Chapter 6
Chapter 6
shi tana ture shi. “Ni dai ka cuceni” Ta faɗa tana sake ture shi, hakan ya sa glasses ɗin dake idonsa ya faɗi ƙasa, duhu ya mamaye sashin ganinsa, dan daga zarar ya rabu da glasses ɗin babu abin da yake gani face duhu. Cak ya tsaya yana motsa idonsa da babu abin da yake gani da shi, hannunsa ya miƙa kan inda yake zaune, yana laluben glasses ɗin nasa, dan ko tafin hannunsa ba ya iya gani, ita ma Gulzar ɗin sai a lokacin ta lura da shi. “Ya Ilahi ana asfe aki” (Wayyo Allahana ka yi haƙuri Yayana) Ta faɗa tana ɗaukan glasses ɗin nasa da ya faɗi ƙasa, ta goge shi a jikin rigarta, sannan ta saka masa shi. Glasses ɗin na hawa kan fuskarsa ya fara gani, sai ya raintse idonsa, sannan ya buɗe. “Mein bahut off-sori hoon bhradaar, mein iss ka matlab nahin tha...” (Ka yi haƙuri Yayana, ba da niyya na maka hakan ba) Ta faɗi cikin harshen Urdu tana dafa kafaɗunsa, sai ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai. “Ma fi shi, insi halla (Ba komai fa, ki manta kawai)” Gulzar ta jinjina kanta, sannan ta miƙa hannu ta ɗauki Hummus daga cikin kayan maƙulashen dake kan teburin kusa da su, ta miƙa masa. “Za ka ci?” Ya ɗan yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya karɓa daga hannunta, ita ma ta ɗauki wani bowl ɗin suka fara ci tare. “Yau mun haɗu da Faisal a Coca-cola Arena” Arman ya faɗa yana kallonta, ita ma sai ta kalle shi tana gyara zama. “Ya faɗa maka wani abin ko?... Kuma me ka masa?” Ta jero masa tambayoyin, sai ya yi dariya yana shafa sumarsa dake cikin askin curly top, dan har sauƙowa take kan goshinsa. “Ban masa komai ba, kuma ban ce masa komai ba, Ivana ma da ta yi ƙoƙarin ce masa wani abin hanata na yi” Gulzar ta harare shi. “Shi ya sa gaba ɗaya ya bi ya rainaka, ba finka ya yi a haife ba amma kullum gainka yake kamar ƙaninsa. Ni ba za ka burgeni ba sai ka yarda ka karɓi shugabancin Alhadi. Ba ma ni kaɗai ba daga lokacin za ka bawa kowa na ahalin nan mamaki” Arman ya ɗaga kansa sama yana kallon taurarin dake ko ina a sararin samaniya. “Shugabancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ya fi ƙarfin makaho kamar Arman, bara a gefen hanya ita ce tafi dacewa da shi!” Gul ta ja tsaki tana aje bowl ɗin hannunta. “Wannan ra'yin wasu mutane ne da ban, kuma idan har ka ci gaba da faɗin haka kana nufin shugabancin ya fi dacewa da shashashan mutum kamar Faisal?” Armaan ya kalleta yana ɗage kafaɗunsa. “Ban sani ba!” Gulzar ta ɗauke ka tana juya idonta, kuma idon nata bai sauƙa a ko ina ba sai a kan saman gidan su Faisal dake ɗan gaba da nasu. Daga nan inda suke tana iya hango Faisal da ƙanwarsa Sakina zaune a saman nasu gidan, masu aikin gidan zaune a wurinsu suna musu hidima. “Kalli can” Arman ya kalli inda take kallo. “Yanda Sakina take ji da kanta kai kace ita matar sarkin Dubai ce. Ko a makaranta ba ta da ƙawaye sai 'ya'yan masu kuɗi. Kullum jin kanta take kamar wata sarauniya, tana kashe kuɗi ta yi yanda ranta yake so. Shi kuma Faisal, lalataccen ɗan da babu uban da zai yi alfahari da shi, a ƙalla 'yan matansa sun kai sha bakwai, babu hotel ɗin da bai taɓa zuwa ba a Dubhai, har ɗaki yake da shi a Burj Khalifa, yanda yake wadaƙa da kuɗi za ka ɗauka cewa babansa ne a kan kujerar shugabancin Majmu'at Shirkat Alhadi, daga an taɓasu za su ce su ne Faisak (FAISAL AND SAKINA)! Humm! Abin haushi” Ta ƙarashe tana mayar da gashinta dake kan kafaɗunta zuwa bayanta, Arman ya yi dariya. “Komai lokaci ne Gul, ki ƙara haƙuri” Ta masa wani irin kallo, sannan ta ɗauke kai. “Lokacin ba zai ƙare ba har sai ka karɓi shugabancin Alhadi.” “Wannan lokacin ba zai taɓa zuwa ba” Arman ya bata amsa zuciyarsa ɗaya. Da Gulzar ta ga takaicin ɗan uwan nata na neman kasheta sai ta miƙe ta bar shi a wurin. “Gobe laraba, ka shirya zan rakaka wurin Doctor Ƙuraishi” Ta faɗa tana barin wurin, Armaan ya yi dariya, Dr Kuraishi shi ne likitan idon da yake duba shi tun yana ƙarami. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. A razane ya kalli tvn da Maama ta ƙure Volume ɗinta, razannaniyyar ƙarar da ta fito daga cikin tvn ce take naiman sawa ya saki fitsari yana zane. “Maama dan Allah ki rage Volume ɗin nan” Ya faɗa yana marairaicewa, kuma cikin harshen hausa, dan a gida sam ba ya larabci ko wani yaren da ba hausa ba, sai idan ya shiga cikin abokansa ne yake magana da wani harshen, tun da su larabawa ne, saɓanin shi da ya kasance ɗan bahaushe. Maama ta yi tsaki, sannan ta kashe kayan kallon gaba ɗaya, ta dawo ta zauna kusa da shi kan sofa, inda yake zaune a tsorace yana cin abinci, Maama ta dungure kansa tana faɗin. “Kai dai ka ji jiki. Na rasa a ina ka kwaso wannan shegen tsoron, kai ba mace ba, amma tsoro kamar farar kura, na rasa yaushe za ka daina wannan tsoron, ni dai ina jiye maka ranar da tsoron nan naka zai kasheka kana tsaye.” Ya ƙifƙifta idonsa yana haɗiyar abincin dake bakinsa. “Ya kamata gobe ka je wurin aiki, tun da yau ba ka je ba” Ya jinjina kansa, dan har yanzu a dame yake. “Akwai sauran wani aiki da shugabanmu ya bani. Ina so na ƙarasa kafin gobe” Maama ta ɗauki wayarta, sannan ta miƙe tana faɗin. “Ya kamata dai, kuma saura ka sake kallon wani film ɗin ban tsoron, wallahi ko ta kanka ba zan bi ba” Sai ya ɗan yi murmushi yana kallonta, har ta bar shi nan zane a falon, a ƙalla yanzu kimanin shekaru biyar ke nan da rasuwar mahaifinsa. Kuma tun bayan lokacin ya rage daga shi sai Maama ne kaɗai suke rayuwa a gidansu. Mahaifinsa yana aiki a wata asibiti dake nan Dubai, kuma aikin shi ne abin da ya rabo shi da mahaifarsa wato Zamfara Nigeria. Dan shi kansa Adam ɗin ma a nan Dubai aka haife shi, kuma har bayan rasuwar Mahaifinsa ba su koma Nigeria ba, saboda shi ma yana aiki a nan. Salma Ahmad Isah ✍️ _Har yanzu somin taɓi ne, domin muna duba da rayuwar jaruman namu ne, kafin mu tsunduma cikin labarin... Ku fai kada ku gajiya, ku biyoni domin jin yanda za ta kaya..._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°° . 🪄...JUYIN KWAƊO...🪄 ©️Salma Ahmad Isah SalmaAhmadIsah @ArewaBooks SalmaAhmadIsah @Wattpad Page-3 *Moorfields Eye Hospital, 20 street Al Razi Building 64, Block E, floor 3, Dubai.* ARMAN POV. “Buɗe idon a hankali” Dr Ƙuraishi ya bawa Arman umarnin yayin da ya gama duba masa idonsa. Arman ya buɗe idonsa a cikin hasken da Dr Ƙuraishi yake haska idonsa. Amma babu abin da yake gani face duhun da ya saba gani, saboda shi bai san banbancin da yake tsakanin idonsa na a rufe ko a buɗe ba, tun da duka biyun
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35