Chapter 3
Chapter 3
Alhadi Group of Companies shi ne babban burin Iƙbal, wato mahaifin Arman. Kuma saboda yana yawan takura masa a kan batun kasuwancin yasa suka fara raba gari. Dan a yanzu Arman ba ya jin yana da maƙiyi sama da kujerar jagorancin gammayar kamfanunuwan Alhadi. Alaƙarsu da su Adam ta samo asali ne tun daga makaranta, abin da ya sa tafiyarsa da su ta yi nisa shi ne su ba su tsangwamarsa dan yana da ƙarancin lafiyar ido. Kuma sam ba sa ɗaukan cewa bai kai ba, dan yana saka glasses ɗin da za su taimaka masa wajen gani, saɓanin yanda ya taso ana nuna masa cewar tun da ba ya gani shi makaho ne. “Na ga kamar sauran awa ɗaya a fara wansa fa!” Adam da ya ci gaba da karanta takardar sanarwar ya faɗa, sai duk su ukun suka dabi juna, kamar wanda suka haɗa baki, haka kowa ya finciki jakarsa suka ruga da gudu zuwa waje, Ivana na faɗin. “Gara mu yi sauri kafin tikitin ya ƙare!” Ai a ɗari suka shige motar Armaan ƙirar Ferrari venon, Adam ya figi motar zuwa Coca-cola Arena, kamar yanda suka yi zato ticket ɗin ya kusa ƙarewa. Dan duk da haka sai da suka bi layin siyan tikitin. Yayin da suke bin layin siyan tikitin, Adam ya shiga bawa Adam labarin film ɗib da ya kala jiya. Shi kuma Arman sai kwasar dariya yake, kamar daga sama ya ji an kira shi da sunan da ya fi masa na mutuwa ɗaci a kunne. “Marhaba makaho! (Hello makaho)” Idonsa ya rintse, dan ko ba'a faɗa ba ya san wa ya mallaki muryar, dan haka ya buɗe idonsa yana gyara glasses ɗinsa, wanna ita ce ɗabi'ar da ya fi yawan yi, ba ya haura minti goma ba tare da ya gyara zamansa glasses ɗinsa ba, ko da ko bai zame ba. Ya juyo yana kallon Faisal tare da wata budurwa tsaye, dariyar da ya ga Faisal ɗin na yi ita ta fi baƙanta masa rai. “Ashe kuma makafi ana ganinku a wurare irin wannan?... Na ɗauka makafi ba sa zuwa kallon live performance!” Ya ƙarashe yana sheƙewa da dariya, budurwa dake tare da shi tana taya shi. “Ka ga malam! Babu wada ya buƙaci jin ra'ayinka a nan, dan haka bama son tada zaune tsaye.” Ivana ta dakatar da shi, dan ko kaɗan Arman ba ya iya tanka masa ko ƙanwarsa Sakina idan suna aibanta shi, idan suka taɓa Gulzar ko mahaifiyarsu ne dai ba ya shiru. “Yi haƙuri malama, ba da ke muke ba, da wannan makahon muke...” Ya yi fasali yana yin taku uku zuwa gaban Arman, sannan ya yi kamar zai rungume shi, ya kai bakinsa saitin kunnensa yana murmushi, sannan ya furta. “Jin daɗi da sharholiya irin wannan ba ta kamaceka ba, ka fi dacewa da yin bara a gefen hanya!” Ya ja baya yana dariya, Ivana ta riƙi kwalar rigarsa a fusace za ta mayar masa da martani, Armaan ya jata baya yana girgiza mata kai. Haka Faisal da budurwasa suka wuce suka barsu a wurin suna dariya. “Da ka bari na mayar masa da martanin da zai hana shi ba ci daren yau. Amma ka hana” Arman ya girgiza mata kai. “Maganganu irin wannan na saba jinsu tun tasowata, ba shi ne mutum na farko da ya fara faɗin hakan ba, dan haka ki share kawai” Ya ƙarshe yana ɗauke kai, cike da damuwa Ivana ta kalli Adam da bai ce komai ba, dan ba zai ce ɗin ba, tsoro ba zai bari yace komai ba, ko shi ya je ya takalo faɗa Ivana da Arman ne ke tare masa, amma ba ya iya taɓuka komai. *House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai.* Motar Armaan ta faka a gaban ƙaramin gidan da bai cika girma ba, amma duk da haka ko daga waje ma yana da kyau. Ivana dake gidan baya na motar ta buɗe ta fita, sannan ta goya jakar guitar ɗinta a baya, ta rufe motar tana kalon Adam da Arman dake gidan gaba. “Me kuka shirya mana zuwa gobe?” Arman da Adam suka dubi juna, sannan Adam ya sake subanta yana girgiza kai. “Babu wani abu, sai dai idan mun haɗu zuwa goben” Ta ɗaga hannunta suka yi fits bump, sannan ta ɗaga musu hannu ta nufi gidansu. Ƙofar shiga gidan ta buɗe, ta shiga, sannan ta rufe ƙofar tana cire takalman dake ƙafarta, ta saka wasu dake aje a bakin ƙofar, sannan ta nufi falon gidan dake a farkon gidan. “Assalamu alaiki ya Yumma!” Ta yi wa mahaifiyarta dake zaune a falo tanq cin fruit sallama, fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma tsohuwar matar na ganinta ta fara murmushi, Ivana ta risina ta sumbaci kan mahaifiyarta, sannan ta zauna kusa da ita tana cire jakar guitar ɗin dake bayanta, tare da ajeta a gefe, ta gyara gashin kanta tana faɗin. “Shu yalli ɗabaktil yaum ya Yumma” (Yumma yau me kika dafa?) Mahaifiyar Ivana me suna Khadija, wadda Ivana da yayarta Hala ke kiranta da Yumma tace. “Shish taouk” “Ba na jin yunwa sosai, dan mun tsaya a Al Fayrooz lounge mun ci abinci tare da su Arman, dan haka ki zuba min kaɗan” “To” Cewar Yumma, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗinsu dake haɗe da falon, dan wata gajerar katanga ce kawai ta raba kitchen ɗin da falon, komai dake cikin falon ba shi da tsada, kuma kayane irin na da, dan a cikin gidan aka haifi Ivana da yayarta Hala, wadda a halin yazu ta yi aure, har da yaronta guda ɗaya. Mahaifinsu ya rasu tun da ƙarancin shekarunsu, hakan ya sa suka taso ba su san shi ba sai Yumma, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma ba su ɗauki rayuwa da zafi ba. Ivana ta miƙa hannu ta ɗauki apple ɗin dake cikin wani bowl a kan center table, tana shirin fara cin apple ɗin idonta ya kai kan wata magazine dake aje a kan center table ɗin. Sai ta aje apple ɗin ta ɗauki magazine ɗin da hannunta na dama, yayin da take saƙala gashinta a bayan kunnenta da hanunta na hagu. Ba komai ya ja hankalinta zuwa kan magazine ɗin ba face hoton dake jikin bangon magazine ɗin. Gani take kamar ta san mutumin cikin hoton, shiru ta ɗan yi tana son tuno inda ta taɓa ganin mutumin. Fuskarsa a yammacin yau ta da ta ganshi ta haska a cikin kanta. Ƙwarai kuwa, shi ne mutumin da ta haɗu da shi a Cavo Espresso Bar, sai ta shiga karanta bangon magazine ɗin. 'Business week' shi ne babban maudu'in abin da magazine ɗin ta ƙunsa. Sai ta zarce zuwa kan sunansa dake gefe guda, Sayyid UWAIS FAZIL... Ta sake kallon fuskarsa tana furta sunan a kan leɓenta. “UWAIS!” Ta furta sunan ba tare da ta ji komai a ranta ba, saboda ɗan adam ba shi da ikon hango abin da ke tunkararsa a gaba, ba shi da masaniyar abubuwan da za su faru da shi, sai na wanda suka riga suka faru da shi. “Ki ci Shish taouk ɗinki” Yumma ta faɗa tana aje mata Shish taouk da ta zuba a cikin plate, Ivana ta aje magazine ɗin tana murmushi, sannan ta kalli Yumma tana ɗaukan plate ɗin,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35