Chapter 9
Chapter 9
shekara biyu saiya dauketa,,cewan yakumbo tana hawaye. Shiru Nasir yayi ganin yadda tsohuwan ta Shiga Wani Hali yace to shikenan,,nan sukayi Mata sallama kowa ya tafi gida.. Nasir da Malam Sai Liman suka tsaya Suna tattaunawa.. Tinda nijlah ta fita da gudu ta Shiga gidan kawayenta tana Kiran su daya Bayan dayan,,bayan sun gama hallara ta fara rawa tana cewa Yau ranar auren nijlah Dan haka kowa ya shirya za'ayi wasa Na kece Raini Yau Yar gidan kaka da Malam zata Hada wasa a dandali.. Yeeeeeeee Yau akwai wasa,,ihu suka sa irin na murna suka sukafara zagaye Dan garin Suna waqa.. *'yan wasa ku fito wasa,Idan baku zoba samarinku suzo Bani Na fadaba angon nijlah ne,,angon nijlah ne me jan baki....* Haka suka riqa waqa Suna wasa Suna Tara jama'a,,cikin lokaci kalilan nijlah da kawayenta suka cika dandali da jama'a" sosai gurin ya cika yakuma kawatar nan fa dandali me kidan kagane yasaki kalanginsa tare da masu kidan kwarya,,masu Kayan saidawa Suma baa barsu Baya ba sun zo.. Kamar yadda akeyi a kowanne biki haka nijlah da kawayenta sukayi Dan sun cika dandali da jama'a anata wasa irin na Fulani,tare da al"Ada irin ta da.. Liman dake tsaye Suna Magana yace,malam kama kida nakeji a dandali" eh Liman Nima haka nakeji Kuma Dai yanzu ba lokacin zuwa dandali bane" Suna cikin haka saiga wasu yammata Suna tafiya,,Malam ne yace ku yara Ina zuwa,, Malam muna wasan bikin nijlah ne,,tafada tana cigaba da tafiya. Cike da mamaki yace Ina ita nijlah,,tana dandali tabasu amsa ,, murmushi Malam yayi Dan yasan nijlah zata aikata Duba da yadda takesan auren,,a Fili yace yaro yaro ne kajifa Liman bikin aure sukeyi a dandali. Eh Ai ta birgeni kaga baza'ayi aure irin Na yaseer da fatima ba,,dariya suka sa,,Liman yace Aiko Yau dandali Ze dauki jama'a Nima baza'a barni Abaya ba.. Tinda suka fita aka zo aka Gaya yakumbo nijlah Na dandali,, murmushi yakumbo tayi ta Rasa inda zatasa Kanta,shin me zatayi farin ciki Ko me.. Ta tabbata Idan tayi baqin ciki ta yiwa Allah butulci Dan haka ta karkata zuwa farin ciki nan itama ta tafi dandali Dan Taya diyar Tata farin ciki.. Bayan tafiyarsu Liman Nasir be bisu dandali ba Dan yace saiyaje ya taho da ango. Sosai ya riqa sauri harya kai Daki,,nan ya Shiga Yana Kiran mashkur,, mashkur dake zaune Yana Hada Kaya zuciyarsa na quna ya dago jajayen idanunsa ya zuba Nasir. Dasauri Nasir ya qarasa kusa dashi ,hannunsa ya riqe yace,, mashkur lafiya naganka haka kama Wanda yayi jinya Na wata guda. Kabari kawai nasir Ina cikin tashin hankali,,ban taba Shiga cikin matsala irin na yanzu ba,,Dana dauki abun da sauqi yanzu Ko magane shayi ruwane,, Nasir adaidai lokacin da aka dauramin aure Sai gashi a lokacin iyayena da 'yan uwana sukesan rabani da wannan gari Nasir yaya zanyi.. Haba mashkur Kamar yaya, meyasa Zaka kayawa mummy wannan aure Bayan kasan halin mummy" cikin faduwar gaba mashkur yace. Ban gayamata ba Nasir kafi kowa sanin yadda mummy take Sona take kaunata,,Na tabbata inda mutuwa zata zo daukana mummy zata Iya fansar Raina da nata" Amma kaga mummy tadau zafi Dani harta Kira manyan yayyena ta gayamusu.. Nasir Bani da yadda zanyi,,yazama Dole a Yau Dinan nabar garin nan indai inasan zaman lafiya. What! Mashkur me kake nufi,,yaya zakayi da nijlah?? Nasir Zan dauki matata,da ita Zan tafi,,Iya wuya Ina tare da ita.. Niko Nace Kamar yadda muke Kenan lolxx.... Kudaure kuna sharing labarinan, Domin wasu su amfana. Comments & share. *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *N@DI@* 1⃣5⃣&1⃣6⃣ Wayyo Allah,,yau Naga ta kaina yanzu mezan Gaya iyayen yarinyarnan,,zagaye titi Bello ya riqayi Yana kallan Motan har Saida suka bacewa ganinsa kafin ya daga qafa yaname danasanin amincewa da rakiyan nijlah.. Yanzu mezan Gaya Kaka,,wanne dalili nake dashi Wanda ze tabbatar musu da maganata gaskiya ce,,sosai ya zurfafa cikin tunani Yana tafiya Yana hada hanya a haka harya Kai kauyen kankan,Yana zuwa dakin Nasir ya Shiga nan ya Samu Nasir ya zuba tagumi Yana tinanin rayuwar kadaicin dazeyi a wannan kauye Shi Daya ba abokinsa.. Ko sallama Bello beba yafara da masifa,,Kai Ashe wannan abokin naka bashida kunya,,miskilancin banza yakewa mutane"" dagowa Nasir yayi Yana kallan Bello da jajayen idanunsa yace" lafiya Bello,,Naganka anan? To a ina zaka ganni Saida muka Shiga mota abokinka ya hankadoni waje,,yace wai ba inda Zan bishi daga Shi sai matarsa zasu tafi,,yanzu me kake tsammanin yakumbo ya dauka,,ni wallahi harna Fara tinanin mashkur Dan yankan Kaine.. Tinda Bello yafara magana Nasir yake dariya harya Kai Aya Nasir be dena dariya ba yanayi Yana kallan Bello,,haushine yakama Bello nan ya Fara hararan Nasir Yana cewa,,Ara ta kanni indai Yanke Kan nijlah zakuyi kaima bamu barinka Ka fita lafiya a wannan kauye.. Nasir be kulaba Saida yagama dariya kafin ya kama hannun Bello Yana cewa,, cool down abokina,,kaga niban iya yaran arna ba,,idan zaka gayamin da Hausa ko fulatanci Ka gayamin.. To shikenan zauna muyi magana,,wacce magana zamuyi alhalin an tafi da nijlah bamusan inda suke ba,,yanzu idan kaima kabi dare Ka gudu ina muka kama.. Haba Bello Ka kwantar da hankalinka nagayama babu wata matsala,,kuma ninasan abinda yasa mashkur yayi haka,,yanzu idan Kaine Ka tafi kiwan shanu sai Ka dawo gida da Mata,,wanne dalili zaka Gaya iyayenka" shiru Bello yayi Yana nazari kafin yace,,Zan gayamusu tsintota nayi a hanya,,to kagani kaima karya zaka Gaya iyayenka,,to tayaya kake tinanin mashkur ze tafi dakai ga kuma nijlah Wanda ya aure batare da Sanin iyayensa ko danginsaba.. Shiyasa akace yabarta anan yafara zuwa ya sanar da iyayensa kafin yakai musu ita,,yanzu ya zeyi Kenan,,Nima bansani ba cewan Nasir Yana qara cigaba da magana.. Inaga wani tinani yayi shiyasa yace Ka dawo shize tafi da nijlah,,Dan haka nakeso kace Kaine kafasa zuwa birni kace su tafi kawai sabida gani kuna ganina,,duk ranar dazan tafi saimu rankaya daku kuje can birni Kuga inda nijlah take,,koya kake gani za'ayi?? Amma Nasir tayaya kake tinanin yakumbo da Malam zasu yadda da wannan karyan,,zasu yadda sai kaqara da cewa dare ne yayi Baku samu mota ba,,dakyar aka samu guda shima gurin mutum dayane,,shine mashkur ya zauna ya Dora nijlah akan cinyensa suka tafi.. Eh to gwara wannan shawaran Amma bazan fita a dakin nan ba sai dare,,hakan yayi,,nan dai suka cigaba da tattaunawa Nasir Yana qara kwamtarwa sa Bello hankali....... ************* Karfe 1 na Rana a garin Kano yama aunty lateefah,tinda ta Shiga gidan tafara Kiran mummy,,duk ta inda tabi ma'aikatane ke gaisheta sedai ba Wanda ta amsa tana tafiya tana Kiran mummy harta isa dakinta.. Kwance ta Sami mummy ta zuba tagumi tana Kiran layin mashkur,,mummy na ganin lateefah tayi cilli da wayan tana cewa,, shikenan mashkur,, shikenan tinda bayana kakesan gani,,da gudu lateefah ta qarasa kusa da mummy tana tambayanta? Mummy meya faru da mashkur menene kuma,,ko haryanzu be dawo gida ba? Ina ze dawo lateefah yafiso saina mutu ze dawo gidannan,, wannan wanne irin karatu yarannan take da Har yazabi bacin raina.. Hannu ladeefah tasa tana gogewa mummy hawaye,,kiyi hakuri Mummy kina kallo nabar aikina Na dawo Nigeria sabida abinda yarannan ya aikata,,duk Da yace Ke Kika amince Amma banji dadin yadda Kika Tashi Hankalinki ba,mummy
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46