Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,202 words 0 views Progress saved
Download Book

cikin raina na fi son ka zamto magajin Alhadi fiye da Faisal Arman...” Arman ya yi murmushi, dan ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi. “Jadda me yasa kowa yake son na zama shugaban Alhadi?” Ya matambaya. “Saboda kai kafi cancantar zama shugaba... Alhadi kamfanin mahaifinka ne, Anwar hannun jari kawai yake da shi!” Jadda ta ba shi amsa, ya girgiza kansa yana murmushi. “Jadda bani da suffofin shugabanci, saboda inada nakasar gani, ba zan iya shugabanci ba” “Arman! Ka ga wannan kujerar dake cikin office ɗin Iƙbal? Ka ɗauketa tamkar kujerar wata babbar masarauta a zamanin baya. Wadda ake yaƙi da zubar da jini duk domin a mallaketa, wannan kujerar na dai-dai da kujerar katafariyar fada a zamanin baya!” “To wai duk me ya kawo wannan zancen?” Jadda ta yi murmushi. “Saboda ba ma so ka bamu kunya. Nan da kwana uku zagayowar ranar da aka haifeka. Iyayenka na shirya maka babban shagalin taya murna. Kuma a wurin shagalin mahaifinka ya ɗauki niyyar baka takardun shugabancin gamayyar kamfanunuwan Alhadi, domin ka sa hannu a matsayinka na shugaba na gaba. Kuma ba na fatan ka bamu kunya Arman!.” *Maison De Curry, Souk Al Bahar, Sheikh Mohammed bin Rashid Blvd, Downtown Dubai, United Arab Emirates.* *10:52 na dare.* THE ADVENTURERS. “Wai me ya faru ne?” Ivana ta tambayi Arman da ya tarasu a restaurant ɗin, kuma ya zauna ya yi shiru ba tare da yace komai ba. Arman ya juya kansa ya kalli Fountain show dake nan kusa da restaurant ɗin, kuma ta tsakanin Fountain ɗin yana iya ganin dogon ginin Burj Khalifa. “Yau saura kwana biyu zagayowar ranar da aka haifeni. Abby da Immi suna shirya shagalin zagayowar ranar” Ivana da Adam suka dubi juna. Sannan suka kwashe da dariya suna tafawa, hakan ya sa Arman ya kallesu da mamaki. “To ai duk mu ma mun san wannan. Dan mu ma muna shirya namu shagalin... Mi ye na damuwa a ciki” Arman ya saka hannu ya shafa ganshi kansa dake a nannaɗe, sannan yace. “Ba wai batun shagalin ne abin da yasa ma taraku a nan ba. Abby yana shirin danƙa min takardun shugabancin Alhadi... Kuma kun san cewa wannan shi ne abin da bana so” Cak Adam da Ivana suka dakata da dariyar da suke, sannan suka dubi juna. Kafin Adam ya kalle shi. “Man! Ni fa da za ka ji shawarata da ka karɓi shugabancin kamfanin nan. Kasancewarka shugaba shi ne burin mahaifinka na ƙarshe. Bayan duk abubuwan da ya mallaka maka a rayuwa kuma sai ka kasa cika masa wannan burin?... Burin da a ƙarshe kai ne wanda za ka amfana da shi” Ya gyara glasses ɗinsa, sannan yace. “Adam ina so na cika burin Abby, saboda ban taɓa neman komai a wurin Abby na rasa ba. Duk abin da na naima cikin gaggawa Abby ke mallaka min shi, dalilina na ƙin shugabanci shi ne, duk wani abu da zai sa a na min kallon nakasasshe ba na sonsa. Duk wani abu da zai zama silar da za a muzantani gudunsa nake, bana so ana aibanta ni Adam. Kuma ku duka kun san cewa ta dalilin wannan kamfanin Ammu Anwar da Faisal da kuma Sakina ke aibantani a ko ina... Shi ya sa nake gudun Alhadi” Shiru ya ratsa tsakaninsu, dan duk abin da ya faɗa gaskiya ne. “Arman” Faɗin Ivana tana kama hannunsa. “A ganina maganar mutane bai kamata tasa ka sare da rayuwa ba. Allah shi ne me bada lafiya, kuma idan ya so a yanzu zai iya baka lafiya. Kuma tun da kana iya gani da taimakon glasses me zai hana ba za ka jarraba bin abinda iyayenka ke so ba” Ya girgiza kansa, Ivana da Adam suka sake duban juna. Sun san abokinsu da taurin kai, tun da yace a'a to fa ba zai sauya ra'ayinsa ba. “Yanzu mi ye shirinka?” Adam ya tambaya. Ya kallesu su duka biyu. “Kamar yanda suke zato. Sam ba zan taɓa basu kunya ba, domin da ace ban san da batun shagalin nan ba da zan amince na je wurin shagalin, kuma idan ya bani takardar a gaban kowa zan saka hannu. Amma tun da har na sani ba zan je wurin shagalin ba” “Me kake nufi?” Ivana ta tambaya a mamakance. “Zan bar Dubai a ranar da suka shirya shagalin, yayin da suke shirya shagali a nan ni kuma zan yi nawa shagalin a wata ƙasar” Adam ya girgiza kai. “Hakan bai kamata ba Arman. Da wannan abin da za ka yi sai ka fi basu kunya, fiye da ƙin amincewa ka sa hannu a gaban jama'a.” “Adam ya zan yi?... Sam ba na son abin da suke so, na kasa fahimtar da su, ya suke so na yi?” Suka yi shiru, tausayin abokinsu na kama su. “Shikenan. Mun yarda da shirinka, amma ba za mu barka ka tafi kai kaɗai ba, duk inda za ka je za mu kasance tare da kai” Faɗin Ivana tana kallon Adam, shi ma Adam kansa ya jinjina, alamun ya amince. Arman ya yi murmushi yana kallon abokansa biyu. “Amma ina kuke ganin za mu tafi?” “Tun da ni zan je ɗaukan hoto me zai hana mu tafi Nigeria?” Adam ya tambaya. Arman ya girgiza kai, a lokacin da idonsa ya kai kan allon da zai sauya akalar labarin gaba ɗaya, kuma allon dake ɗauke da zanen ƙaddararsu. Wadda za ta yi juyi irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi. Lokacin da ya gama karanta sunan wurin a jikin allon, fatar bakinsa ta furta sunan dajin a hankali. “Bayericher wald (Bavarian forest)!” “Germany ke nan?” Cewar Adam, Arman ya gyaɗa kansa. “Dajin yana da kyau sosai. Sannan za mu shaƙata a cikinsa, kai kuma za ka samu abubuwan da za ka ɗauka a cikin dajin... Kamar dai wancan hoton!” Ya ƙarashe yana nuna musu wani allo dake ɗauke da hoton Bavarian forest ɗin. Suka waiga suka kalli board ɗin a tare, allon dake ɗauke da zanen sauya labarin kowanne a cikinsu. *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai* IVANA POV. Sanye take da yellow maxi skirt, da farar shirt, wadda a samanta ta saka denim jacket. Tana zaune a kan gadonta, yayin da take goge guitar ɗinta da hanki, Yumma kuma na shirya mata kayanta a cikin jaka, dan ta riga da ta sanar mata da cewar za su yi tafiya tare da su Arman. “Ivana” Yumma ta kirata tana saka wasu takalmanta a cikin jakar da take shirya mata kayan. “Na'am Yumma” Ta amsa tana ɗaga kanta, tare da kallon Yumman. “Me ya sa Arman ba ya son ya karɓi abin da yake nasa?” Ivana ta girgiza kanta tana murmushi, ta saka hannu ta ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sannan tace. “Tun yana yaro kawunsa da wasu daga cikin 'yan uwansa suka raunata masa zuciya. Bayan nakasar ido da yake da ita sun ƙara masa da nakasar zuciya Yumma. Abokina yana da zuciyar zinare, yana son taimakon wanda ba shi da shi, duk da tarin dukiya da Allah ya yi wa mahaifinsa sam ba ya dubawa, domin ba ya nuna banbanci tsakanin mu da shi. Amma wannan raunin da suka yi a zuciyarsa yasa sam ba ya son zama shugaban Alhadi...” Ta ƙarashe tana ɗaga

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35