Skip to content

Chapter 1

Chapter 1

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 _Daga ruwa zuwa ruwan zafi_ From the writer of: YADDA ƘADDARA TA SO LABARINSU HASKE ƘADDARA CE ArewaBooks @SalmaAhmadIsah Wattpad @SalmaAhmadIsah *Gabaki ɗaya labarin JUYIN KWAƊO, da littafin kansa. Na sadaukar shi zuwa ga ZAHRA ROYAL STAR and NAINARH KD NKD'S. Your love and acceptance mean everything to me. Thank you for being my safe space and my forever friends.* بسم الله الرحمن الر حيم *Page-01* *MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.* ARMAN IƘBAL. Babu abin da yake tashi a ko ina sai hayaniya da iface-iface, sai kuma sautin sara da sukan takkuba. Kuma ko ina jini ne ke zuba... A tsakiyar wannan hatsaniyar yaƙin yake tsaye, can ya hango wani mayaƙi ya taho da gudu ya iyo kansa, hannunsa riƙe da wani takobi me tsananin kaifi, ya kawo masa sara da ita... Tahowar sukan takobin cikin tunaninsa ya yi dai-dai da tahowar sukan takobin abokin karawarsa a tsakiyar filin hall ɗin koyon wasan takobi na MK fencing academy. Cikin zafin nama ya buɗe idonsa, sannan ya yi azamar kaucewa sukar takobin wasan. Cike da ƙwarewa kuma ya yi amfani da nasa takobin ya kaiwa abokin nasa farmaki, farmakin da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan yasa ya zamo zakaran wasan, domin shi ne ya lashe!. Malamai da ɗaliban wasan na takobi suka shiga tafa masa, hakan yasa ya juya kansa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a hankali yake fitar da numfashi, domin wannan mafarkin da ya saba yi ido biyu yau ma ya raɓe shi, ya rasa mece ce alaƙarsa da wannan yaƙin da yake yawan yin mafarkinsa ido biyu ko cikin bacci. Ba ya jin ya taɓa tsallake sati ɗaya ba tare da ya yi mafarkin wannan yaƙin me firgitar da ɗan adam ba. Shi dai ya san ba a haifeshi a ƙarnin da aka yi yaƙin ba, amma kuma ya rasa dalilin da yasa a ko da yaushe yaƙin yake raɓar rayuwarsa. Hannu ya kai ya taɓa farin glasses ɗin da ba ya taɓa rabuwa da su duk rintsi, kasancewar yana fama da lalurar rashin gani, wadda aka haife shi da ita. Da ace kuɗi yana samar da lafiya ya tabbatar da mahaifinsa Sayid Iƙbal Alhadi zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka domin sama masa lafiyar ido. Amma tun yana ƙarami ake fafutukar naima masa maganin da zai warkar da idon har zuwa yanzu da yake da shekaru talatin da ɗaya a duniya ba'a dace ba. Hakan tasa aka haƙura aka ƙyale maganin, ya ci gaba da amfani da glasses ɗin da da taimakonsu kaɗai yake iya ganin abin da Allah ya yassare masa ya gani. “Muna tayaka murnar lashe wannan gasa Arman! Fatan nasara!” Faɗin ɗaya daga cikin malaman dake koyar da su wasan takobi cikin harshen larabci. Yayin da yake miƙa masa award ɗin da aka tanada domin zakaran da ya lashe wannan gasa da aka saka a tsakanin ɗaliban makarantar. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi award, sannan ya yi murmushi me kyau, tare da furta. “Na gode” Ya juya ya kalli abokansa da yake koyar wasan tare da su, ya ɗaga musu award ɗin, suka saka tafi har da masu ihu, shi dai murmushi kawai yake, har ya sauƙa daga kan stage ɗin wasan. Ya nufi ɗakin sauya kaya dake cikin hall ɗin, a nan ɗakin da ya shiga ya sauya kayan fencing ɗin da suke jikinsa, ya mayar da kayan da ya zo da su. Wato black plain hoodie, wadda ya ɗorawa red bomber jacket a sama, da blue jeans sai baƙaƙen canvas ɗinsa. Sannan ya nufi backpack ɗinsa ya buɗeta ya saka award ɗin da aka ba shi, kafin ya ɗauki wayarsa dake ciki, ya buɗe da fatan ganin missed call ɗin abokinsa ADAM, amma babu alamar ma ya kira, dan haka ya ja tsaki, ya buɗe wayar ya nemo lambarsa ya sake aika masa kira, a karo na barkatai a ranar, dan tun kafin ya shiga fencing class ɗin yake ta kiran wayarsa. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM ALI ABBAS. “Adam! Adam! Adamm! Wai ba za ka buɗe ƙofar nan ba!?” Wata bahaushiyar mata ke faɗi, cikin harshen hausa, yayin da take tsaye a jikin ƙofar ɗakin da take a kulle, yanayin shigar dake jikinta kaɗai zai sanar maka da ƙabila da kuma ƙasar da take. Duk da su mazauna ƙasar ta Dubai ne bai sa ta daina saka kayan al'adarta ba, a matsayinta na ainahin 'yar ƙasar Nigeria, kuma bahaushiyar arewacin ƙasar. Daga cikin ɗakin da take buga ƙofarsa kuwa, wani matashi ne tsugunne a ƙasan desk, ya lulluɓa da blanket har kansa, yanayin tsoro shi ne kwance a kan fuskarsa, ban da rawar ɗari ba abin da yake, kamar wanda ya kwana a cikin fridge. Ɗakin bai cika girma ba, amma yana ɗauke da kaya masu kyau da sauƙin kuɗi, kallo ɗaya za ka yi wa ɗakin ka san cewa na mai ɗaukan hoto ne. Dan ko wace kusurwa ta ɗakin na ɗauke da hotunan mabanbanta abubuwa, da kuma hotunan cameras da ma cameras ɗin na zahiri, tarkacen da ɗakin ya cika zai sa ka san cewa ɗakin matashi ne. Daga wajen ɗakin, matar nan ta ɗazu da take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta girgiza kanta cike da takaicin halin ɗan nata. “Allah ya raba bawa da wahala!” Ta faɗa kawai, sannan ta juya ta dawo ɗan ƙaramin falonsu dake ƙasan gidan, wanda ke ɗauke da kyawawan furnitures masu kyau. Tana shirin wucewa kitchen ɗin dake haɗe da falon wayar Adam ɗin dake a falon ta yi ringing kamar ɗazu. Dan yawan kiran wayar da ake run ɗazu ne yasa ta gane cewa Adam ɗin bai fita ba, shi ne ta je domin duba shi, amma sai ya ƙi buɗe ƙofar ɗakin. Wata shawara ce ta faɗo mata a rai, hakan yasa ta nufi wayar tasa ta ɗauka ‘Bin Iƙbal’ shi ne abin da aka rubuta a matsayin sunan wanda yake kiran, kuma ta gane cewa abokinsa Arman ne, dan haka ta ɗaga wayar, ta sanarwa Arman ɗin halin da Adam ɗin ke ciki. Daga ɗayan ɓangaren, Arman ya sauƙe wayarsa ƙirar iPhone 'yar yayi yana dariya a nutse, ba sai Maaman Adam ta yi dogon bayanin abin da yasa ya shiga ɗakinsa ya kulle kansa ba. Dan ya san dalilin ba zai wuce ya kalli wani horror ko Zombie movie ba, ya san abokinsa da tsoro kamar farar kura. Kuma ga shi da naci, dan duk yadda ya kai ga tsoron horror film ɗin sai ya kalla daga zarar sabo ya fito, Allah yasa yanzu haka bai kwanta zazzaɓi ba. Kansa ya sake girgizawa yana ɗaukan backpack ɗinsa, ya goyata a bayansa yana kama hanyar barin Business Bay, sai da ya fita daga building ɗin sannan ya fara dialing numbern ɗaya ƙawar tasu wato IVANA!. *Repton school Dubai, Nad Al Sheba 3, Abu Dabhi, United Arab Emirates.* IVANA SAGAR. Zaune take a kan maroon bowl chair, sanye take cikin farar hoodie da baƙin distressed jeans, ƙafafunta cikin farin canvas, baƙin dogon gashin kanta kwance a gadon bayanta, yayin da hannayenta ke kaɗa guitar ɗin dake kan cinyarta. Farar balarabiya ce, kyakkyawar gaske, me manyan idanuwa da dogon

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35