Chapter 8
Chapter 8
kamar yanda Faisal ya saba yi wa rayuwarsa karan tsaye, haka ma yau ya masa. “Makaho!?” Idonsa ya rintse yana gyara zaman glasses ɗinsa, kafin ya buɗe idon nasa ya ɗaga kai ya kalle shi, sai dai yau ba shi kaɗai ba ne, akwai Sakina tare da Anwar mahaifinsu. Kansa ya kawar daga barin kallonsu, dan haka kawai ya ji zuciyarsa na hassala da dariyar da suke masa. “Kaya ka kawo kamfanin ne?. Dan na san ko cikin ma'aikatan dake wurin nan babu makaho irinka” Cewar Sayyid Anwar yana dariya. Arman ya dunƙule hannunsa yana haɗiyar yawu da ƙyar, dan yau ji yake kamar ba zai iya ɗaukan cin zarafin da suke masa ba. “Ai ko a cikin masu shara babu makaho Abbu, ballantana a cikin masu kawowa kaya” Sakina ta faɗa tana tata dariyar. Arman bai tanka musu ba, kansa kawai ya sake sunkuyarwa, saboda yanda mutanen dake kusa da su suka fara kallonsa. “Allah sarki makaho! Su fa da ma makafi ba su da wani aiki da ya wuce bara a gefen hanya... A taimaka min da sadaka! A taimaka” Faɗin Faisal yana kwatanta yanda mabarata ke bara. Arman ya miƙe da sauri zai mayar musu da martani muryar Abby ta kaste shi. “Arman!” Ya tsaya cak da shirin dukan da yake son kaiwa Faisal yana huci, ya dunƙule hannunsa da mugun ƙarfi yana jin kamar ya daki bango ko zai huce. Abby da Gulzar da suka sauƙo ƙasa tare suka tsaya a wurin suna kallonsu. “Me yake faruwa?” Abby ya tambaya yana dafa kafaɗar Arman. Amma sai Arman ɗin ya kauce, ya kalli Gulzar. “Idan kin gama ina mota” Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar Building ɗin kamfanin. Har ma'aikacin da ya tafi kawo masa ruwan laimo na binsa da shi yana faɗin ga ruwan laimon nan ya kawo masa, amma bai tsaya ba ballantana ya karɓa. Tun da Gulzar ta ga haka ta san cewa wata baƙar maganar Faisak (FAISAL AND SAKINA) suka faɗawa ɗan uwanta da har ta sa ya shiga wannan halin. “Me kuka gayawa ɗan uwana?” Ta tambaya tana raba idonta a kan su ukun. Amma babu wanda ya amsa mata, sai murmushin da suke suna duban juna. “Wai ko kunya ba ku ji?... Sakarkaru kawai!” Ta faɗa rai a ɓace, sannan ita ma ta juya ta bi inda ɗan uwanta ya bi ba tare da ta yi wa Abby sallama ba. Daga Anwar har FAISAK ba su ji haushin abin da Gulzar ta yi ba, dan sun san su ne a gaba. “Na ji an ce ka faɗi da fatan ba wata matsalar ba ce?” Sayyid Anwar ya tambaya yana duban Abby da murmushi, Abby dake cikin jin rashin daɗin halin da yaransa ke ciki ya girgiza kansa. “Na ji sauƙi” “To sai a kula nan gaba, dan wata ƙila idan an faɗi ba lalle a tashi ba!” Faɗin Sayyid Anwar yana murmushi, tare da taɓa kafaɗar Abby, sannan ya ja yaransa suka bar Abby cike da zullumi. *FACT MAGAZINE, Building 8, Dubai Media City, Abu Dhabi, United Arab Emirates.* ADAM POV. Sanye yake cikin baƙin dress trouser, da farar sweat shirt, kafaɗarsa rataye da briefcase ɗinsa, ƙafafunsa cikin moccasin dockside. Sumar kansa me ƙarfi irin ta Africans na cikin askin crew cut. A ɗarare ya ƙarasa seat ɗinsa dake cikin na tarin ma'aikatan kamfaninsu ya zauna yana raba ido. A hankali ya aje briefcase ɗinsa a kan table, sannan ya buɗe system ɗinsa dake kan table ɗin, ya ciki gaba da aikin da bai ƙarasa ba. Adam baƙi ne a kalar fata, kuma dogo ne, sannan yana da kyau dai-dai gwargwado, dan a fuskarsa ba ka ce ga abin kushe ba. Yana tsaka da aikin da yake wani cikin abokansa na wurin ya lallaɓo ta bayansa, ya shammace shi yace. “Booom!” Da ƙarfi, hakan yasa Adam ya zabura har yana ɗaukewa ƙafafunsa daga ƙasa, zuciyarsa kuwa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar tsoro. Sai jujjuya ido yake yana haki, abokin nasa da ya tsorata shi ya kwashe da dariya yana tafa hannu. Haka sauran abokan aikinsa da teburan aikinsu ke kusa da nasa suka taya shi dariyar. “Matsoraci!... Ka gama aikin da shugaba ya baka?” Abokin nasa ya tambaya yana duba system ɗinsa, Adam ya masa banza yana sauƙe ƙafafunsa da ya ɗora a kan kujera zuwa ƙasa, tare da dafe ƙirjinsa dake barazanar ɓallewa. “Haisam bana son irin wannan, kuma ka sani” Ya faɗa cikin son nuna ɓacin ransa a kan abin da Haisam ɗin ya masa, Haisam na dariya ya dafa kafaɗarsa yana faɗin. “Ka yi haƙuri abokina, a duk sanda na ganka cikin tsoro nishaɗi kake bani” Adam ya galla masa harara yana ɗauke kai. Har Haisam ya ƙaraci surutansa bai ce da shi uffan ba. Har ya ƙyale shi dan dole, ya ci gaba da aikin dake gabansa, kafin landline phone ɗin dake kan teburinsa ta shiga ruri. Shi ma ringing ɗin wayar sai da ya kusa tsorata shi, da ƙyar ya saita kansa ya ɗaga wayar. “Sabahul Khair Ustaz (Barka da safiya shugaba)” Ya faɗa bayan ya ɗaga wayar, dan kira ne daga wayar ogansu. “Barka da safiya, da fatan ka gama aikin da na baka?” Ya jinjina kai yana faɗin. “Eh Ustaz na kammala shi” “Ina son ganinka yanzu a office ɗina” “Hadir Ustaz (To Shugaba)” Daga haka ya aje wayar, ya ɗauki system ɗinsa ya miƙe ya nufi office ɗin ogan dake can wata kusurwa ta ma'aikatar. Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar gilashin dake ofishin, dan ko daga nan inda yake yana iya ganin ogan nasu zaune a kan kujerarsa yana cin shawarama, sai da Ustaz ya ba shi izinin sannan ya shiga da sallama. Shugaban ya amsa sallamar da ya yi yayin da yake zama a kan kujerar ofishin nasa. A ladabce ya buɗe system ɗinsa, sannan ya miƙawa Ustaz. Ustaz ya karɓa, ya shiga duba ayyukan yana jinjina kai, alamun sun burge shi. “Hotuna sun yi kyau Adam. Kuma na ji daɗin ganinsu a haka... Lalle na jinjinawa ƙoƙarinka” Adam ya yi murmushi me sauti yana faɗin. “Haza wajibi Ustaz (My pleasure shugaba)” Ustaz ya jinjina kai shi ma yana murmushi, sannan ya aje guntun shawarman da bai ƙarasa cinyewa ba, ya kalli Adam, kana ya furta masa dalilin ƙaddarar da za ta zama silar juyin rayuwarsa. “Nan da wattani biyu masu zuwa gwamnatin Dubai na shirin bamu kyautar karramawa, a wannan bikin da za'ayi ina so mu gabatar da hotuna masu kyau da jan hakali. Hotuna irin wanda ba'a saba ganinsu ba, kuma ina so ya zama kai ne wanda zai zo da hotunan... Da fatan za ka zo min da abin da zan yaba” *Dubai Miracle Garden, Street 3, Al Barsha South, Dubai.* IVANA POV. “Na gode” Ta yi wa mutumin da ta sai juice a wurinsa godiya, sannan ta juya da nufin barin wurin, domin zuwa wurin ɗan 'yar uwarta Imran da suka zo Miracle Garden ɗin tare, dan shi ne ma ta zo wurin. Hannayenta duka biyu na riƙe da cups ɗin juice ta nufi wurin da wani jirgin wasa yake, wanda aka haɗa shi da ganyayyaki, a jikinsa kuma akwai rubutun 'Emirates'. Kasancewar a kusa da wurin ta bar Imran na wasa da wasu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35