Chapter 15
Chapter 15
ba,,bakinta Na rawa tace,, Ba adadi,, to Amma Ke Daga Jin an ambaci Sunan yarinya Sai dagawa kanki hankali Nima ki nemi dagamin. To wallahi ki Maida hankalinki kafin....mama Bata Iya qarasa maganan ba ganin yadda Abba ya shigo ranshi a mugun bace,,Jin yadda mama tayi Shiru takasa qarasa Magana yasa Yasmeen tayi saurin dago Kanta a hankali ganin Abba yasata Tashi a guje ta fada jikinsa tana kuka tare da makerketa.. Hannu biyu Abba yasa ya rungumeta Yana shafa bayanta,, Wayyo Allah abba,,Abba mashkur ne" bakin Abba a Bude yace au kema ya gayamiki Kenan.. Dago kai Yasmeen tayi kafin tayi Magana mama tace.. Sannu da zuwa abban Yasmeen,,yakamata ta zauna ka huta kafin tafara yima shirmen nata.. Ba shirme Yasmeen tayi ba,,tabbas abinda ta gayamiki gaskiya ne Domin ko mashkur ya daura aure da wata jinjiran yarinya Kamar yadda mahaifinsa yake gayamin yanzu shiyasa Na Tashi a office,,Ko bakiga lokacin tashina Beb...kasa qarasawa Abba yayi ganin Yasmeen Na neman zubewa a qasa,,numfashinta na barazanar daukewa.. Kafin yayi Wani Abu harta zube qasa summama,,salati mama tasa tayi kansu da gudu tana kwala Abu me aiki Kira,,Abu kawomin ruwa,,kafin Abu tazo Har Abba yayi Kanta yana Bata taimakon gaggawa a matsayinsa na babban likita me fada Aji a wannan qasar.. Baki yasa cikin hancinta Yana hura Mata iska,,Seda ya Dade Yana Bata oxygen kafin Yasmeen ta amsa,,da kuka ta farka tana kallan Abba tace... Abba dagaske mashkur yaci amanata ya yaudareni,,Abba bantaba ganin baqar Rana irin Yau ba,,Abba wacce shegiyar yarinyace tayimin shigar sauri? Yar uwan waye a fadin duniyar nan? Shiru Abba yayi Dan yasan Yasmeen zatayi fiya da haka indai Akan mashkur ne.. Abba kayi Shiru Baka gayamin ba,,wallahi Abba sainayi maganinta Saina zame Mata dakalin majina,,Saina sa mashkur ya zame Mata hawainiya ta yadda zata kasa gane kanshi da gindinshi Abba Saina.... Dakata Yasmeen Wai Kishi haukane Zaki Samu agaba kina wadannan maganganun Ko Kunya bakiji a matsayinki Na 'ya mace Ko bakiga yawan Matan Duniya ba,,Idan akace kowanne namiji mace daya Ze aura Ai sauran sun Shiga uku,,Bama su kadai ba Harda iyayensu da 'yan uwa koke bakiga sauran kanninki Mata b,,tsawar da daddy yayi ne yasa mama tayi saurin Hade bakinta tana kallanshi... Dakata ummu Yasmeen Idan Ke baki damu da itaba Nina damu,,aure fa saurayin dazata aura yayi Amma Kika rufeta da fada saikace bakisan ciwan 'ya mace ba,,kokin manta ance ciwan 'ya mace Na 'ya mace ne. Ba haka bane abban Yasmeen Sai yaushe Zaka fara Gaya Yasmeen gaskiya,,yaushe Zaka fara nuna Mata bakomai kake nema kake Samu ba,,bafa abinda muke tsarawa kanmu muke riskaba,,face abinda Allah ya tsara mana.. To anji Malama yanzu Zaki fara wannan wa'azin naki Na banza da Wofi,,Idan kincika Ke malamace meyasa baki fara zuwa tashar arewa 24 kina fadakar da Mata ba... Kuka Yasmeen tasa tana rirriqe Abba tace,,Abba Dan Allah kayi Wani Abu wallahi Bazan Iya Zama da kishiyaba,,Abba waye ubanta?? Murmushi Abba yayi Jin tambayarta ta qarshe yace,,kwantar da Hankalinki Yar albarka,,ubanta ba Wani bane mace me yawo a daji Yana bi Lungu da Sako Yana kiwan shanu da Saida nono a qarshe Mota ta malkadesu suka Mutu shida uwarta,,Sai kuma yayi dariya irin tasu ta manya kafin ya dawo da kallansa inda take kwance a qasa"yace kitashi inasan Magana dake.. Kasa Tashi tayi mama Ko Dan haushi Bata bi takantaba Duk da itama Taji haushin auren da mashkur yayi.. Abba Da kanshi ya Daga Yasmeen ya zaunar Kan kujera,,ruwa ya dauko me sanyi yabata Tasha.. Nan yacigaba da Magana,,'yar lele ki kwantar da Hankalinki wannan yarinya ba 'yar kowa bace Yar matsiyatace Wanda suka kasa riqewa suka ba mashkur sadaka,,basuyi Duba da inda zasu kaitaba.. Shikenan sausu Rasa wazasu ba sadaka Sai mijina,,Abba Zan Mutu wallahi,,hannun Abba ta kama ta Dora a saitin zuciyarta tace,,Abba ka taba Kaji yadda zuciyana take bugawa kama zata fado Abba Kaine gatana ka temakeni ya saki wannan yarinya.. Kiyi hakuri 'yar Lele Nina yanke hukuncin Hana mashkur aurenki,,kiyi hakuri nasan Zaki Samu Wanda ya fishi,, Bakin Yasmeen Na rawa tace ah ah Abba Bazan Iya rayuwa ba mashkur ba,,Jinina da nasa dayane munzama hanta da jini,,Abba tayaya kake tinanin za'a raba hanta da jini Kuma su rayu??? Jikin abbane yayi sanyin ganin yadda Yasmeen ta kidime ta rikice ta gigice tana Magana kama wadda Tasha kwaya.. Sabuwar tsanar iyayen nijlah ne ta tsirga masa harya kasa Magana ya zuba Yasmeen Ido Yana mamakin yadda ta zurfafa a cikin soyayyarsa.. Abba kayi Shiru Abba ka taimaka ya saketa inyaso saimu Basu kudi ta Kula da rayuwarta Abba ka ceci rayuwana.. Surutai Yasmeen ta riqayi marasa Kan gado Hakan ba qaramin haushi Yaba mama ba,,sedai ta godewa Allah dayasa ba Kowa a falon Daga ita Sai Abba. Abba ko ranshi inyayi dubu ya baci,,ganin yadda 'yar Lele take sumbatu yasashi kama hannunta ya nufi dakinta da ita,,Duk Taku saiya Mata sannu Yana qara Bata hakuri... ********* Dakyar ya Iya juyowa Yana Kallan mummy Sai kuma yasaki hannun nijlah ya tako Har zuwa gabanta ya durgusa Kan gwaiwoyinsa tare da Hade hannunsa biyu,,idanunsa na hawaye.. Dauke Kanta mummy tayi Dan bataso soyayyarsa ta tauye Mata nata haqqin Har Taji ta amince da tafiyansa Duk da yasani zuciyarta bazata taba Lamunta da Hakan ba... Qara rarrafowa yayi cikin kaduwar zuciya da fargaba yafara magana"mummy Dan Allah kiyi Karki juyamin Baya,,mummy fishinki masifane a gareni,,mummy karkisa nafada cikin fishin mahaliccina,,mummy nijlah matatace Kuma amana,,Bata Dan gata balle Dangi a kusa,,mummy Koda Suna kusa Na tabbata Basu da abinyi,,Ke mahaifiyace.. Nijlah marainiyace shiyasa nakesan taimaka Mata,,Amma kiyi tunani Idan Har baki yaddaba nizan hakura da nawa farin cikin nayimiki biyayya a matsayinki na uwa.. Yana gama fada ya Tashi beko jira amsar mummy ba ya kama hannun nijlah dake rakube jikin Kofa tana hawaye,,sedai yakai jikin Kofa ya Dan risina yace.. Yaya,, aunty lateefah Saida safe,,Yana gama fada Yaja musu kofa.. Yana fita mummy tasa kuka tana cewa kungani ko,, mashkur ya tafi shikenan sun kangaranmin da yaro ya Shiga Wani Hali,,Ko rantsuwa nayi baza kaffaraba Akan surkullensu Na Fulani sukayiwa yarona.. Hakuri su lateefa suka riqaba mummy harta Dena kuka,,nan ta kwanta tana Nishi Sama Sama tare da tinanin abinyi.. Mummy Dan Allah kiyi hakuri Karki Bari hawan jini ya kama mana ke,,Idan Wani Abu ya sameki wallahi Saina tada hankalin kauyen kankan gaba dayansa cewar Yaya cikin tashin hankali... Mummy abin yazo da sauqi tinda yabaki zabi,,mu Kuma zamuyi masa zami mafi dacewa dashi,hakane lateefah shiyasa nakeso mummy ta kwantar da hankalinta,,da dadan kalamai suka riqa bin mummy Har bacci ya dauketa Bata Sani ba.. Mota yasa nijlah Shima ya Bude ya Shiga,,tinda suka fara tafiya nijlah take kuka tana qara qanqame jikinta,,hannu biyu mashkur yasa ya janyota jikinta,,nan ya kwantar da Kanta bisa cinyanshi Yana shafa lallausan gashin kanta tare da tuqi da Dayan hannunsa,,Duk da yadda yamata Bata Dena kuka ba Saima qara sautin kukanta tayi tana Kiran kaka,, sosai yakejin kukanta Har cikin zuciyarsa Dan haka yayi qoqarin dakatar da ita,, Kiyi hakuri kinji amaryar mashkur,,indai Ina tare dake Babu me qara tabamin Ke,,turo baki tayi tana kuka tace.. To to ba agabanka wannan mutumin yayi cilli Dani ba,,Kuma aka zageni hadda zagin Malam Duka bakayi Magana ba,, Karyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46