Skip to content

Chapter 26

Chapter 26

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
Download Book

Mata jikin dayayi,,sedai bata da damar gayar hakan sabida tinawa da Jan kunnan daya Mata.. Jin shirun yayi tawa yasa daddy cewa" kinyi Shiru yarinya muna sauraranki.. Mashkur Kam Banda faduwar gaba babu abinda yake ji, so yake ta dago Kai su hada Ido koya Samu damar Tina Mata gargadinsa ita kuma taqi dagowa Saima qara yin qasa dakai take.. Ahankali nijlah ta bude baki jikinta da bakinta Kai komai ma na jikinta rawa yake tace" Acan din Zan zauna nijlah ta fada cike da tsoro.. Tsaye mummy ta tashi tana cewa" Wallahi Baki isaba,,kujimin shegiyar yarinya,, "yar mitsitsiya dake kin iya gulma da kini Bibi" To anan zaki zauna kinji na gayamiki,, nijlah na karkarwa tace to.. Kallan daddy mashkur yayi daddy ya shafa kanshi Yana cewa Ka kwanta da hankalinka auta,,can din data zaba anan zaki sauna kaji.. Sabida dadi har besan lokacin da murmushi ya subuce masa ba ,,kasa yayi da Kai Yana cewa,,daddy mun gode Allah yaqara girma.. Tashi kuce daddy yafada abinsa. Haukane kawai mummy batayi ba,,taso dukan nijlah sedai bazata iya saka hannunta jikin wannan kazamarba,,tana ji tana gani haka suka fita a falon... Har mota Mashkur ya kaita Yana murmushi,,bayan ya bude mata kofa ta Shiga a zaga ta inda take yayi kissing bakinta Yana cewa"haka nakeso ki Zama mejin magana kinji amaryata"" yanzu dai ki jirani ina zuwa 2 minutes kawai ya ISA.. Yana tafiya nijlah ta Tabe Baki tana cewa ko menene kuma 2 munat oho masa,,shiyasa yasani tafada tana kwantar da kanta jikin kujeran.. Falon mashkur ya koma ya je daf da mummy ya riqe hannunta,,fizgewa tayi tana hararansa,, murmushi yayi Yana cewa haba sweet mom,,kinfasan banasan bacin ranki,,Dan Allah mummy ki saki ranki,,kiso nijlah kamar Yadda kike Sona.. Ka rufemin Baki auta,,kana da kunya kuwa" rufe Ido yayi Yana cewa mummy anjima Zan dawo kinga diyarki tana Kiran waya,, yafada Yana Nuna Mata wayar data fara ringing a hannunsa.. Tuni number Yasmeen ta bayyana,, murmushi mummy tayi tana cewa idan kaje Ka gaisheta. To yace ta tashi yana dariya,,abinda mummy bata sani ba kuwa,,shiya tura Yasmeen text massage yace ta kirashi.. Yana zuwa ya Samu nijlah harta fara bacci bayan ya tada mota ya dauka wayar,, A kunne ya Kara Yana cewa" hello baby.. Uhmn uhmn wai haryanzu Baka zoba inata jiranka" bayan kasan na Gama hada lefen gani kawai zaka zo kayi,,abinda be makaba sai a chanza.. Murmushi yayi me sauti Yana cewa" nasan baby na ta iya Zabe,,karki wani damu nasan kayan sunyi kyau.. Kuka Yasmeen taka tana masa shagwaba,,nan da nan yaji babu abinda yakeso sai ganinta,,tini ya karya akalar motar ta dawo daga hanyar saban gida suwa gidansu Yasmeen... To to shikenan ki kwantar da hankalinki ina hanya yanzu haka.. Wani tsalle Yasmeen tayi ta katse Kiran tana fadawa cinyar mama.. Seda Mashkur yayi nisa a hanyas ta zuwa gurin yasmeen ya Tina da nijlah dake kwance bacci me nauyi yafara daukanta,,yazo juyawa Amma baze iya ba Dan haka ya tafi da ita a cikin motan.... Comment & share *Momn sultan ce ✍ ✍✍* 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *SIS NAJA'ART.....* 3⃣9⃣&4⃣0⃣ Tafiya yake Yana Jin farin ciki da annashuwa na qara ziyartar zuciyarsa" tin Yana tafiya anhankali har yaga tafiya bata sauri" gudu ya saki tare da kunna waqar soyayya dadi,,tini ta hade cikin motar da sauti me dadin gaske.. Tafiya yake Yana jinjiga,,kallo daya zaka masa kagane Yana cikin farin ciki.. A Dan firgice nijlah ta Farka sabida Jin iska me zafi tafara kadawa ga qaran kidan dake tashi.. Hannu daya yasa ya tare da,,dayan Yana tuqi dashi,, fuskanshi dauke da murmushi yafara shafa fuskanta Yana cewa" Keda wa Naga kintashi a firgice" langwabewa tayi a jikinsa taqi tankasa" kodai azumin magana kika dauka,,nan ma nijlah batayi magana sema kwantar da kanta jikin kujeran mota tayi tana lumshe ido.. Uhmn" kema kin iya muskilanci ko,,turo Dan qaramin bakinta tayi tana girgiza masa Kai.. To meya tasheki adaidai wannan kuma,,har kina firgita? Ahankali nijlah tace" Nima bansani ba.. Shikenan kirinqa addau idan zaki kwanta bacci" Cike da sanyin jiki irin na Wanda ya tashi a bacci tace" Aiba da dare bane,,kuma indai Zan kwanta da dare inayi,,kakama tana tofamin.. Waya gayamiki a bacci dare kawai Ake addu'a? Shiru tayi Dan ba Wanda ya gayamata,,Niko nace wasu manyan ma basa addua lokacin baccin rana,yakuma kamata mu gyara,,sabida addu'a tana taimaka mana gurin kariya daga sharrin shaidan,,katangar qarfece ga duk wani musulmi... Kinyi Shiru? Nima bansani ba,,to shikenan saiki kiyaye,,kinga dai abinda yafaru yanzu.. To nijlah tace tana qoqarin komawa vaccinta. Kingama munzo inda nakesan zuwa" ki zauna a mota nizan Shiga nan gidan yafada Yana Nuna get gidansu Yasmeen.. A hankali ta daga Kai tana kallan gidan gabanta na faduwa tace" kado nan kuma inane waiku Dama a birni kowa gidansa haka yake da ciyawa" kaga Dana zo da saniyana Aida ta Samu abinci,,ba ruwanmu da kaita jeje kiwo ko??? Hararanta yayi Yana cewa" zaki fara shirmen naki ko,,waya gayamiki abincin dabobine? To menene Shi,,gashinan wani ya girma wani kanana a qasa,,sai ruwan banza Ake bashi tinda bashi da amfani.. Inji waye ta tambayeta Yana tsareta da Ido.. Gashinan na gani.. To wannan Bana saniya bane,,ado akeyi dashi anan bakuma nasan yawan surutu kinji nagayamiki.. Hannu tasa ta rufe Baki tana girgiza Kai alamar ta dena.. Daga haka yafara qoqarin Kiran Yasmeen a waya.. Yasmeen na kwance a cinyar mama tana zubamata shagwaba wayanta yafara ringing dasauri ta daga mama ta vita da kallo.. Hello baby gani na iso" oyoyo ta fada tana kallan mama" Ganin zuwa' No kibarshi Zan shigo da kaina kedai kawai ki budemin qofar Baya" Ni dai ah ah,,Allah nizan shigo dakai tafada tana katse Kiran. Gefensa ya duba yaga Yadda nijlah ta hade qiran Sama Dana qasa tare da turo Baki gaba.. Gabansa yaji yayi mugun faduwa da kyar ya iya magana cikin sanyin murya yace" Ke kuma me aka Miki zaki bata fuska ko duk baccin ne" Kama zatayi kuka tace" ba Kai bane. Zafi Ido Mashkur yayi Yana kallanta,, Nikuma me nayi Naga kece me laifi Amma zaki doramin kodan kinga bamu qarasa gida na hukuntaki ba,shiyasa zakimin rigima? Turo Baki nijlah tayi tana Jin bacin Rai tare da kishi me zafi tace.. Kuma shikenan saika kawoni nan kana waya da wata qatuwa. Mamakine ya cika mashkur cikin zuciyarsa yace na Shiga uku kaddai ace yarinyar nan kishina take" a fili ko cewa yayi ke wai harkinsan wani Abu kishi? Koda bansani ba ai bazakayi waya da wata a gabana ba.nijlah ta fada tana murguda Baki. Rasa Yadda zeyi da ita yayi gashi Yasmeen taqi Yadda ya Shiga ciki,,yasani idan yaqi tsayawa su Shiga tare baza'a Samu hiran arziqiba ta riqa yimasa Mita kenan,,to idan kuma ta fito taga nijlah fa,,Yaya zanyi ya tambaya kansa.. Sai yanzu yake Dana sanin zuwa da nijlah be Ida zancen zuci ba yaji nijlah Na cewa" Kaga Ni Idan bazaka kaini gidaba saika budemin nayi wasa acan tafada tana nuna jikin wasu fulawa.. Tsawa ya daka Mata Yana cewa waini sa'ankine zaki riqa magana Dani Yadda kikeso? Dasauri nijlah tace nadena.. Bangaren Yasmeen ko da sauri ta koma daki ta

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46