini can” Ba tare da yace komai ba ya jinjina kansa yana gyara zaman glashin dake idonsa, sannan ya ja mota ya juya akalar tuƙin nasa zuwa Alhadi Group of Companies. Duk kuwa da ya jima rabon da ya je kamfanin, amma tun da ta buƙata ba zai ƙi kaita ba. *Majmu'at Shirkat Alhadi, Al Saaha street, Lobby C, Downtown Burj Khalifa, Abu Dhabi, Dubai.* “Jininka ya hau da yawa Sayid Iƙbal (Mr Iƙbal). Ya kamata ka riƙa sauƙaƙawa kanka” Faɗin likitan Sayid Iƙbal, yayin da yake tattare blood pressure monitor ɗin da ta yi amfani da shi wurin duba hawan jinin nasa, saboda haka kawai ɗazu ya yanke jiki ya faɗi ba gaira ba dalili. Zaune yake a kan wata boudoir chair, yayin da suit ɗin da ya cire daga jikinsa ke rataye a jikin chair ɗin. Ya lumshe idonsa yana shafa damtsen hannunsa da aka cire abin blood pressure monitor ɗin a jiki. PAnsa na tsaye a gefe, haka ma babban abokinsa Sayid Nusayr (Mr Nusayr), duka sauna cikin karafaren office ɗinsa dake ma'aikatar ne. “Ni zan wuce” Cewar Dr, yayin da ya gama haɗa kayan gwajinsa, sai a lokacin Sayid Iƙbal ya buɗe idonsa, sannan da ido ya yi wa Falak alama da ta raka Dr, ta jinjina kanta tana nunawa Dr hanya. “Mu je na rakaka Dr” Daga haka suka fice daga office ɗin. Suna fita Sayid Nusayr ya zauna kusa da Abby yana masa sannu. “Bai kamata ka riƙa saka damuwa a ranka ba Iƙbal” Abby ya kalle shi yana sakin hannun dress shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin da ya cire, dan bayan suit ɗin akwai waist coat a ƙasa. Zamansa ya gyara yana shafa sumar kansa da ta fara sirkawa da fari, alamun tsufa ya fara masa sallama. “Dole na shiga damuwa Nusayr! Sam Arman ya kasa fahimtar abin da nake son nusar da shi, ba na so na faɗi na mutu na bar shugabancin kasuwancin da na sha wahala kafin na kafa shi a hannun da ba na gari ba. Da ace Akhi Anwar da kansa ne yake son shugabantar kamfanin na bayan raina ba zan ji komai ba, amma Faisal yake so ya danƙawa shugabancin nan, ya nuna shi ba shi da sha'awar ci gaba da kasuwanci. Arman ba ya son karɓan abin da yake nasa, Gulzar mace ce, kuma har yanzu tana da ƙarancin shekaru, sam ba za ta iya shugabantar babban kafani kamar wannan ba... Na rasa abin da zan yi!” Nusayr ya girgiza kai cike da tausayin abokinsa. “Ka yi haƙuri Iƙbal, ka ci gaba da addu'a, da yardar Allah ba za ka mutu ba har sai ka ga Armaan a kan waccan kujerar!...” Ya ɗan yi fasali yana nuna hamshaƙiyar kujerar dake office ɗin, sannan ya ci gaba da faɗin. “A matsayin shugaban kamfanunuwan Alhadi..” Abby ya yi murmushi me sauti. “Wannan shi ne mafarkin da na daɗe ina yi, kuma da dukkan fatan duniya nake roƙon Allah ya sa ya zama gaskiya kafin na bar duniya” Kafin Nusayr ya kai ga faɗin wani abu Gul ta buɗe ƙofar office ɗin ta shigo a dugunzume. Tana ganin Abby zaune ta fara hawaye, ta nufe shi da gudu ta faɗa kansa ta rungume shi tana kuka. “Abby!?” Abby ya shafa dogon gashin kanta dake cikin style ɗin long wavy. Yana murmushi, a da Arman ne yake masa haka, saboda a baya Arman ya fi kusanci da shi fiye da kowa. Amma a yanzu Arman ya fi gudunsa fiye da kowa, kuma ba komai ya ja hakan ba face maganar gadon kamfani da yake yawan yi masa. “Abby me ya sameka?” Abby ya sake yin murmushi yana shafa gashin kanta. “Lafiyata ƙalau, kawai na ɗan ji jiri ne, sai na yi kamar zan faɗi, amma babu abin da yake damuna” Ta kwanta a jikinsa tana kallon Sayyid Nusayar dake murmushi. “Ammu Nusayr wai haka ne?” Sayid Nusayr ya jinjina mata kai. “Abby ka dinga kula dan Allah.” Ta ƙarashe tana kallon Abby, Abby ya share ƙwallar da ta zubo mata yana gyaɗa kai, sannan ya sumbaci kanta yana kwantar da kanta a kafaɗarsa. “Ina ɗan uwanki? Imminku ta faɗa min cewa tare kuka fita da shi” Nan da nan ta ɓata fuska. “Yana reception, wai zai jirani a can” Abby ya girgiza kansa, dan ya sam dalili, wato shi ba ma zai shigo ba, ballantana ya ga office ɗin da bathroom ɗinsa ma ya fi shi muhimmanci a wurinsa. “Ki yi haƙuri, Akuki (Ɗan uwanki) zai daina duk wannan abin da yake” Ran Gulzar a ɓace tace. “Ai sai dai idan zamanin baya yaje ya dawo, sannan ne zai sauya ra'ayinsa, taurin kai ne da shi kamar mutumin wancan zamanin!” Abby ya dungure mata kai. “Kin taɓa ganin wanda yaje zamanin baya ya dawo?...” Ta turo baki tana tura gashinta baya, sannan ta kwanta a jikinsa tana zuba masa shagwaɓarsu ta autanni. * “Asirul laimun wu bass (Juice ɗin orange ma ya isa)” Ya bawa ma'aikacin kamfanin da ya tambaye shi abin da yake son sha amsa. Ma'aikacin ya amsa da to, sannan ya bar wurin, Arman ya ɗaga idonsa yana kallon katafaren reception ɗin kamfanin dake ƙasan ma'aikatar. Gaba ɗaya jinsa yake kamar zaune a kan ƙaya, dan ko kaɗan ba ya son abin da zai haɗa hanyarsa da ta kamfanin nan,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35