Chapter 30
Chapter 30
abin da suka yarda da shi a matsayin wayewa kauce hanya ne... “Ki yi haƙuri idan maganata ta sa kin ji ba daɗi!” Uwais ya sake faɗa yayin da suka ci gaba da tafiya, ta girgiza masa kai tana murmushi, alamun ba komai, sannan ta gyara zaman jakar guitar ɗinta dake goye a bayanta, dan yanzu Arman ne yake ɗauka mata kaya. “Mi ye sunan abin da yake cikin jakar nan, na ga kina yawan kulawa da shi” Uwais ya tambaya. Ivana ta kalle shi, amma kamar yanda wancan Uwais ɗin yake mata magaba ba tare da ya kalleta ba shi ma wannan haka. “Guitar sunanta, kuma ana yin kiɗa da ita, kamar dai sarewarka!” Ya jinjina kansa. “Ina son kiɗa sosai” Ya faɗa, kamar yanda wancan Uwais ɗin ya taɓa faɗa mata cewar yana son kiɗan guitar. “Ka iya busa sarewa?” “Sosai, ko kina so ki ji?” Ta gyaɗa kai, sai ya saka hannunsa ya zaro sarewar tasa dake saƙale a ƙugunsa, sannan ya kafata a bakinsa, ya soma busa sarewar cikin sauti me daɗin saurare, wanda ya cakuɗe da yanayin sanyin dajin da suke ciki. Hatta su Adam kansa busar sarewar tasa na musu daɗi. Hakan yasa tafiyar tasu ta ƙara armashi, suna tafe yana musu busa me kwantar da hankali, a lokacin kuma suka yi kiciɓis da tawagar wasu mutane, sanye cikin shigar jajayen kaya. Hakan ya sa suka tsaya suna kallon yawan jama'ar, kafin su yi wani yinƙuri har mutanen sun musu ƙawanya... Kuma sam ba su da kataɓus, dan sarkin yawa, ya fi sarkin ƙarfi. ASRA. Tsaye take a cikin dakarun da take da alhakin koyar da su salon yaƙi na masarautar Jiyad, yayin da suke a wani babban fili da aka tanada domin koyar da faɗa a cikin masarautar, wani lallausan yashi ne zube a ƙasan wurin, yayin da muggan makamai na koyon salon yaƙi ke aje a ko wace kusurwa na wurin. Ta harɗe hannayenta, yayin da take kallon yanda ɗaliban nata ke nuna mata abin da ta koyar da su. Tun daga nesa suka fara jin takun sawun masu gadin Malik Cangaz, hakan yasa ta dakatar da ɗaliban nata tun kafin ƙarasowar sarki wurin. A kan idonsu aka buɗe ƙofar filin, Malik Cangaz tare da masu tsaronsa suka shigo cikin filin. Hakan yasa Asra da ɗalibanta duka suka durƙusa domin kwasar gaisuwa. Sai da sarki ya amshi gaisuwar tasu, sannan kowa ya miƙe kan ƙafafunsa, hakan ya bawa Asra damar matsawa kusa da Malik, domin jin abin da ke tafe da shi. Yau ma kammaninsa sak na matasa, ba za ka ce shi ne mahaifin gimbiyoyin uku ba, kai kace wani yayansu ne. “Horarwa na tafiya yanda ake so Asra!” Cewar Malik cike da izza, Asra ta yi murmushi tana duban mahaifinta, sannan ta jinjina kanta a ladabce. “Sosai ma kuwa Darvesh (Holy man)” “Ko za mu iya ganawa na wasu daƙiƙu?” Faɗin Malik Cangaz, Asra ta gyaɗa kai, a tare suka taka zuwa wata kusurwa dake cikin filin, wadda ta fitar da su (balcony) dake can saman fadar, daga wurin ma za ka iya hango gine-ginen gidaje masallatai da kuma kasuwar masarautar kaf. “Zuwa yanzu kwanaki uku kacal suka rage a ɗaura auren Iqrah da yariman Azad... Duk wasu shirye-shirye mun kammalasu, ɓangaren tsaro ne ba mu yi komai ba, dan haka ina so a tabbatar da tsaro a masarautar nan, domin akwai tarin baƙin da za su zo daga baƙin masarautun da suke maƙotantaka da mu... Ba na son a samu wani kuskure!” Asra ta jinjina kai tana saƙala gashin kanta a bayan kunnenta. “Zan tabbatar da hakan Darvesh...” “Zuwa gobe zan je kaiwa abokina sarkin Mamlakatul Dahi goron gayyata, domin ba na so na aika Manzo! Na fi so na je da kaina domin isar da saƙon... Dan haka ki shirya, ina so ki min rakiya!” Asra ta risina cikin girmamawa. “An gama Darvesh...” “Na sallameki” Da haka ta juya ta barshi tsaye a wurin yana kallon girman masarautarsa. Kafin kuma amintaccen hadiminsa ya shigo wurin a hanzarce. “An kamo matasan da ake zargi da cin amanar ƙasarmu ta hanyar fitar da bayanan kasuwancinmu na sirri ya shugabana!” Cewar hadimin, bayan ya kwashi gaisuwa. Malik ya dube shi cike da isa, sannan ya furta. “A kai min su kurkukun cikin ƙasa, a gana musu azaba ta mako guda, kafin na kai ga zartar da hukuncin da ya dace a kansu, kafin su mutu ina so su ɗanɗana azabar da za ta bawa duk wani me sha'awar aikata laifi irin nasu tsoro!” Hadimin ya risina cikin alamar dake nuna ya karɓi saƙon shugaban nasa. “An gama ya kai wannan adalin sarki!” Daga haka shi ma ya fita daga wurin ya barshi, tsaye cikin sallalamin jiran ranar da boka Jalis zai sake naimansa. Domin tun bayan ranar da suka haɗu a kan maganar gano matasan nan uku bai sake naimansa ba, kuma hakan na nuna cewa har yanzu boka bai gano inda suke ba. A tsarinsa shi kuma ba ya zuwa wurin bokan ba tare da bokan ya naime shi ba... Amma a wannan karon dole ya karya ƙa'idar, dole ya je ya ji yanda aka yi aka haihu a ragaya. MAMLAKATUL AFSAH. Cike da zaƙuwa Malik Safraz ya ɗaga kai ga tawagar ɓoyen da yakan aika domin bincike, ya ƙagu su sanar da shi inda takobin mulkinsa yake. “Ya shuganmu, haƙiƙa takobinka ya bayyana a ban ƙasa, sai dai samunsa shi ne abu mai matuƙar wuya a gareka!” Muryar ɗaya daga cikinsu ta furta, ba tare da ya bayyana ba, domin ko shi kansa ba ya iya ganinsu sai idan sun so hakan. Ya ɗaga kansa ya kalli saitin inda maganar ke tashi, sannan ya furta. “Shin har akwai wani abu da zai gagareni samu a faɗin wannan duniyar?” “Ƙwarai kuwa ya shugabanmu, kuma wannan takobi na ɗaya daga ciki!” “Me nene dalilinku na faɗin hakan?” “Wanda yake tare da takobin shi ne abin ji, domin ko da yankar naman jikinsa za'ayi a kan takobin nan sai dai a yi, amma ba zai taɓa bari a raba shi da wannan takobi ba...” “Waye shi?” Malik Safraz ya tambaya ransa na ɓaci. “UWAIS!” Muryoyi uku suka ba shi amsa take, a nan ne fa hantar cikinsa ta fara motsi, domin in har Uwais ko Feroza na raye a ban ƙasa mulkinsa na cikin haɗari!... Ke nan me ya kamata ya yi a wannan gaɓar!?... Tambayar ta tuno masa da wata hatsabibiya ɗaya da zai iya sawa wannan aikin hankali kwance. Lokaci guda ya yi murmushi, sai kuma ya haɗa da dariya yana jinjina kai, sannan laɓɓansa suka furta sunanta. “NATILA!” GARIN QUDWA, YANKIN GABASHIN SAHARAR SUBAH. Hayaniyar jama'ar dake kaikawo a cikin 'yar ƙaramar kasuwar garin ce ta cika ko ina. Komai na kayan siye da siyarwa daga ƙasashen duniya akan kawosu kasuwar wannan gari na Qudwa. Domin garin ya kasance cibiyar kasuwanci, duk da garin bai cika girma ba. Ko wani mutum dake cikin kasuwar za ka same shi sanye da shiga irin ta garinsu ko yankinsu, ko kuma masarautarsu. Yayin da ake hada-hadar cinnikayya a cikin kasuwar. Wata iska me ƙarfi ta taso daga cikin sahararar dake gabas da kasuwar, hakan yasa ƙura ta shiga bule mutanen cikin kasuwar.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35