Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Juyin Kwado Book One Complete Hausa Novels 1 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

ba ta cinyesu ba ya sa ya fara son kwantar da hankalinsa, kusan a tare suka dubi Ivana dake can nesa da su, hakan ya sa Arman ya miƙe ya nufi inda take, ita ma ya tasheta. “Wai a ina muke ne?” Adam ya tambaya yana miƙewa tsaye, yayin da Arman ya cillar da tsohon glasses ɗinsa da ya fashe, Ivana kuma ta ba shi wani domin ya saka, sai da ya saka glasses ɗin sannan shi ma ya tsaya ƙarewa wurin kallo, daji ne fetal, ba gida gaba ba gida baya. “Kai! Ina ƙofar da muka shigo?” Cewar Ivana tana waige-waige, amma sam babu alamar ta a wurin, shi ko Arman shiru ya yi yana wani lissafi a cikin kansa, idan zai iya tunawa bayan wannan Cheetah ɗin ta biyosu sun buɗe wata ƙofa sun shiga, bayan da suka shiga ƙofar kuma ba su iya ganin komai ciki sai haske, sai wani abu me kama da iska da suka ji ya kwashesu, to daga nan ne ba su sake sanin me ke wakana a duniya ba sai yanzu... “Arman a ina muke ne?” Adam ya tambaya yana riƙo Arman, shi kansa Arman ba shi da wannan amsar, domin bai san a ina suke ba, bai san ya aka yi suka zo nan ba. A hankali ya ɗan matsa bayan bishiryar da suke kusa da ita, nan ya hangi wata bukka guda ɗaya tal. “Ga wani ɗaki can, mu je mu duba” Ya faɗa yana ɗaukan jakarsa, tare da goyata a bayansa. Suma nasu kayan suka ɗauka, sannan suka bi shi, shi dai Adam ya san cewa ɗakin bukka ce, su kuma sauran ba su san wani abu me kama da hakan ba. Shi ya sa tun kafin su ƙarasa kusa da bukkar suka fara taradaddin a duniyar da suke. Ko da suka iske bukkar sai aka tsaya kallon-kallo, dan ba su san me za su iske a ciki ba. Arman ne ya fara ƙundun balar nufar ƙofar, yana taku a hankali, hannunsa ya sa ya ɗaga wani abu me kama da labule da ya saya ƙofar, hakan ya ba shi damar ganin cikin ɗakin. Babu komai a ciki face tarin littattafai irin na da, da kuma wasu takardu da aka yi su da fatar dabbobi, sai wani gadon ciyawa dake a gefe, sannan wani gajeren teburi, wanda a kusa da shi wani farin dattijo ne zaune. “Barka da zuwa JAGORA” Su ne kawai kalaman da dattijon ya furta yana ɗora ido a kan Arman. Shi kuma Arman tsaye ya yi yana kallon tufafi da kayan ɗakin mutumin, ko kusa ko alama bai yi kama da wanda yake rayuwa a zamaninsu ba, mutumin ya fi kama da irin mutanen da suka rayu a baya. Shiru suka yi su ukun, yayin da suke zaune gaban dattijo, banda kallonsa ba abin da suke, suna jiran ya amsa musu tambayoyin da suka soma masa, shi kuma sai murmushi yake musu, kamar wanda ya san da zuwansu. “Ina ne nan?” Arman ya sake nanatawa datijjon tambayar da Ivana ta fara masa tun ɗazu. Kuma sai yanzu ya samu damar ba shi amsa. “Hayy al- Umda!” Arman Ivana da Adam suka dubi juna cike da kokwanton da ya zarce na da, su har yanzu sun kasa gane abin da yake faruwa, amma Arman ya fara fuskantar wani abu guda... “Ban taɓa jin sunan dajin nan ba, kuma mu a Bavarian forest muke ba Hayy al- Umda ba” Cewar Ivana. Dattijo ya yi murmushi, sannan cikin larabcinsa me matuƙar daɗi da bawa ko wani harafi hakkinsa yace. “A halin yanzu kun bar zamaninku matasa, a yanzu kuna zamaninmu ne, a ƙalla shekaru 1000 baya!” Wani abu ne ya bada sautin tau a ƙirjin Adam, dan zai iya cewa ya riga kowa sauraron shekaru dubu ɗayan da aka furta. Ita kuma Ivana sai ta ji kamar ba ta fahimci abin da yake faɗa ba, saboda kalar larabcin da yake ya sha banban da nasu, nasa kyakkyawan larabci ne irin wanda ke cikin Alkur'ani me girma. Su kuma ba da shi suke magana ba, dan haka kalaman nasa suka mata wuryar ganewa, duk da taso ta gane, amma da ta ɗora maganar a mizanin hankali sai ta ƙi yarda da gaskiyar. Shi ko Arman idonsa ya lumshe kawai, domin tun da ya kalli mutumin ƙwaƙwalwarsa ta fara raya masa hakan, amma ta ya ya ke nan? Ta ya mutumin da yake rayuwa a 21st century zai dawo 11th century?... Taya hakan za ta kansace?... “Na san cewa ba lalle wannan maganar ta zauna a kanku ba, domin kuna ganin kamar hakan ba me iyuwa ba ne... To yau ya iyu a kanku, kuma wata ƙila ku zamto ababen misali, domin gagarumin abin da za ku tunkara a gaba!” Dattijo ya sake faɗi. Arman ya buɗe idonsa, sannan ya kalli tsohon. “Ya za'ayi mu koma gida!?” Ita ce kawai tambayar da ta zo ransa, dan bayan ita kuma ba ya jin yana da abin faɗe. Tun da ya furta tambayar Ivana ta gaskata abin da datijjon ya faɗa ɗazu, amma ta yaya su da suke rayuwa a zamanin da dogayen gine-gine suka yawaita a ko ina, da wayoyin hannu, da kafafen sada zumunta, da ababen hawan zamani, da ci gaban technology za su dawo rayuwa a zamanin da babu skyscrapers, babu wayoyin hannu, babu ababen hawan zamani, babu... Babu... Babu, babu komai sai yaƙi da rigima a kan mulki!. Shi ko Adam ko motsi bai kuma ba, ya ƙame ne ƙam yana kallon mutumin, saboda shi yana iya jin kyakkyawan larabcin da dattijon ke yi. “Dogon labari ne, amma zan yi ƙoƙarin gajarce shi, kafin ku koma gida yana da kyau ku san manya manyan masarautu ukun dake mulkin wannan duniya a wannan zamanin!...” Ta farko MAMLAKATUL MAJDAL, Babbar masarauta ce, wadda a zamanin nan sam babu kamarta, masarautar na da girma da yawan al'umma na ban mamaki. Mutanen masarautar na rayuwa cike da farin ciki da kuma samun ci gaba a ko wani lokaci, domin sun yi sa'a da samun adalin sarki da ya dace da mulkarsu. Masarautar na da tattalin arziƙin noma, kiwo da kuma ma'adanan ƙarƙashin ƙasa, kana gari ne da ya zamto cibiyar kasuwanci. MAMLAKATUL MAJDAL tana a ta yammacin saharar Majma, ginin masarautar ya sha banban da sauran masarautu, domin a zamanin za'a iya kiran masarautar da ta zamani. Masarautar na kewaye da ganuwa, wadda aka ginata da duwatsu da kuma taɓo. A batun yaƙi kuwa sun zarce tsara, domin a ƙalla masarautar na da kimanin mayaƙa dubu goma, waɗan da suke a shirya ga mutuwa, ga kuma kayan yaƙi masu firgita abokin gaba. Rayuwa a MAMLAKATUL MAJDAL tana da sauƙi... Masarauta ta biyu ita ce MAMLAKATUL AFSAH, Babbar masarautar Aljannu dake a cikin gajimare, Masarautar tana da kyau da tsarin gine-gine masu ban sha'awa irin nasu na waɗan da suke ba bil adama ba. A fagen yaƙi su ma ba'a barsu a baya ba, domin suna da dakaru da kuma kayan yaƙin tunkarar duk wani abokin gaba idan yaƙi ya taso. Masarauta ta uku kuma ta ƙarshe ita ce MAMLAKATUL JIYAD. Babbar masarautar da a masarautun bil adama ta kasance ta biyu. Masarautar da na kyau da kuma albarkatun ƙasa, sai dai kuma

Table of Contents

Chapters

35 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35