Chapter 8
Chapter 8
taqi nuna damuwanta akai bayan Ka dagamata hankali muma Ka dagamana''cikin sanyin jiki da tinanin irin tashin hankalin daze tarar a gida yace shikenan aunty..kit ta katse Kiran tanajan dogon tsaki tare da cewa yaro besan komai ba sai bin talakawa kaskantantu wulaqantantu wadanda Basu San komai ba sai yawo a jeji da shanaye.. Tinda mashkur ya Gama waya ya zauna a gindin bishiyar dafe da kansa Yana ji kama ze fado qasa sabida sarawan dayake masa" dakyar ya iya daga qafafunsa yafara tafiya Yana hada hanya harya Kai dakinsu" Kan katifanshi ya kwanta hannunsa dafe da kansa yanajin zuciyarsa na azalzalasa akan abubuwa da dama,,rintse idonsa yayi yanasan bacci ya daukeshi sedai abin ya gagara Dan a yadda yakeji bacci baze taba daukansa duk kuwa da irin sunan dayayi gurin satar mutane,,runtse Ido yayi Yana hango kyankyawar fuskar nijlah,, qirjinta yake hanqe yaga Babu komai a jikinta danko qirgan danqi Bata fara ba,,sedai nijlah akwai iyaye dasan ado da kwalliya Duk da Bata da kayan kirki Amma kullum saita chanza Koda Bata samu sabulun wanki ba,,sosai ya zurfafa cikin tinanin yarinyar tare da yaban halayenta,,abu daya yakeji tare da ita shine rigima,,yasani Idan tafara rigima bataji Bata gani saita kwana tana kuka" oh Allah ya fada a Fili,,yanzu Idan nijlah tafara wannan kukan yaya zeyi da ita,,wanne irin mataki mummy zata dauka akansu gaba daya,,Rasa amsa dayayine yasashi saurin Tashi ya fita. Alwala ya daura nan ya dawo Daki ya shinfida Sallaya.. Sallah yayi Har raka'a biyu nan ya dungura kanshi a qasa Yana neman dauki a gurin Allah.. Bayan an fidda Alhaji ya'u,,Liman yafara Magana kama haka" Malam inaga yakamata mu qarasa gida Domin ayiwa yakumbo bayanin abinda Ke faruwa tare da gayamata wannan aurin aure.. Hakane Liman sedai Ina tsoran yadda yakumbo zata riski wannan labari,,bansan yadda zata dauki rabuwa da nijlah ba,,Malam yaqare maganar da cikin kuka Wanda baza'a kirashi Na bakin ciki ba,,Sai Dai Ko farin ciki.. Haba Malam yaya da kuka,kaida zakayi farin ciki gashi yarinya tayi dacen Miji bame San hayaniya ba.. Kwarai dagaske cewan Nasir,, Ai Liman Idan kaga mashkur yayi Magana to ba qaramin Abu akeyi ba,,bashida San hayaniya,wallahi tinda muka taso da mashkur bantaba ganin abokin fadan Saba kowa yabansa yake,,shiyasa nazabawa nijlah Shi Duk da nasan wasu zasuyi tambaya Shin Ni meya hanani aurenta nasa abokina yayi? Nan mutane sukafara surutu Suna fito da tambayan dankuwa sunga lokacin da Nasir Ke gayawa mashkur yazo ya taimaki nijlah" wasu nacewa shimeya hanashi taimakonta indai Dan Allah take.. Kuyi hakuri yanzu Zan Baku amsar tambayoyinku" wallahi Ni Nasir Zan Iya auren nijlah Duk da Babu shaguwa tsakanina da ita Kamar yadda ta Shaqu Na mashkur,,sedai banqi amsar aurenta sabida komai ba sedai, Ni inada zafi Bani da rigima sannan abu kadan Ke batamin Rai nayita jibgar yara,,Idan Ko sa'anane Daga lokacin Ina Iya Dena abota dashi.. Nan ya numfasa yace mashkur kadai Ke Iya Zama Dani sabida miskilanci irin nashi da hakuri Wanda Koda nayi Abu sedai yace Allah ya shiryeka koya girgiza kai,,Idan Ko fada Na tsokalo shike Bada hakuri Har adawo daidai. Natabbata wannan dalili nawa ya isa kugane nijlah ba sa'ar aurena bace Duba da yanayin rigimarta ta Babu gaira Babu dalili.. Sosai Yan gurin sukasa dariya,Bello yace ainaga alama shiyasa Daga zuwanka garinnan kafara Dukan yaran gari" Aina nasan haka halinka yake da rufdugu zamuma" nan ma dariya akayi kafin Liman yace. Babu shakka Nasir munji dadin kalamanta akan abokinka Kuma muna fada abinda ka fada ya Zama gaskiya" insha Allahu Nasir yafada kanshi a qasa. To Malam yakamata mu tafi Ko,,nan suka Tashi suka tafi gidan Malam. Yakumbo dake zaune nijlah nakan cinyanta tana rigima Taji sallamar Malam,,amsawa yakumbo tayi tana kallan nijlah tace. Toga malam yazo Naga Yana murmushi ga dukkan alamu yayi samuwa inaga Yau zakici shinkafa da miyar dakiketa mafarki"turo baki nijlah tayi tana kallan Malam kafin ta kurma uban ihu tana cewa. Wallahi yakumbo Babu abinda yakawo bakiga hannunsa Babu komai ba,,nidai Allah saikin siyamin burodi... Qarasawa Malam yayi ya cewa kinga Yar albarka Tashi kizo kiji Abu Wani Na tabbata Zakiyi farin ciki kinji Yar gidan kaka.. Maqe kafada tayi tana birgima a qasa,,nan Malam ya Kalli yakumbo yace,,kinga yakumbo dauko tabarma ki shinfida a rumfa ya fada Yana nuna yaloluwar rumfar Kara dake maqale jikin Dakin daba lallai ya wuci damuna ba,, Shinfida tabarma yakumbo tayi tana cewa Ikon Allah suwa muka Samu,,Malam kodai Yau zakka ta biyo ta gidanmu. Kedai ki shinfida kafin nayimiki albishir,,nan Malam ya juya Yana cewa ku shigo Daga ciki.. Liman ne a gaba Sai Nasir da Bello tare da sauran mutane dake tayasu murna,,wasu Ko yan uwan mahaifiyar nijlah ne... Tinda suka shigo yakumbo tabisu da kallo tana mamakin abinda ya kawosu adaidai wannan lokaci Kuma gaba dayansu,,kowanne ta Kalla fuskanshi dauke da annuri,,nan ta zauna Kan buhun dawa tana binsu da kallo.. Kinga yakumbo ruwa Zaki Basu ba wannan kallanba,,gaba daya suka Hada baki gurin cewa ah ah alhamdulillah ta zauna kawai muyi abinda ya kawomu.. Gaisu yakumbo tafara nan Taji suna yimata Allah ya Sanya alkairi" Seda suka gama ta juyo tana kallan Liman tace,,Liman me Kuma ya faru Naji ana yimin addu'a.. Eh yakumbo Yau Dai Allah yayi an daura auren yarinyarki" wacce yarinya Liman??, yakumbo ta tambaya mejin faduwar gaba,, nijlah dake kwance a qasa tana sharar hawaye tayi Shiru tana sauraransu tasan Dai ita dayace yarinyar yakumbo Dan haka ta Maida hankalinta gaba daya Kan Liman tanajin amsar dayake bawa yakumbo.. Yakumbo yarki nijlah,yanzun nan,Bayan idar da salla malam yabada aurenta ga.....Ai nijlah Bata jira Jin wane angon ba ta Tashi da gudu sabida Jin Kunya ya kamata,,Daki ta Shiga ta dauko dakalmin Danko Wanda yasha dinki da zare da allura tasa ta fita da gudu ta Bayan gidan,,kasan cewar gidan bashi da danga Babu Wanda ya Ganta. Mashkur" zabura yakumbo tayi ta miqe tsaye cikin rashin hankali da dimuwa tace,,badai wannan yaran mashkur ba,da naira hamsin bashi masa wahalan badawa??? Eh shifa Malam ya fada Yana Kallan yadda yakumbo ta haukace ta tubure masa.. To Wallahi Baze taba yiwuwa ba ,Akan me Zaka auran da nijlah ga Bako Wanda bamusan asalinsa ba,hasalina karatun arnane ya kawoshi ruga... Haba yakumbo be kamata kina fadar hakaba,,kinga Nasir yabamu labarin mashkur bashida Wani matsala ki kwantar da Hankalinki. Cikin kuka yakumbo tace haba Liman yanzu shikenan nijlah zata tafi ta barni" Bazan iyaba,kugayamasa wallahi ki warware wannan aure aba Dan gari yadda koya na juya zanga marainiya,,Anya Ko Malam ka riqe amanar da danmu yabari,,kaico mutuwa kinyiwa yarinyar shigar sauri,wayyo niya Allah Na,,nan fa yakumbo ta juya tana fillanci Niko nayi zugun tare sauraranta sedai banji abinda take gayaba,,ta jima tana kuka kafin Daga bisani sukayi nasaran shawo hankalinta.. Haba yakumbo meyasa Zaki haka,,kinsan bakisan auren Kika yadda naje naba,,kaga Malam niba aureni Bani so Wanda Kaba auren nijlah Baze taba Zama kusa damu ba nijlah zatayi nesa damu bamusan rayuwar dazatayi ba. Insha Allahu nijlah zatayi rayuwa me kyau ku kwantar da Hankalinku cewar nasir cike da tausayin yakumbo.. To Amma Dai ba yanzu Ze tafi da itaba ko??eh saimun gama service nan da wata 9 insha Allah" gaskiya yayi wuri yadai Yi hakuri Sai nijlah ta qara wayo nan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46