Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

nuna ƙirjinsa da keyn motar dake hannunsa. “Eh kai nake so ka zo ka kaini, saboda akwai wasu kaya da zan sai maka kaima” Sai ya yi dariya. “Gani nan zuwa” Ya katse kiran, tare da aje wayar, sannan ya yi wa motar key yana kunna wata waƙar Sa'ad Lamjarred da Elissa me taken Min Awal daƙiƙa. Da haka ya koma gida, ya je ya ɗauko 'yar rigimar tasa, sannan ya nufi Dubai Mall. Sai a lokacin ya lura da shigar da Gulzar ɗin ta yi. Wasu pink Chickankari (Pakistan) ne a jikinta. Rigar kayan da ta kusa taro wandon tsayi na ɗauke da ratsin sea green daga ƙasa, hakan yasa mayafin kayan ma ya kasance net sea green, wanda ta yafa shi a kanta, ammma duk da haka bai hana dogon gashinta bayyana ba. “Gul” Ya kira yana duban hanya, ta ɗago daga barin kallon wayarta ta dube shi. “Umm” “Su kuma waɗannan kayan fa?” Ta dubi jikinta. “Mi ye laifinsu?” Ta tambaya, ba tare da ta hangi makusar kayan nata ba. “Amma Aii (Mahaifiyar Immi dake Pakistan) ce ta aiko miki da su?” Gul ta ƙanƙace ido tana kawar da gashin da ya kwanta mata a gefen fuska. “Wato ni ba zan iya siyan Chickankari da kaina ba sai Aii ta aiko min ko?” Arman ya yi dariya, dan da ma abin da yake so ke nan. Ita ma da ta gane cewa kunnata yake son yi sai ta ɗauke kai tana duban wurin da suke nufa. “Akhi ni fa Mall of the Emirates zan je ba. Dubai Mall ba” Ya dubeta. “Shi Dubai Mall ɗin mi ye laifinsa. Na ga ko Immi a nan take siyayya” “La (No) ni ba zan je can ba, yau Mall of the Emirates nake son zuwa” Arman ya girgiza kansa. Sannan ya juya kan motar zuwa wata hanyar da za ta fi saurin sadasu da Dubai Mall ɗin da take son zuwa. Siyayya ta yi kamar ba ta masu hankali ba, dan kaya ta yi ta jibgowa kamar da za'ayi bikin aure ba na ƙarin shekara ba. Shi dai Arman bai isa yace ƙala ba, tun da Abby ne ya ɗaure mata gindi, don hatta da kuɗin siyayyar ma shi ya biya, yau da safe tace za ta je siyayya, dan haka ya bata ɗaya daga cikin ATM cards ɗinsa. Yayin da kowa na ahalin Alhadi da sauran 'yan uwan mahaifiyar Arman da suka samu zuwa tun daga Pakistan ke shirya masa kyakkyawar liyafa ta taya shi murnar ƙarin shekara. Shi da su Adam kuwa na can suna shirya tafiyarsu zuwa Germany. Shi da kansa yay musu booking flight, daga Dubai zuwa Germany, wanda zai tashi a daren da zai cika shekaru 32 a duniya. Kuma a ɓoye yaje ya yi siyayyar wasu kaya da zai buƙata a tafiyar tasa ba tare da ya bar kowa na ahalinsa ya sani ba. Hannu ya sa ya buɗe wata drawer dake kusa da dressing mirror ɗin ɗakinsa. Ban da glasses iri-iri babu komai a ciki. Gaba ɗaya glasses ɗin cikin drawern irinsu ɗaya, domin duka farare ne, masu ɗauke da square frame, banbancinsu kawai shi ne rims ɗin da suka zagaye frame ɗin glasses ɗin. Dan kaloli ne birjit, kuma ko wace kala akwai kayan da yake sakawa da shi, shi yasa adadin glasses ɗinsa suka wuce ɗaya, amma kuma ya fi saka mai farin rims da kuma mai baƙi. Glasses biyu kawai ya ɗauka, dan ba ya jin za su yi wata daɗewa a can da har zai ɗaibi sama da uku, har wanda yake tare da shi a yanzu. Wani kit ya ɗauka ya saka glasses ɗin duka biyu a ciki, sannan ya dawo kan gadonsa, inda jakar kayan da yake haɗawa take, ya saka kit ɗin a ciki. Kuma yana saka shi ya zuge jakar, domin ya gama saka duk wani abin buƙatarsa a ciki. Sauƙewa jakar ya yi daga kan gado, ya jata zuwa ƙofar bathroom ɗinsa, da nufin idan an jima kaɗan zai saka ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya fitar masa da ita waje. “Aki Wainak? (Yayana kana ina)” Da sauri ya fito daga wurin, jin Gulzar na ƙwala masa kira, tsaye ta yi tana kallonsa. Dan alamu sun nuna cewa wani abu yake ɓoyewa. “Mi ye?” Ya tambaya cikin son waskewa tambayoyinta. Ita da yake akwai abin da ya kawota sai ta manta da wannan batun, tace. “Su Rahma ne suka zo...” Cikin rashin fahimta ya kalleta. “Wace ce Rahma?” “Mts ƙawata da take Riyadh, ta zo ne domin tayaka murna” Sai ya dage girarsa duka yana kaida kai. “Ohh na gane” “Me kake ne?” Ta tambaya tana kallon dressing table ɗinsa da yake a hargitse, domin gujewa zargi sai ya ɗauki hair dryer ya shiga busar da gashin kansa da babu ruwa yana faɗin. “Gyaran kai nake, ke yaushe za ki je a rage miki tsayin wannan gashin naki” Gulzar ta kalle shi tana taɓa dogon gashinta. “Ai ba zan taɓa yanke wannan gashin ba” Ya taɓe baki yana aje dryer, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar da take sama, kafin ya juyo ya kalleta. “Su waye suka zo kuma bayan ƙawarki? Na ji hayaniya ta ƙara yawa a ƙasa” Ta ɗage kafaɗunta. “Ban sani ba, amma mu je mu gani” Ta ƙarashe maganar tana juyawa, ya aje comb ɗin da ya ɗauka ya bi bayanta. Ko da suka sauƙa ƙasan ba kowa suka ga ba face 'yan uwan Abby na Qatar da suka samu isowa. Duk dangi sun zo, kai kace bikin aure za'a yi ba na ƙarin shekara ba. Duk waji abu da suke Arman kallonsu kawai yake, dan gani yake kamar ihu suke bayan hari, a ganinsu bai san abin da suka shirya ba, shi ya sa wasu daga cikinsu ke farin cikin zai zama shugaba ba tare da sun furta ba. Amma shi ya san farin cikin na miye, kuma zai musu albishir na wannan burin nasu ba zai taɓa cika a yanzu ba... Tunanin nasa na tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙaddararsa, domin kamar yanda yake ganin cewa ba zai karɓi shugabancin Alhadi yanzu ba yabbas ba zai karɓa ɗin ba, kuma hakan zai faru ne sakamakon ƙaddarar dake jiransu a Bavarian forest. Wadda za ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu, daga ruwa zuwa ruwan zafi. *House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.* ADAM POV. Tsaye yake a gaban Maama wadda ke masa addu'ar Allah ya tsare shi, hannunsa riƙe da jakarsa ta kaya, yayin da yake murmushi yana dubanta. “Zan yi kewarki Maama” Ya samu bakinsa da furta hakan. Domin a ganinsa kamar sati ɗaya ya yi kaɗan da zai sa ya riƙa jin kewarta a ransa irin haka, Maama ta yi dariya. “A sati ɗayan? Na ga ka sha yin tafiyar da ta fi wannan tsayi, kuma kana daɗewa, sai wannan ta sati ɗayan ne zai sa ka yi kewata?” Ya aje jakar hannunsa, sannan ya rungumeta yana jin kamar ya fasa tafiyar, shi dai ba ya ce ga dalilin da ya sa yake jin cewa zai yi nisan gaske da ita ba. “Sakeni haka mana, sai ka karya min ƙashin tsufa” Faɗin Maama, sai ya saketa yana murmushi. “Allah ya

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35