Chapter 22
Chapter 22
na tabbata babu abinda ze sameta indai tana tare Dani... Dakata haka mashkur kaida Yasmeen kunyi hannun riga,,niba wannan bayanin na tambayekaba,,kazo nan da minti 5 kafin na fita.. Abba be ajiye wayan ba Yasmeen ta riqe qafafunsa tana kuka,,Abba inasan shi,,bazan iya rayuwa babu shiba,,Abba Dan Allah ka chanza wannan hukuncin yayi masa tsauri... Murmushi mama tayi tana kallan Yasmeen sedai bata iya magana ba ta tashi tabarsu a falon... *Kwana biyu kunjini shiru,,kada ku dauka Jan ajiyene,,hakan yafaru sakamakon samun matsalar wayana,,Wanda har yanzu bata gama zama daidai ba*.. Yawan comment yawan typing. *Momn sultan ce* 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *WASILA....* 3⃣3⃣&3⃣4⃣ Mama na shiga daki ta zauna saman bed tana murmushi.. Da gudu Yasmeen ta shigo ta fada kan mama tana kuka.. Mama dan Allah kigaya Abba kada yafasa aurena,, wallahi mama inasanshi,,zamu shiga wani hali idan har bama tare.. Cike da takaici mama take kallanta sai kuma ta ture ta tana cewa,,ke dai anyi sakarya,mara wayo keda nake gayamiki gaskiya kina toshe kunne,,sai yanzu da kika gama harzuqa abban Baki shine Zaki kawomin Kara,,toki tashi kibani guri ban iyawa.. Kije gurinsa kusan yadda zakuyi,,naga dai kunfi kusa.. Cikin kuka Yasmeen tace Allah mama Abba yadauka zafi akan mashkur kuma ba haka yakamata yayi ba.. To ai saiki gayamasa yadda zeyi kafin mashkur yazo labari yasha babban,tinda yagayamiki baze iya sakin matarsa ba. Ni Allah seya saketa tinda ba itace zabinshi ba,to ai shikenan ga gurinann daga haka mama ta fita a dakin tabar yasmeen.. Daki Abba ya shiga yana zagaye dakin tare da cije labe,,waini zaa wulaqantawa yarinya,, yarinyar da tintini samari 'ya 'yan manya ke bibiyar aurenta Amma taqi ta nacewa wannan yaran,,gashi yanzu abinda ya sakamana dashi,,sosai Abba ya shiga cikin tinani har besan lokacin da Yasmeen ta shigo dakin ba.. Kusa da Abba ta tsaya tana kallansa,,kafin tayi qarfin halin cewa.. Abba kayi hakuri ninasan ba laifin mashkur bane,,laifin iyayen yarinyarne,,kaga sadaka suka bashi ita Kuma Abba aiba fasa aurenmu zaayi ba,,sedai Kawai ya saki wannan 'yar masu yawan jejen.. Hakane Yasmeen Abba baki tinanin nan gaba ya dawo da matarsa,,Kuma fa kinsan yadda matar fari ke shiga ran namiji.. Murmushi Yasmeen tayi tana kallan Abba Sai Kuma tace,,hakane Abba amma ba irin wannan matan ke shiga ran miji ba,,Abba idan ka duba nijlah sadakace agurinsa ba auren soyayya akayi ba,nidai fatana roqon danake abba ka bishi a hankali kaga yadda ka dagamasa hankali dazu.. Zaro ido Abba yayi Yana kallan Yasmeen kafin yace,,ke har tausaya mar kike,,yaran da yaci amanarki.. Hakane abba sedai haryanzu banji chanji a soyayyar danake masa ba,,maimakon naji haka saima qara Sansa da tausayin halin dayake ciki n.. Doke bakin Yasmeen Abba yayi tare da nuna mata qofa,,magana take Shirin Yi Abba ya daka mata tsawa.. Fita nace,,ki fita kafin naci gidanku,,haka ,zaayi auren kije yana juyaki kamar yadda ze juya yar sadakan daya dauko,,nasan zeyi tinanin duk daya kuke.. Da gudu Yasmeen ta fito a dakin Abba tana me danasanin nuna baqin cikinta akan auren nijlah,,sedai tana fitowa suka kusa cin karo da mashkur Wanda ke tsaye jikin falon yana kwada sallama.. Jikinsa taso fadawa yayi saurin yin baya,,nan ta zube a qasa ta saki saban kuka.. Da sauri Abba ya fito yana cewa lafiya,,ganin mashkur yakasa qarasa abinda ze fada ya zuba masa ido.. Kai me kayimata? Bakin mashkur na rawa yace Abba faduwa tayi' shine kana kallo baka taremin yarinyarba ta fadi qasa,,kodan kada da asara.. Ba haka bane abba,,naso yin haka kuma ta qoce,,Kai meya hanaka gocewa ka tare ta.. Mamace ta fito tana girgiza Kai,,dai kuma tace sannu da zuwa mashkur,,har qasa Mashkur ya zube yana gaida mama yayinda yasmeen ta cika da mamakin qin tareta da mashkur yayi.. Seda mama ta amsa kafin tace Bismillah ka shiga ciki. Jiki ba kwari mashkur ya qarasa cikin falon yana addua acan cikin zuciyarsa.. Bayan kowa ya zauna Abba ya kalli mashkur ransa a bace yace,, yanzu Kai abinda kayiwa yar lele kayi daidai kenan,,koka Manta lokacin da kake zuwa safe da rana kai har dare zuwa kake gidannan kana 'yarmurya,,Seda kasu soyayyar ta zaka watsamana kasa a ido kaje can wata ruga ka aure Yan matsiyata kace zaka hadasu Kishi da diyar Dana Haifa?? Ita Dai mama shiru tayi Dan da so samune ita daki zata koma suyi yadda sukeso,sedai bata da damaryin haka,Dan haka ta zuba ido da kunne tana sauraransu.. Seda Abba yakai aya kafin mashkur yafara Magana cike da fargaba da tashin hankali.. Abba nasan nayi laifi sedai ina me Neman afuwa,,ayi hakuri a dauka uzurina. Wanne uzuri gareka kaida ka,, dasauri mama tace.. Alhaji hakurin Dai zaayi. To shikenan na hakura amma ya sani aure Babu Shi.. Raurau Yasmeen tayi da ido tana kallan abba,, mashkur ko kasa Magana yayi Banda addua Babu abinda yake.. Ganin Abba yayi shiru yasa mashkur Dan risinawa yace,,Abba nagode sosai hukuncin daka yanke yama tsauri ka sassauta ko yasmeen.. Kama qadan garuwa haka Yasmeen ta shiga daga kai tana zubda hawaye.. Seda Abba yagama ciwa mashkur mutumci da fada San ransa kafin ya nuna ya hakura.. Sharuda iri iri Abba ya gindayawa mashkur amma duk da haka mashkur yace yaji ya gani,,Shi burinsa Kawai ya samu nutsuwa ta bangaren Yasmeen Sai yaji Dana mummy da sauran Yan uwansa.. Tashi kace amma kasani badan kai nayi haka ba sedai yar lele Naga ta nace akan soyayyarka saikace kai kafi kowa iya soyayya kana tafiya Sumi Sumi dakai.. Godiya mashkur yayi yayiwa mama sallama,,sabida kunya dakyar mama ta iya amsashi,,ta Kuma tabbata Yana yiwa Yasmeen soyayya ta gaskiya danda wanine da tini yabarta koda itace autar Mata.. Duk da mashkur beji dadin yadda Abba yamasa ba sedai be nuna yasmeen a fuska ba dan haka ya fita a gidan cikin sauri.. Yana fita mama ta Kalli Abba Ranta a mugun bace tace.. Gaskiya Alhaji baka kyautaba,, wannan fa surukinkane nan da sati uku amma ka tsaya kana yimasa irin wannan Abu duk akan yarka,, wannan wacce irin wayewa gareka,,to wallahi ka sani wannan abun dakayi ba qima ka siyamana ba,, mutunchi Kawai ka zubar mana a idan Duniya,,ke Kuma ki shiga hankali mara kunyar banza da wufi,,kinsan Kina San nashi kika Bada dama mahaifinki ya wulaqantashi.. Kuma Yasmeen tasa tana kallan abbanta.. Cikin fada Abba yace ke wannan abun da kikayi daidaine,,ina mijinki kina dagamin murya.. Tabe baki mama tayi tace daga gayar gaskiya Sai cibi yazama Qari.. Ke Naga alama sabida takuran da kikema 'yar lele shiyasa takeso ayi auren nan itama ta huta,,kina Abu kama bake kika haifetaba.. Fita mama tayi adakin yayinda Yasmeen tabi Bayan ta,, Yasmeen Na fita ta shiga dakinta,,waya ta dauka ta Kira mashkur.. Bugu daya ana biyu ya dauka.. Ko sallamarta be iya amsawa ba yace,,kin kyauta da kika bari aka yimin irin wannan tarban a gidanku,,Yasmeen nayi tinanin tallafi rayuwa a lokacin da yan uwana suka sani gaba,,sai gashi kema kinyi fiye da abinda sukamin.. Cikin yauqi Yasmeen tace,,haba baby ai duk kaika ja,,kasan yadda na tsani kishiya sai gashi kayimin ita tinkafin na shigo cikin gidanka kuma daka tashi yin auren sai auri abu mafi tsana a cikin zuciyana,,ta Yaya kake tsammanin hankalina baze
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46