Skip to content

Chapter 2

Chapter 2

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,269 words 0 views Progress saved
Download Book

tasa tana cewa shikenan yanzu na rasa aishi nijlah ma bazan samu Zama da itaba,,hakuri mijin ya riqa bata Dan yaga alaman yakumbo bata da niyyan bada nijlah.. Tin bayan rasuwar iyayen nijlah yakumbo ta tattara komai nata da Soyayya ta maidashi Kan nijlah,,itace sirfe,dakau,Kai Harma da wanki yi take sabida Kula da nijlah,da sai Mata madara,,sedai duk da haka watarana bata samun kudin sai Mata madara,,haka ta riqa bin shanu tana matso nono me dumi tana Bama nijlah.. Akwana a tashi har nijlah ta Fara girma tana qara wayo,,kowa ya kalla nijlah saiya tausaya Mata,,Dan kowa yakanzo dandali ya sai Abu Banda nijlah danko biyar bata samu,,haka zata dawo gida tasa yakumbo gaba tana kuka tana birginia,,wata Rana sai dai yakumbo itama tasa kuka suyi tare.. Malam bashida karfi balle ya riqa aiki Yana Nemo kudin Kula dasu,, gashi kawu Shi kadaine dansa kuma Allah yamasa rasuwa.. Sosai abubuwa suka rinchabemusu,Abu Daya ke taimakonsu shine wadatar zuci da godiyan Allah. Al'adan wannan fulani shine auran da yara kanana,duk yarinyar data haura shekara sha 3 tayi da yawa,,shiyasa malam yake Allah Allah nijlah ta Kai shekara 13 ya auran da ita... ************** Mummy Dan Allah ki janye wannan matakin da kika Dora,,wallahi bazan iya tafiya da Yasmeen wannan kauyen ba,, Mashkur Kenan kana tinanin Zan Bari Ka tafi service ba aure,,gashi amsa bikinnan, na kuma tabbata idan akace saika dawo dole a daga biki,,ni kuma abinda banaso Kenan. To Amma mummy shikenan saina kama da tafiya da Yasmeen bayan kinsanta da kyankyami,,salan muje da ita ta kasa cin abinci,,Azo arasa mafita,,koma dai menene kaje kasan yadda zakayi,ko a daura aurenka Ku tafi ko kuma Ka fasa zuwa service.. Eyyah mummy nah, shikenan nayi karatu abanza,, mummy kiji tausayina,, Turesa mummy tayi tana masa Wani irin duka,,kafin tafara Magana cikin fada,, mashkur narasa meyasa bakasan ayi maganan aure Sai anyi magana kace Baka shirya aure yanzu ba,, mashkur ka Duba arziqin da Allah ya bamu,ka Kalli gidannan Na tabbata munada kudinda zamu aura Maka Mata Dari Idan anayi,,toka gayamin menene Shirin Naka.. Shiru yayi Yana sauraranta sedai yakasa cewa Koma,,jiyake ajikinsa Baya buqatar auren yanzu sedai ya Rasa ta hanyar daze sanar da mahaifan nasa.. Kai dubani mashkur bafa kai daya ka Iya miskilanci ba,,da sainayi Magana kasani gaba kana kallo, Idan Yasmeen ce bakaso kaduba yara Yan Mata gasunan 'ya'yan masu kudi irinka, saika aura Baka tsaya kana batamana lokaci ba,, Shiru mashkur yayi nan ma be Iya Magana ba.. Kai mashkur mummy ta daka masa duka a cinya"kaga Idan bakada lafiyane ka gayamana.. Wannan Karan haushi tambayan Mummy ta bashi Dan haka ya turo Baki kama mace Yana kallanta"" eh mana Naga da anyi maganan aure kake hade giran Sama Dana qasa,,ko wani ne yace kafara soyayya da Yasmeen.. Mummy Nima abinda nagani kenan,ni mace inasanta sedai banshirya aure yanzu ba,,to mummy ba sekumin hakuri ba zuwa lokacin Dana shirya,,Amma kunqi,,sai dagamin hankali kuke,,to wallahi akayi Wasa saina fasa aurenta kowama ya huta.. Riqe Baki mummy tayi tana sauraran Dan autan nata,, Cigaba da magana yayi, ahankali Yana qara kwantar da kansa jikin mummy,, mummy Dan Allah ki amince nayi tafiyan nan,kinga Dana dawo sai ayi auren hankalinki ya kwanta... To amma,,hannu yasa ya rufe bakin mummy cikin Wasa yace,,addu'a kawai zakimin kinji sweet mom.. Anya ko mashkur zaka girma yanzu ni kake dannewa haka Hadda rufemin Baki,,eyyah mummy duk wannan girman nawa.. To ai Naga zaka....kash mummy Naga dai barewama da danta take Wasa a dawa.. Nan dai yayita bata Baki harta hakuri da niyyan Daya dawo za'a daura auren.. Yau ya kama Monday kuma yaune mashkur ze tafi kauyen kankan Dan yin service,,tin asuba yake shiri har dai yaga.. Karfe 10 daidai ya fito get mummy riqe da yar akwatinsa tana ja,, drive ne ya amsa da sauri yasa a mota yayinda mashkur ya rungume mummy.. Mummy zanyi missing dinki,,nida zaki yadda tare zamu wuce,, murmushi Mummy tayi irin na manta tana shafa kansa tace,,Aida Yasmeen Ka dauka zaifi sauqi Dan gaskiya ni banasan Zama cikin Fulani,sabida kasan banison nono. Shikenan mummy nizan wuce sabida mu 3 aka tura can,nasan sauran suna jirana,kafin ya rufe Baki wayanshi yafara ringing. *Comment & share,na rasa meyasa bakusan sharing dakun karanta saiku barshi a watanku,,pls ku riqa turawa wasu group's kodan jamaa su amfana* *Comment ne kadai zesa nacigaba da typing,kunsani ina iya 3 page a Rana,kuma kuke sani hakan* *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN FAREESAH* 1⃣&2⃣ Amsa Kiran mashkur yayi,,kafin yayi Magana Nasir yace,,abokina muke jira kaga lokaci Baya jira,, murmushi mashkur yayi Yana Kallan mummy.. Shikenan Nasir karka damu gani a hanya,kabani 5 minutes Zan qaraso,, shikenan Ina jiranka cewan Nasir Yana kashe wayan.. Murmushi abbakar yayi Yana cewa Ai nasan mummy bazata Bari ya fito da wuri ba,,Dan Dama da kyar ta Bari zeje wannan kauyen"Ni wallahi ta birgeni data nuna bataso Duk be yadda da Hakan ba mansur ya fada Rai bace. Inama inama,,Kai nifa naso Nike da wannan gatan irin na mashkur da ko zaman Nigeria baniyi, dariya suka sa daidai lokacin da mashkur yazo. Drive ne ya Bude masa qofa nan ya fito cikin takunsa na qasaita,, Ido suka zuba masa suna kallo,,shiko murmushi yayi ya qarasa kusa da Nasir tare da miqa masa hannu,,Daya bayan Daya suka riqa gaisawa da abokan nasa. Gaskiya abokina Baka dace da zaman kauye ba,,kauyen ma wai Fulani,,Tabe Baki mashkur yayi tare kallan nasir,,Nasir Ka kirani gashi nazo banga alamun tafiya ba. Karka damu yanzu zamu wuce drive ya kusa zuwa,, mashkur be qara magana ba,suka cigaba da hira batare daya sa musu Baki ba. Bala,zaka iya tafiya,, dasauri Bala drive yace, ah ah ranka ya Dade hajiya tabani umarni Karna sake na tafi har sainaga tafiyanka,, girgiza Kai yayi Yana me Jin dadin yadda mummy ke Kula dashi fiye da yadda ta damu da kanta,, Karka damu kawai kaje Ka gayamata mun wuci,,kayi hakuri ranka ya dade bazan iya tsallake umarnin hajiya ba.. Seka ta Zama Dan wahala cewan Nasir Yana hararan Bala,, Ba'afi 2 minutes ba sai ga lafiyayyan mota ya faka a gabansu, Basu bata lokaci ba gurin Shiga,nan drive yaja suka Fara tafiya sai kankan Fulani.. Garin kankan.. Karfe uku dai suka safka cikin kauyen dabe wuci a qirga gidajen ba,,suna zuwa aka kaisu gidan me gari,,hannu biyu me gari ya amshesu tare da yi musu sauka ta musamman,, Fura da nono aka Basu sai kankana da aka jere kusa dasu,daga gefe dabino aka kawo cike da kwarya sai warar Fulani,Wanda akeyinta kama awara saidai ita da nono akeyi ake soyata kama awara. Nan da nan guri ya cika da kamshi ,,mashkur ne ya saurin dago Ido Jin kamshin dabe taba Jin irinsaba adukkan abincin dasuke ci,,saliva ne ya cika masa Baki,nan da nan ya hadiye Yana Yana tandar Baki.. Guri aka Basu Don su ci abinda suke so,,nan fa yara kauye suka zagaye motansu suna shafawa tare da yimusu zane,, Da gudu wata yar karamar yarinya tazo tana zana photon saniya a cewarta saniyar yakumbo ce,,nan yara suka riqa tsalle suna murna, mashkur da abokansa Basu San aika aikan da yara ke musu ba,wara kawai sukeci suna

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46