Chapter 5
Chapter 5
bazan iya rayuwa a irin wannan gurin ba,,Kai dai dakaga zaka iya saika zauna" To ai shikenan kinga Kenan bakisan gani,,Allah hubby inaso Kaine Ka zabamana wannan rayuwa ta nisanta juna,, Hira Sosai sukayi har Saida Nasir ya kasheshi kafin suyi sallama su koma kauyen,,bayan kwana biyu kowa aka kaishi gurin aikinsa inda mashkur ze riqa koya yara karatu a makarantar primary ta gari. Sosai yayi mamaki da ganin ko ajujuwan babu gaba daya sun lalace birbiri ya Gama lalata sauran,,a haka yake koya musu duk da ba zuwa sukeba,,watarana sedai yaje Shi Daya yagama abinda zeyi ya dawo... Nasir yayi sa'a kauyen da aka Kashi a kusa yake sedai Shi ana samun lalbai Dan Har headmaster garesu.. Wasa wasa Shakuwa me karfi Na qara Shiga tsakanin nijlah da mashkur,kullum saita kawo masa warar Fulani shiko yanasan taimaka musu Amma Malam ya Hana yace indai ba auren nijlah yakeso ba Baze amsa kudinsaba,,ba yadda mashkur ya Iya haka ya hakura sedai kullum Yana ba nijlah naira Goma Ko biyar tana zuwa dandali. Yau tin safe Malam ya tashi bashi da Ko naira biyar balle su Sami abinda zasu sa a bakinsu. Tinda nijlah ta Tashi take kuka ita yinwa takeji gashi Har karfe 12 Na safe Basu Sami abinda zasu sa a bakinsu ba. Dan Allah Malam kabar yarinyarnan ta Shiga Ko gidansu Indo ne tasa Wani Abu a cikinta kaga yaro besan Babu ba" Ni kaina abinda nake tinanin kenan sedai Bazan bar yarinya tana zuwa kwadayi gidan mutane ba,,tinda su Basu tausaya sun bamu ba.. Malam me zakayi Kar ka cemin Baka fasa Bada sadakan nijlah ba,,Dan Allah kabari kaqarasa Ko shakara Goma sha biyu ne" kinga yakumbo ki rufemin baki,,Ina yanzu nijlah ta cika shekara Goma. Dan Allah ba shawaranki nake nemaba.. Amma Malam...!Amma me kinfisu yinwa ya kashe yarinya muna kallo,,Idan Ko Na auradda ita Na tabbata bazata Rasa abinda zata Ciba... To Malam wazata aura kasan Dai iro bashi da kudin aure Kuma Koda ka bashi sadaka Baze Iya ciyar da nijlah ba sabida Shima dakyar take samu yaci.. Bashi zanba auren taba sedai inaso kisani a kwana kusa Zan auran da ita,,kai malam kafa Duba lamarin nan, Nijlah Najin batin aure ta tashi tana me Jin Dadi tace,,Malam ka gyale maganan kaka kayimin aure Nima Na riqa tuqa tuwo da kaina mijina Na siyomin tsire inaci... Yauwa Yar albarka,Allah yasa asamu Wanda Ze Iya riqemana Ke ya Kula da maraicinki,,hawaye kaka ta goge da zanin jikinta tace.. To a gaskiya koka auran da nijlah sedai mijin ya biyota gidannan Dan gaskiya banga Wanda Ze Iya juran rigiman nijlah ba" Idan kinga ana haka Sai kiyi,kinga Nina fita karbomana bashi Ko gari musamu Musa a cikinmu.. Adawo lafiya yakumbo tayiwa Malam kafin ta janyo nijlah ta rungume tana rera kuka" Kaji kaka da baqin ciki,,bakiso Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi .. Yawan comments yawan typing,Dan Allah ku rage godiya ki riqa sharshi Ta hakane zan gane sakon danake San isarwa Yana zuwa muku Comments & Shareπ *Momn sultan ce*βββ ππ *'YAR SADAKA..*ππ *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *HUSSAIN 80k* 7β£&8β£ Kujimin kaka da baqin ciki,baki Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi iron na abu, nijlah ta fada cike da yarinta!. Cikin kuka yakumbo tace!uhmn nijlah Kenan angayamiki kayan Dadi shine aure,,me Kika Sani game da Zaman takewar aure" Allah kaka Na Sani,,badai ruwa Ake zubawa a buta na alwala ba,Sai kuma ka zauna Idan anyi tuwo a cikin gida ka dauka Langa a zuba masa tuwo.. Nijlah Kenan babu abinda Kika sani"Allah kaka Na Sani Niki Dena kirana yarinya Kuma Naga Abu tayi zamanta a gidan Musa Ai Dai Nima Zan zauna" Allah ya kyauta cewan kaka tana Jin quna cikin zuciyanta.. Tana nan zaune Har Malam ya dawo dauke da Leda a hannunsa,, Wai haryanzu kina zaune kina tunani Akan abinda bashida mafita Sai wacce na fada" uhmn uhmn fa Malam wallahi nijlah bazata Iya Zaman aure ba,,ka Duba qanqantar shekarunta? Yakumbo Kenan tin yaushe muke neman mafita bamu samu ba,,se yanzu Dana samu Zaki kawo matsala,,kiyi tinani Dan Allah. Shiru yakumbo tayi tana nazari kafin tayi iya Bude baki tace" yanzu Malam Idan muka auran da ita akazo haihuwa ta kamu da jajjan fitsari ya zamuyi,, murmushi Malam yayi Dan ya gano abinda yakumbo Ke tsoro.. Indai wannan ne ki kwantar da Hankalinki,na tabbata nijlah bazata samu wannan matsalan ba,,to Malam kasan Wanda Ze aureta?? Kinga yakumbo Idan bakisan ayi aurennan kawai ki fada ni Kuma Zan zuba Miki Ido Naga yadda Zaki Iya Kula da ci da Shan nijlah,, yakumbo kinfi kowa sanin halin nijlah,,yinwa kawai Idan Taji ta riqa surfafa Miki kuka Ke Akan kudin dandali Sai nijlah ta kusan kwana tana ihu,,Ina Sai yanzu da Allah ya kawo mashkur wannan kauye nijlah ta Dan samu gata,,Idan ba haka bane Sai gayamin.. Matsowa nijlah tayi jikin Malam tana murna tace,,Malam kawai kayimin aure ka kyale kaka tayi ta abunta,,Nima Na riqa Cin tsire da kosai irin Na birni Ko,,dungurinta Malam yayi Yana cewa eh Zan Miki aure Amma sekin Dena yiwa mutane kukan dare" Dasauri nijlah tace Allah nadena,,kaka aidai Na Dade banayi Ko? Shiru kaka tayi tana sauraran shirme nijlah kafin tayi qoqarin cewa,,Hakane Malam Nima Na yadda Na Kuma amince da auren nijlah sedai inaso ka zaba Mata mijin daze Iya Kula da ita! Haba yakumbo muda zamu Bada sadakanta mune zamu zaba Wanda zamu aura Mata" to ai abin ne' kinga kedai kawai kiyiwa yarinya addu'a. Kinga dauki wannan kanzon ki jiqamana Musa a cikinmu" Ni Allah gari kwaki nakeso ba kanzo ba nijlah ta fada cike da shagwaba,,rarrashinta Malam yayi yayinda yakumbo ta tafara jiqa qanzon,,bako Mai haka ta zuba kuli suka ci. Suna gamawa Malam ya tafi gidan kakannin nijlah Na wurin uwa,,anan ya samesu da magana nan,Basu Bada matsala ba Dan kowa ya amince,nan ya dawo gida cike da farin ciki Na samun nasara Dan a ganinsa auran da nijlah shine Abu mafi sauqi daze Bata farin cikin dasuka kasa Sama Mata Shi a matsayinta Na marainiya Kuma jika a gurin su.. ******* Zaune take ta hannu biyu Akan kumatu da alama tayi zurfi cikin tinanin,,a hankali ta cire hannu ta dauko wayanta dake Kan center table ta qara Danna Kiran layinsa. Abu daya Ake gayamata Dan haka tayi cilli da wayan tana Tashi tsaye,,Saida Nace karkayi tafiyan nan Amma ka dage Saida kayi gashinan wayama ya gagaremu sedai kayi kasamu lokaci ka Kira,,Anya kuwa mashkur be samu matsala ba.. Girgiza kai daddy yayi Yana qarasowa kusa da mummy, nan ya zauna kusa da ita Yana kallanta cike da kulawa yace,, Haba Khadija Se yaushe Zan gayamiki kidena sa damuwa a ranki,girma fa ya kamaki,,Karki sa ciwo yamiki illah Akan abinda bashida Wani illah.. Haba Alhaji Taya kake tinanin hankalina Ze kwanta Akan tafiyan mashkur,kako je kauyen kaga inda yake zaune,, toyaya kikeso ayimasa, mashkur Dai ba yarone qarami ba,da inyaji wahala Baze dawo gida ba,Kuma kina kallo nasama masa admission a UK Amma fur yaran nan yace bayaso ga idda yake muradi Toba seki barshi yaje yayi ba.. Cikin kuka mummy tace haba Alhaji kana nufin haka zamu zuba ido mashkur ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46