Skip to content

Chapter 5

Chapter 5

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

karɓar shugabancin kamfanin to Faisal shi ne wanda zai karɓi kujerar. Ƙoƙarin karkato da hankalin Arman shi ne abin da yake ta son yi tun kafin lokaci ya ƙure musu, amma shi Arman ya kasa ganewa. A ko da yaushe yana ɗaukan kansa a ba jowa ba, ya bar zuciyarsa ta mutu, saboda an ce masa dan yana da matsalar gani ba zai iya zama jagoran kamfanin Alhadi ba. Kuma saboda yanda ake aibata lalurar tasa yasa ya tsani duk wata harka ta kamfanin. “Armaan ina zaka je ba ka gaishe da Abby ba?” Immi ta dakatar da shi, hakan ya sa ya juyo, ya kalli Abby da shi ma ke kallonsa. “Masa'ul khair Abby” Ya faɗa daga nan inda yake, dan a yanzu ko kusantar Abby ba ya so, daga ya kusance shi zai ji kamar yana kusantar kamfanin Alhadi ne. Abby ya sauƙe numfashi yana kallon ɗansa, sannan a hankali ya jinjina kansa yana amsawa, Arman na jin ya amsa ya juya ya nufi sama. Dan sam ba ya ma son zamansa da Abby ya yi tsayi, dan daga sun ɗan jima a wuri zai fara masa maganar da ta mutuwarsa ta fita daɗin sauraro a kunnensa. Yana shiga corridorn ɗakunansu ya hangi Gulzar na nufowa downstairs da alama wani abin za ta yi a ƙasa. Farar matashiyar da za ka iya kira da balarabiya sanye take da baƙin wide black jeans, da farar blouse top, ƙafafunta cikin fluffy sliders farare, dogon gashin kanta kuwa sai reto yake a bayanta. Ita sam ba ta kama da indiyawa, saɓanin Armaan da kammaninsa suka sirka da na Immi, ita Gulzar sak Abby ce, wayarta ce riƙe a hannunta tana latsawa, da alama ma ba ta lura da shi ba. Arman ya yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya fara taku a hankali yana nufarta, sai da ya je dab da ita sannan yace. “Me dogon gashi!” Ya faɗa da ƙarfin da ya razana Gulzar, har wayarta na suɓucewa a hannunta, ta kalli wayarta da ta faɗi ƙasa sannan ta dube shi tana haɗe girar sama da ta ƙasa, ta kai masa duka a ciki tana faɗin. “Duk ka bi ka tsorata ni!” Arman ya dafe wurin da ta daka a cikinsa yana dariya, sannan ya sunkuya ya ɗauko mata wayarta, ya miƙa mata, ta warce wayar tana harararsa. “Idan ka sake min irin wannan sai na faɗawa Immi ta min maganinka” Ta faɗa tana nuna masa ɗan yatsa, Armaan na dariya ya dafata tare da juyata suka nufi ɗakinsa. “Ina am imzah! Bas, mu aksar (Wasa fa kawai nake miki ba komai ba)” Gul ta mintsini cikinsa tana faɗin. “Kada ka sake min irin wannan wasan” Armaan ya saketa yana dafe inda ta mintsi ne shi. “Yarinyar nan kin iya mugunta” Gul ta matsa daga jikinsa, dan ta san halinsa, yanzu zai ce zai riƙe mata gashinta da ta fi so, dan ko sau ɗaya ba ta jin ta taɓa rage tsayinsa. “La wain rayiha? (Ina kuma za ki je?)” Ya tambaya yana kallonta, ta ruga da gudu, shi ma ya bi bayanta zuwa ɗakinsa. Gul na shiga ɗakinsa ta faɗa kan gadonsa tana dariya. Shi kuma yana shigowa ɗakin ya yi tsaye yana kallonta a kan gadonsa. Kansa kawai ya girgiza, ya nufi wurin da ya saba aje awards ɗin da yake samu a wasan fencing da yake yi. Ɗakin nasa na da girma, komai na ɗakin brown da fari ne, gadonsa na daga bangon yamma na ɗakin, yayin da balconyn dake cikin ɗakin yake ta bangon gabas, ta yanda daga hasken rana ya fito zai sauƙa kan gadon, dan slide glass door ce a wurin. Akwai dressing mirror da 'yan wasu tarkacensa a ɗakin, yayin da closet ɗinsa ke cikin banɗaki. Babu tarkace da yawa a ɗakin, amma komai ka ga a ɗakin sunan kuɗinsa yake furtawa, dan kallo ɗaya za ka masa ka fara ƙissima tsadarsa. Daga kusa da chest drawern da ya saba jera awards ɗinsa kuwa, hotunansa, da wanda suka ɗauka shi da su Gulzar da Immi, da nasa shi da su Ivana ne manne a ko ina. “Ni fa kallon mara aikin yi nake maka aki! Ni ban ga dalilin da zai sa ina koyon wasan takobi ba. Bayan ni ba a 18th century nake rayuwa ba. Yanzu kai ya waye, babu wanda yake faɗa da takobi, da ma koyon harbi kake da sai na ce dama-dama!” Ya juya ya kalli Gulzar dake zaune a tsakiyar gadonsa tana danna wayarta. Lokaci guda kuma wannan yaƙin da ya saba yin mafarkinsa ya kutso cikin tunaninsa. Shi kansa ba ya ce ga dalilin da yabsa yake son koyon wasan takobi ba, amma haka kawai iya sarrafa takobi ke burge shi. “Ba ni na zaɓi fencing ba Gul! Fencing ne ya zaɓeni” Ya bata amsar yana cilla mata backpack ɗinsa, ta cafe jakar tana kallonsa sanda ya shiga bathroom. Wayarta ta aje a gefe, sanna ta buɗe jakar, ta soma fitar da wasiƙun dake ciki, wanda yawancinsu 'yan matan dake sonsa ne ke turowa. “Aki waɗannan fa? Ko tsofi ne?” Ta tambaya da ɗan ƙarfi, dan ta ji ya kunna ruwa, alamun wanka zai yi. “Satin da ya wuce aka aiko da su!” Shi ma ya bata amsa daga cikin bayin, Gulzar ta buɗe ɗaya daga ciki, sannan ta fara karantawa a bayya ne. “Zuwa ga kyakkyawan tauraron wasan fencing da babu kamarsa a MK fencing acadamy. Haƙiƙa ka iya sarrafa takobi cikin ƙwarewa, kana bawa takobi umarni cikin iko da burgewa, ka haɗu sosai Arman!...” Gulzar ta zaro ido tana rufe bakinta. “Aki ai wanna 'yar makarantarku ce” Tana jiyowa dariyarsa a cikin bayin, kafin taji ya bata amsa da. “Ba ɗaliba ba ce, malama ce!” Ita ma Gulzar ɗin kwashewa ta yi da dariya, sannan ta aje wadda ke hannunta ta ɗauko wata ta shiga karantawa, har Armaan ya fito daga bathroom ɗin sanye cikin blue polo shirt da baƙin cargo trouser. Ya tsaya a jikin dressing mirror yana busar da sumarsa da ya jiƙa yayin wankan da ya yi. “Ke dan Allah ki aje wannan wasiƙun da ba ƙarewa suke ba” Gulzar ta kalle shi ta cikin madubin da yake tsaye a gabansa, sannan ta aje wasiƙun agefe, ta saka hannunta a cikin jakar, ta fito da tikitin Coca-cola Arena da suka siya ɗazu. Ta karanta tikitin, sannan ta kalli Arman tana faɗin. “Wai yau Chris Brown ya yi live performance kuma ka je amma ba ka faɗa min ba?” Ta tambaya tana sauƙa daga kan gadonsa, Arman ya aje dryer dake hannunsa, sannan ya juyo ya kalleta. “To ai abin ne ya zo a ƙurace!” Gulzar ta iyo kansa da gudu tana faɗin. “Ai ka iya ɗaukan abokanka zuwa wurin! Ni kuma ka barni a nan” Shi ma gudun ya saka ya fice daga ɗakin, tana biye da shi har zuwa saman gidan, dake ɗauke da sitting areas, daku ma runfunan shaƙatawa. Masu aikin gidan kuma ma aikin tsaftace wurin, Arman ya zauna a kan kujera yana kallonta. “Ki yi hakuri mana me gashi” Gulzar da take a fusace, ta sa hannu ta mayar da gashinta da ya suƙo mata kan fuska zuwa baya tana huci, sannan ta zauna kusa da

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35