Skip to content

Chapter 17

Chapter 17

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,287 words 0 views Progress saved
Download Book

kai sabida kunya yace,,sanko Kichi abinci ko har kindena Jin yinwan.. Dasauri nijlah tace ah ah tana Tashi zaune. Hannun ta ya kama suka safko qasa ya,, takeaway guda ya bude tare da saka cokali guda biyu. Bismillah mana,Naga kin zuba abinci ido kina kallansa,,ko har yinwan ta tafi,,turo baki nijlah tayi tana nuna Dayan takeaway dake gefensa,,hannu yasa ya yaqara janyosa Yana nuna Mata Wanda ya bude.. Kici wannan idan baki qoshiba Sai a bude wannan ko,,cike da shagwaba nijlah tafara girgiza kai,,ni ah ah,,ni ni tuwan dawa nakeso.. Dariya mashkur yayi Yana kallan kwayar idanta,,ita dinma Shi take kallo bakinta a gaba,,hannu yasa ya doke bakin a hankali Yana cewa,,daga yau irin wannan abincin zakina ci,,bake bacin tuwan dawa Sai ranar da kika kaima kaka ziyara,, wannan akeci anan,,ya fada Yana nuna takeaway dake gefensa.. Beyi aune ba yaga nijlah Na rawa hadda juya duwawu,,baki ya saki Yana kallanta tare da sauraran abinda take fada.. Yeeeeh nima nazama 'yar gata,,kaza ya zama abincina,,tini nijlah ta maida abin waqa,,abinka da 'yar kauye lolxx.. Murmushi Kawai yayi Yana cewa idan kingama saiki zo muci abincin,,rawanta ta cigaba dayi ganin Bata da niyyan zuwa mashkur yace.. Shikenan ni Zan cinye Kazan,Naga alama bakici,, nijlah najin haka tayi saurin dawowa kusa dashi tana Jan takeaway.. Yaya haka,,ki ajiye muci,, Allah bazan ajiye ba Naga kaci rabanka,, wannan nawane.. Riqe baki yayi Yana kallanta,,bece komai ba ya kyaleta,,itako tasa abincin agaba tana chi tana waqa" Haka Kawai kaka zatamin baqin ciki da tinin ana bani tuwo yanzu ko nazama 'yar gata irin abun Mai gari.. Shi Dai mashkur kallanta Kawai yake Yana murmushi,, nijlah Bata ajiye abincin ba saida ta cinye tsaf kafin ta janyo Dayan takeaway Shima saida ta cinye duka kafin tayi hamdala... Bayan ta gama mashkur ya zuba tagumi Yana tinanin yadda zasu qare da mummy dafe kansa yayi daya Tina da Yasmeen,,lokaci guda bugun zuciyarsa ya qaru,,jiyake beyiwa Yasmeen adalci ba,,bisa ga irin soyayya da suke,,lokaci guda yaci amanarta ya saka Mata da Kishiya,to kishiyamana koma yace ta wuci Kishiya.. Sosai ya shiga tinanin nijlah ko har bacci ya dauketa.. Tinda Abba yakai Yasmeen daki ya kwantar da ita Yana Bata hakuri tare da yimata alqawari iri iri,,be baro dakinba saida yaga bacci ya fara daukanta,,Yasmeen Na ganin fitan Abba tayi saurin Tashi tana hawaye hannunta dafe da zuciyarta ta janyo wayanta.. Number mashkur tayi dealing tana hawaye zuciyarta Na qunu.. Mashkur dake zaune gefen nijlah yakasa bacci ga tinanin Yasmeen ya addabi zuciyarsa sedai baze iya kiranta ba sabida sanin tsananin Kishi nata yaji wayarsa Na ringing. A hankali ya daga idansa dayayi masa nauyi ya Dora kan kan wayarsa number daya gani ce tasashi firgita tare da wintsilowa kasa.... Inajin dadin yadda Luke bibiyar labarinnan duk da ba kullum yake zuwa muku ba,,kuyi hakuri ina fama da rashin chaji.. Yawan comments yawan typing... Comments & share.. *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN MAHMUD....* 2⃣7⃣&2⃣8⃣ Dakyar ya iya tashi ya zauna gefen bed,,zuciyarsa a tashe,,be iya magana ba sai Jin muryar Yasmeen yayi cikin Kuka,,baby dole Ka kasa amsani,,sabida irin abinda Ka aikatamin,,nayi mamaki sedai ina fatan hakan yazamamin mafarki,,baby Dan Allah Kada Ka gaskatamin wannan bakin labarin dake Neman tarwatsamin zuciya,,kukane yaci karfinta Dan haka ta saki abunta tanayi ba kakkautawa.. Jin kukanta yake kama ana diga masa dalma a cikin zuciyarsa ganin bata da niyyar denawa yashiyin karfin hali ta hanyar hada dukkan nutsuwarsa tare da daidaita numfashinsa bakinsa na rawa yafara magana,, Yasmeen Dan Allah kidena wannan kukan ki saurareni.. Baka da abinda zaka gayamin baby kawai kagayamin karyane abinda naji,,kasani natsani kishiya bazan iya hada soyayyarka da wata ba,,watan ma 'yar sadaka,,kuka ta cigaba dayi shiko yayi zuru Yana sauraranta,,seda tayi kusan minti biyu kafin ta cigaba da magana.. Baby kayi Shiru,, Dan Allah kace karyane,,wallahi Zan mutu Ka tausayama rayuwana,,baby kasan Yadda nakeji akanka,,Ka sani ko kawata banyadda ta gaisa da kai ba muddin akace da haske a gurin balle har na Bari aganka da Rana,, sai gashi duk Yadda nake tattalinka Saida Ka daukomin abinda ze zama ajalina.. Sai yanzu mashkur ya iya bude baki a hankali yace" akul dinki Yasmeen Kada naqarajin irin wannan maganar,,tsakanin keda nijlah babu Wanda zeyi ajalin wani,,fatana Ku zauna lafiy.. ... Yasmeen bata Bari ya qarasa magana ba tace,, Kai dalla rufemin Baki,,mugu azzalimi,,Wanda besan darajar soyayya ba,,Ashe zaka iya bude baki ka gayamin irin wannan maganar,,nayi mamaki sedai hakan dakayi ya nunamin Kai cikakken mayaudarine,,kuma maci amana.. Yasmeen kiyi hakuri ki fuskanci magana ta,,banayi Danna qona ranki kodan kiyayya ba,,wallahi,, Dasauri ta katseshi wallahi me,,nidai kawai Ka cuceni Amma bakomai nasan abinda zanyi,, Pls Yasmeen karkice haka,,yanzune Zan gane irin soyayyar da kikemin,,kiji tausayina karki Bari tashin hankali yayimin illah,,wallahi har yanzu inasanki babu abinda ya chanza a soyayyar ki,, haryanzu kina cikin zuciya tah.. Kukan da Yasmeen take ba bata damar Jin abinda mashkur yake cewa ba,, tari ta Shiga yi tana cewa nidai Ka yaudareni kodan kasan bazan iya rabuwa da Kai ba,,shiyasa kakemin irin wannan,,ba haka bane Yasmeen Dan Allah kidawo cikin hayyacinki,,nizan zo har gida muyi magana.. Ba wani magana da zamuyi,,sai yanzu na gane abinda yasa kaketa daga maganar aurenmu Ashe 'yar matsiyata masu yawo a jeje kake Neman daukomana... Dafe Kai yayi ya kuma kasa magana,,Banda faduwar gaba babu abinda yake,,dakyar ya iya magana Yana cewa,, shikenan kema ki dagamin hankali kamar Yadda mummy tayi ni Dama nasan,,kasan me baby.. Shiru yayi Yana sauraranta batare da yayi magana ba,,haka Yasmeen ta zage ta riqa zazzaga masa masifa tanayi tana kuka,,be iya amsataba Saima hakuri ya riqa bata yanasan kwantar Mata da hankali danshi bega laifintaba,,yasan anyimata abinda zatayi fiye da hakan.. Tana magana masifa ta katse Kiran tana cewa kuma wallahi karka sake qafarka ta sake takowa gidanmu,,kabari idan na mutu saikazo gaisuwa kaida 'yar sadaka.. Tinda Yasmeen ta kashe wayan mashkur yakasa zaune ya kasa tsaye Banda zagaye dakin babu abinda yake,,babu abinda yafi daga masa hankali illah magananta na qarshe,,Kada Ka sake qafanka ya sake taka qofar gidanmu,, dafe kansa yayi Yana cewa tome Yasmeen take nufi,,ina wallahi baze yiwu ba,,dake nasaba sai yanzu sabida qaddara ta samemu zaki gujeni,, wannan wanne irin masifane,,hannu ya daga Sama Yana addua,,ya Allah Ka kawomin dauki,,yafada idansa taf da hawaye... A hankali nijlah tafara bude idanta harta budesu gaba daya ta safke Kan mashkur dake saune kama mutum mutumi,,kallan idansa tayi taga Yadda hawaye ke rige rigen zuba,,dasauri tasa hannu tana goge masa,,tare da girgiza masa Kai.. Kayi hakuri Dan birni,,babba da hakuri aka sanshi,, murmushi yayi tare da goge hawayen yace,,ba kuka nayi ba,,harkin tashi a baccin?? Hannu nijlah tasa ta gogo hawayen tana Wasa dashi a hannunta,,Dan birni wannan menene,,bazan hanaka kukaba Dan Naga wannan qatuwar matar Zata iya zaneka,,duba da Yadda take zaremana Ido,,nasan itane tazo ta dakeka ko??? Bata fuska yayi ransa a bace yake kallanta,,Baya tafaraja tana bashi hakuri, Zonan yafada fuskanshi da muryanshi babu alamar Wasa yace" Bana gayamiki mummy itace mahaifiyataba,,amma shine kike maimaita abinda na hanaki?? Dan Allah kayi hakuri wallahi na manta kuma ni bazan iya fadar sunan ba,,sedai idan Ka Yadda Zan riqa cemata baba,..

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46