Chapter 24
Chapter 24
sarki masu yasa gadi ba su yi ƙoƙarin dakatar da su ba, suka yi saurin wangale maƙareriyar ƙofar ganuwar masarautar. Ko da suka bar fadar dajin dake kusa da masarautar suka kutsa, dokunan na gudu a cikin dajin, yayin da Sarki Cangaz dake keken dokin ya matsu da su kai ga ƙarasawa fadar bokansa. Domin a daren jiya ya samu saƙo daga wurin bokan nasa, kan yana son ganinsa a safiyar yau, hakan ya sa ya yi sammakon tashi. A lokacin da ya ji dokunan tare da keken sun tsaya cak, matsuwa tare da zaƙuwarsa na son ganin bokan ta ninku, ta yanda bai jira matuƙin ya buɗe masa ƙofar ba, da kansa ya buɗe ya fita, duk wata izza da isa da yake nunawa a masarauta a cikin dajin bai yi ta ba. Hasalima sauri ya yi ya faɗa wani gida dake jikin bishiya a cikin ƙungurmin dajin. Yana buɗe ƙofar ya kutsa kai cikin gidan, babban boka Jalis dake durƙushe a gaban wani maƙareren allo ya ɗaga kai ya kalli Cangaz kammaninsa suke a na matashi, domin akwai wani sabon tsafi da boka Jalis ɗin ya haɗa masa a kwana nan, wanda yake sawa kamanin matashin kan yi tsawon kwanaki a jikinsa har na kimanin mako biyu, durƙushewa ya yi a gaban bokan, yayin da Boka Jalis ke ƙare masa kallo, fuskarsa ɗauke da murmushi. “Ka yi kira na amsa Jalis, da fatan da wani labari me daɗi ka zo min” Muryarsa me ɗauke da izza da ƙasaita ta furta suna duban juna shi da Boka Jalis. “Ƙwarai kuwa shugaban talakawa. Mafarkin da ka daɗe kana yi na tsawon kwanaki ne ya zama gaskiya...” “Ka yi saurin sanar da ni abin da yake faruwa” Ya yi saurin katse shi, dan sam ba ya son wani tambihi, boka Jalis ya girgiza kai yana murmushi, sannan a hankali ya juyawa Malik Cangaz fuskar allon dake aje a gabansa, Malik Cangaz ya kalli allon dake ɗauke da hoton wasu matasa uku, waɗan da sam kammaninsu da kuma shigarsu ba ta yi kama da ta mutanen duniyarsu ba, cike da kokwanto ya kalli boka. “Baƙi aka yi daga wata duniyar?” Boka Jalis ya girgiza kai. “Ba za mu iya kiransu da baƙi daga wata duniyar ba kai tsaye, amma za mu iya kiransu da baƙin sa'a, masu tafe da cikar mafarkinka... Kalli ka ga” Ya ƙarashe yana nunawa Malik sarƙar wuyan Arman. “Wannan shi ne makullin ƙofar da muke ta naiman mabuɗinta... Wannan makullin shi ne ƙarshen abin da zai sa ka ci gaba da zama a matashi har duniya ta naɗe” Lokaci guda Malik Cangaz ya saki wani ƙassaitaccen murmushi, suka haɗa ido da Boka Jalis. “Shin a ina waɗannan matasan suke? Domin ba na so na ƙara ko da sa'a guda ba tare da na buɗe ƙofar nan ba” “Ai ba'a nan gizo yake saƙar ba Shugabana, waɗannan matasan uku da kake gani, sam ba mutanen wannan zamanin namu ba ne, ƙaddara ce ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu zuwa wannan zamanin namu. Kuma a halin da ake ciki su ma suna fafutukar yanda za'a yi su koma zamaninsu. Sannan an sanar da su cewa wannan ƙofar taka ita ce ƙofar da za ta mayar da su zamaninsu, dan haka su ma kansu suna tunkararka ne, ba kai ne kaɗai kake naimansu ba...” Malik Cangaz ya miƙe tsaye, ya yi taku uku tare da juyawa boka Jalis baya. “Ai ko ba za su taɓa komawa zamaninsu ba, domin ba zan taɓa bari su kai ga ganin ƙofar nan ba, ballantana har ta kai ga sun samu damar shiga cikinta... Zan sa a naimo min su duk inda suke a duniyar nan, domin a karɓo min makullin da suke tare da shi, saboda na buɗe ƙofar nan na cika burina!...” Ya ƙarashe yana bushewa da dariya, shi dai Boka Jalis bakinsa ya ja ya yi shiru, dan ba zai sake cewa komai ba, shi ya san abin da ya gani kawai, domin Malik Cangaz farkon yaƙin ya sani kawai, bai san ya ƙarshen yaƙin zai kasance ba, kuma shi ɗin ma da ya sani ba zai faɗa masa ba domin tsira da rayuwarsa... Malik Cangaz ya juyo tare da duban Boka Jalis. “Haƙiƙa yau ka sanar da ni labarin da ya fi ko wanne daɗi a duniyar nan, dan haka dole na maka gagarumar kyauta, sannan ina gayyatarka zuwa wurin ganawa da yariman masarautar Azad, wanda zai zo tare da mahaifinsa a kan maganar auren Gimbiya Iqrah, da fatan za ka zo?” Boka ya jinjina kai yana murmushin ɓoye sirrin zuciyarsa. “Ƙwarai kuwa shugabana, zan kasance a wurin a lokacin da ake buƙata!” DANEEN IQRAH. Yalwataccen hasken rana da ya fara ratsowa cikin masarautar ne ya samu damar shiga ɗakinta ta hanyar ƙatuwar tagar dake saman ɗakin. Hasken ranar ya samu nasarar sauƙa a kan wata kyakkyawar hallita dake kwance a kan katafaren gadon dake tsakiyar ɗakin. Kyakkyawan dogon gashin idonta na sama ne ya ɗaga zuwa sama, farin idonta dake ɗauke da ƙwaya kalar (brown) ya bayyana, sake rufe idon nata ta yi, sannan ta sake buɗe shi a karo na biyu, ta saka dogayen fararen yatsun hannunta, ta murza idonta, sannan a hankali ta saka hannunta ta yaye mayafin da ta lulluɓa da shi, ta tashi zaune, yayin da gashin kanta me tsayi ya lulluɓe kafaɗunta da kuma gadon bayanta. Lokacin da ta yi miƙa tare da hamma kuyangu da bayin da suka saba mata hidima a kullum rana suka fara shigowa ɗakin ɗaya bayan ɗaya, kowanne ya shigo ɗakin sai ya miƙa mata gaisuwa, sannan zai fara aikinsa na kullum. Yayin da ita kuma ta nufi bayin dake cikin ɗakin, wasu kuyangu biyu suka rakata zuwa bayin, domin tayata tsaftace jikinta. Lokacin da suka dawo ɗakin har an gama tsaftace ko mai da ko ina, a kan wata kujera ta zauna, kuyangun da aikinsu shi ne shirya gimbiya suka kewayeta, kowa da aikin da yake, wasu na gyara mata gashi, wasu na aikin gyara mata fata, yayin da wasu na taimakawa wurin saka mata tufafi. Sai da suka ƙawata sarauniyar da ado irin wanda ya dace da duk wata 'yar sarki me jin isa da iko a wannan zamanin, sannan suka koma gefe, masu aikin kawowa sarauniya shayinta na safe suka matso, aka bata shayin ta sha, sannan ta tashi domin zuwa ɗakin karin kummalo da kowa ya saba halarta domin cin abinci. Sai da ta yi taku uku, sai kuma ta dakata, hakan ya sa su ma bayin da suka shirya domin take mata baya suka dakata. Cikin iko isa da izza ta kalle su da gefen ido. “Ku bani wuri, akwai abin da zan gabatar cikin sirri” Ta furta cikin muryarta me sanyi da zaƙin sauraro. Dukan ma'aikatan nata suka risina mata, alamun sun amsa saƙon nata, sannan suka soma barin ɗakin ɗaya bayan ɗaya. Sai da suka fita daga ɗakin gaba ɗayansu, ya rage sai amintacciyar hadimarta kaɗai a ɗakin, ta kalli hadimar da kanta yake a ƙasa. “EID ya aiko da wani saƙo?” Hadimar ta jinjina kanta dake ƙasa. “Ƙwarai gimbiyar kyawawa...” Daga haka ta nufi tagar ɗakin dake a bangon gabas, ta saka hannayenta ta buɗe ƙofar, hakan ya bawa mujiyar (owl) dake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35