Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,199 words 0 views Progress saved
Download Book

ko irin ya saba da cin abincin nan. Kuma dan tsabar yana son tuwon yasa a wasu lokutan yake tattaki ya zo gidansu Adam, dan kawai Maama ta ba shi tuwo, yace a cikin abincin hausawa tuwo ya fi komai daɗi. “Ya zalame (Man) na rasa wurin da ya kamata ace na je na ɗauki hotunan da za su ja hankalin mutane, irin hotunan da ba'a saba gani ba ka gane?” Armaan ya gyara zaman glasses ɗinsa, sannan yace. “Ka je ka ɗauko hotunan Creek harbor, ko Dubai Fountain show, ko Museum of the future...” “Ina maganar abin da ba'a saba gani ba kana lissafo min wuraren da babu wanda bai sansu ba a Dubai. Duka waɗannan wuraren da ka lissafo ɗaiɗaikun mutanen garin nan ne kaɗai ba su taɓa zuwa ba, in ma ba su je ba sun san wurin. Kuma me zan nunawa mutane a wurin da suka riga suka sani?” Adam ya katse shi. Arman ya gyara zama yana aje bowl ɗin hannunsa a kan center table. “To ka je Bastakia, Deira, ko ka ɗauko gaba ɗaya Palm Jumeirah...” “Dakata Arman, hotunan wuraren nan tuntuni an riga an ɗauke su, imfact ba na son ɗaukan hoton wani abu a Dubai, na fi son na fita wajen Dubai dan na zo musu da sabon abu.” “Ina za ka je to?” Ya tambaya yana gyara zaman glasses ɗinsa. Adam ya yi shiru kawai, dan har yanzu ya kasa tsayar da shawarar inda ya kamata ace yaje. “Me zai hana ka je Nigeria, ka ɗauki hotunan masarautun gargajiya da al'adun Hausawa?” Maama dake tsaye a kitchen, tana sauraron duka hirarrakinsu ta bada shawarar. Kusan a tare suka juya suka kalleta. “Kyakkyawar shawara... Idan za ka je zan rakaka, dan ban taɓa zuwa ƙasarku ba, ko ba komai ka ga ni ma zan buɗe ido” Adam ya yi murmushi. “Zan duba na gani” Arman ya kai masa dukan da a ɗan ƙanƙanin lokaci ya sa ya razana. Dan sam bai zaci dukan Arman ɗin a wannan lokacin ba. “Miye ne?” Ya tambaya yana zaro ido. “Me za ka duba ka ga?. Ai tun da Maama ta riga ta bada shawarar nan ta karɓu, ko kai ba ka karɓa ba ni na karɓa maka, dan haka ni zan ɗauki nauyin tafiyarmu Nigeria. Dan a private jet ɗin Alhadi za mu tafi” Adam ya yi dariya. “To ya kamata mu sanar da Ivana, dan ita ma ba za ta kasa zuwa ba” “Zan faɗa mata” Arman ya faɗa yana ɗaukan wayarsa dake ruri, alamun shigowar kira, ganin lambar kakarsa ‘Jadda Nahila’ (Kaka Nahila) yasa ya ɗaga kansa yana girgizawa. Dan tun da har ya ga kiranta ya san wani abin aka ce mata ya aikata. “Shu sar (Me ya faru?)” Adam dake rufe system ɗinsa ya tambaya. “Jadda ce ke kirana” Ya faɗa yana nuna masa wayar. “To ka ɗaga mana” Sai ya girgiza kansa yana miƙewa. “Babu amfanin sai na ɗaga, na san cewa za ta yi duk inda nake, duk abin da nake na bari na tafi gidanta” Adam ya yi dariya yana kallon Arman ɗin da ya nufi kitchen, ya wanke hannunsa, sannan ya dawo falon ya ɗauki Denim jacket ɗinsa ya saka. Sannan ya ɗauki keyn motar da ya fito da ita. “Na tafi... Maama na tafi” Ya musu sallama yana nufar ƙofar fita daga gidan, wadda ta kasance ita ce ƙofar falo. “To Arman ka gaida Imminka” “Za ta ji” Daga haka suka fita tare da Adam. Motarsa silver color ƙirar RR (Rolls-Royce) sweptail. Na fake a ƙofar gidan. Kallon motar kawai idan ka yi za ta baka labarin kuɗinta. Dan sam motar ba ta yi kama da ta ƙananun masu kuɗi ba. Shi kansa Arman ba ya hawa mota ɗaya, idan yau ya hau Bugatti La Voiture Noire, gobe za ka ganshi da Lamborghini Venone Roadster. “Idan na dawo daga gidanta zan kiraka a kan maganar tafiya Nigeria ɗin nan” Arman ya faɗa yana buɗe ƙofar motarsa. Adam ya amsa masa da to, suka yi sallama, sannan Arman ya ja motar zuwa gidan kakarsa, wadda ta haifi mahaifinsa, dan duka 'yan uwan mahaifiyarsa suna can Lahore, Pakistan. Salma Ahmad Isah ✍️ _______________ _Shin a ganinku me Arman zai yi ifan jar ya san abin da iyayensa ke shiryawa?._ _Wata alaƙa kuke hasasowa tsakanin Uwais da Ivana?._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-5 A ƙofar gidan ya faka motarsa, sannan ya fito yana kallon kyakkyawan gidan da tsohuwar ke ciki, dan kakansu ya daɗe da rasuwa, ita Jaddan ce kaɗai ta rage, sai jikokinta da kan zo tayata zama jifa-jifa. Dan bayan mahaifinsa da Anwar Jadda na da 'ya'ya mata huɗu, waɗan da suka kasance ƙannen mahaifinsa. Ba tare da knocking ko danna door bell ba ya buɗe ƙofar gidan ya shiga, a ɗan hall ɗin dake bakin ƙofa ya tsaya ya cire takalmansa, ya saka wasu da ya ga a wurin, sannan ya shiga falo yana dube-dube. Bai ga kowa ba bayan wata kyakkyawar budurwa da ta fito daga ƙofar da ya san cewa kitchen ne. Hannunta riƙe da tray, wanda kallon kyanta bai sa ya san miye a ciki ba. Da alama ta ji buɗe ƙofar tasa ne shi yasa ta fito dan ganin wanda ya zo. “Marhaba” Ta faɗa tana kallonsa da murmushi, dan ita ta san shi, shi ne dai alamu suka nuna cewa bai santa ba. Kansa ya jinjina kawai yana ƙare mata kallo, ba zai yi ƙarya ba, yarinyar tana da kyau. “Aina Jadda” (Ina Jadda) “Bi gurfatah, kallini nadilah. (Tana ɗakinta, bari na kirata)” Ta amsa da muryarta me daɗin saurare. A living room ya zauna yana ci gaba da kallon matashiyar, har ta nufi corridor ɗin da zai sadata da upstairs. Sai a lokacin ya ɗauke idonsa a kanta, yana zaune a wurin har ta dawo, ta sanar masa ga Jaddan na sauƙowa, sannan ta koma kitchen ɗin. Tun da Jadda ta fito take wurga masa harara, har ta iso living room ɗin, ta zauna a gefe da shi tana kallonsa a kaikaice. Kuma duk da ya lura da hakan bai sa ya fasa dariya ba. “Masa'ul khair ya Jadda. (Barka da yamma Jadda)” Jadda ta masa banza ta ɗauke kai tana girgiza ƙafa. “Ƙira nawa na maka?” Ta tambaya bayan wani lokaci. “A ƙalla goma” Arman ya amsa. “To me yasa ba ka ɗaga ba?” “Saboda na san maganar da za ki faɗa, shi yasa na zo tun kafin ki ce na zo” Jadda ta kuma yin shiru. “Arman zo nan” Ya dubeta, sai ya miƙe ya koma gefenta ya zauna. “Magana nake so mu yi...” Ya jinjina mata kai, yana kallon yarinyar nan da ta dawo falon ɗauke da kayan taɓawa, ta aje a kan center table, sannan ta juya ta koma kitchen. “Jadda wace ce wannan?” Ya tambaya. Jadda ta harare shi, dan ta lura tun da ta shigo falon yake kallonta har ta koma inda ta fito. “Gufran sunanta, ita ce yarinyar gwaggonka Bilƙisa, wadda ke Qatar.” “Ohh na gane. To ina jinki” Ya amsa yana jinjina mata kai. “Da Anwar da Iƙbal duka 'ya'yana ne. Da kai da Faisal jikokina ne, haka Gulzar da Sakina. Amma Wallahi har

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35