Skip to content

Chapter 45

Chapter 45

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

zuciya Dan shiyake kama ya cireta ya cillar koze huta da abinda yakeji. Wallahi sainayi Sharia dakai matata ka doka Har kana Iya maimatawa a gabana. Ba Musa Mai Gadi ba Hatta Maryam Saida maganar ta girgiza, a tare suka maimata maganar' Matarkafa kace? Fuskan mashkur a Hade kama hadari yayi Kan Musa Yana cewa' ka Hada kayanka yanzu basai anjima ba' Dan wallahi bazakayi kwanan farin ciki ba, ka kumayi sa'a bantaba fada Da Wani ba da tau Saina kusa kasheka.. Hannu Musa ya Dora aka Yana cewa' wallahi ban daketaba sharri kawai Maryam tayimin' Ke Maryam Dan iyayenki ki gayamasa Karya kike wayyo Allah Na Ni Musa Ina Zan Samu ogah kamarka me tausai dajin kai' Na tuba ranka Shi Dade nizan Bata hakuri. Be jira cewan mashkur ba ya rarrafa zuwa ga nijlah Yana kuka da hawaye Yana cewa' Kiyi hakuri ranki ya dade Banda abinki Ai bayani ake' Ina zanyi tunanin ogah Ze sauri wannan abun,,kiwa Allah ki ceceni. Nijlah Bata kulashi ba Saima turo masa baki tayi tana fulatanci Wanda nikaina bansan abinda take Gaya ba.. A fusace mashkur ya fuzgo Musa Yana cewa' kai Wai haka be ishekaba saika samin ita a gaba' to Bari nayi maganinka saika dawo cikin Hankalinka tinda Baka dashi. Tattare hannun Riga mashkur tashiga Yi Yana qoqarin damqar Musa mummy ta saki Wani ihu Wanda yasa suka dawo cikin Hankalinsu' be Iya aikata abinda yayi niyyaba ya Shiga cikin falon da gudu zuciyarsa na bugawa da sauri Dan tinda yake be tabajin kukan da ihun mummy Kamar Na yanzu ba. Jikinsa a sanyaye ya qarasa Shiga falon sedai abinda ya gani yayi bala'in Daga masa hankali Har besan Sanda ya riqa tsallake kujerun daya Bayan daya ba' ji yayi tamkar Ze Rasa mahaifiyar Tashi sabida Jin sautin bugawan da zuciyarta keyi. Yana zuwa inda take yayi saurin rungumata jikinshi Yana jera Mata sannu' Lafiya mummy badai haduwa kikayi ba? Mummy Bata Iya Magana ba Dan Iya azaftuwa ta azaftu Banda nuna masa cinyanta Babu abinda take tanayi tana kuka. Shiru yayi Yana Jin kukan nata kama ana diga masa dalma' da kyar ya Iya tashin mummy ya kaita Kan carpet Yana jera Mata sannu' Mummy Bata Iya amshiba Sai cije lebe take tana Kiran wash wash' sannu mummy Wai garin Yaya Hakan ta faru? Nijlah ce da Maryam suka shigo suka bar Musa nata zagaye faluwa yana sumbatu cikin tashin hankali. Cikin wannan Hali Mummy ta dago kai' tana cewa' ku ficemin da wannan shegiyar yarinyar banasan ganinta' Sai kuma tasa kuka tana cewa' Auta kaga abin bake gayama Ko,, gashinan tayi sanadiyyar gurguncewar uwarka Dan banza kawai da Baka Kishina... Baba ni kuma, menayi Miki Nijlah ta fada tana nuna Kanta? Ki fita nace, fita Dan ubanki' Kallan Maryam mashkur yayi bakinsa Na rawa yake tambayanta? Maryam meke faruwa kiyimin bayani Dan Allah,, mashkur ya qare maganar cikin rauni da tausayama rayuwarsa. Bakin Maryam Na rawa take gayamsa abinda ya faru ta qare da cewa' Nidai bansan yadda akayi ta fadi ba' Iya abinda nasani Na gayama. Bata Ida rufe baki ba mashkur yayi Kan nijlah ya fizgota fada Kan kujera' nan ya zare belt Yana daka Maryam tsawa' .fita a Dakin nan kafin Na Hada dake.. Sosai jikin nijlah ya Shiga rawa tana bashi hakuri tare da cewa' wallahi Bani bace wasu aljanu nagani inaga itama sune suka Bude Mata Ido kaga Kuma tayi qatuwa da yawa bazata Iya gudu ba shiyasa suka cutar da ita.. Haushi mashkur yawaraji Dan Dama ya tsani ta Kira Mummy da qatuwa gani yake kama raini ne' Bude baki tayi da niyyan cigaba da bashi hakuri Amma ya rufe Ido ya Daga hannu ya safke Mata belt din a bayanta' Razananniyar qara nijlah ta saki Dan tinda take ba'a taba yimata irin wannan Duka me Shiga jiki ba Dan Ko Dukan da Yasmeen tayi Mata bekai wannan zafi ba. Saida tadena Ji Na wasu 'yan lokuta kafin jinta da ganinta su dawo' Rikice masa tayi ta Kuma Rasa inda zata sa Kanta Taji Dadi Banda juya kai Na azaba Babu abinda nijlah take,,kuka takesanyi sedai kukan yaqi zuwa haka ta kife a gurin tana birgima. Daga belt din ya kumayi Yana cewa' kin Tashi kin Bata hakuri Ko saina qara miki' nidai banga lokacin da Zaki hankali ba nijlah Anya Ko kinaso mu zauna lafiya? Bata Iya Magana ba Saima shesheqan kuka ta riqayi numfashinta Na sarqewa' amma Duk da haka be kyaketaba ya dakamata tsawa Yana koranta waje. Da gudu nijlah ta Tashi ta fita a Dakin cike da tashin hankali ta fita. Tana fita mashkur yasa hannu ya goge hawayen tausan nijlah Dan ba'a San ranshi yayi Mata haka ba yayine kawai sabida mummy Taji Dadi ta Kuma barshi da nijlah Dan yasan Babu makawa mummy zata Iya cewa saiya saki nijlah adaidai wannan lokacin Duba da halin daya tsinceta a ciki.. Kallan Mummy mashkur yayi Yana cewa' Mummy kiyi hakuri nizanyi maganinta,, yanzu ki Tashi Na kaiki hospital' Cike dajin ciwo mummy tace ' Bazan Iya tashiba auta' ka Kira Dr kawai yazo ya dubani anan.. Beyi Magana ba yayi dealing number likitan.. Nijlah na fita ta zauna bakin kofa tana kuka tare da Dana sanin yadda da rabuwa da kaka Ashe dai talauci yafi Wani tashin hankalin sauqi,dama shirme nake danake ganin Zan Samu farin ciki Idan nayi aure ya Allah nijlah ta furta daqarfi tana yarfe hannu sabida Har yanzu bayanta be gama saisaita ba. Hannu tasa ta shafa gurin aiko tana cirewa taga jini kwance a hannunta' wayyo Allah nijlah saita Tashi da gudu tana zagaye get din tana Kiran kaka da laman' Dama haka aure a birni yake gashi Na kawo kaina inda za'a kashemini' wallahi Bazan zauna ba gida Zan tafi' Bata qara neman shawaran zuciyantaba ta tashi,,Bata Ko dauki takalmi ba ta fita da gudu tayi titi' Sai da tayi tafiya mai Nisa kafin taga me napep ta tsayar dashi' . Qoqarin tsayawa yake nijlah Tasha gabansa Aiko ya bigeta ta fadi gefe' tsoro da tashin hankali suka sa me napep ya gudu Sai wata matashiyar budurwa dake Bayan me napep dince ta tsaya kasan cewar layin ba mutane sosai ta nemi dauki Bata samu ba,,haka ta cire mayafinta ta dauka nijlah tasa a Mota tana mejin tausan yarinyar ta tafi asibiti da ita... _________ Haba kawata yakamata ace munyi shagali a bikin nan gashi wannan corona tazo tayi kaka gida Har ansa dokan ta bashi a kowanne state kinga Ko Dole a Daga biki suwa Bayan Sallah.. Zaro Ido mubeena tayi tana cewa'haba kawata keda Zaki addu'a ayi bikin nan a gama saiki kawo wata magana' Naga Dai ba dolene ayi chasu a biki ba. Ke kinga mubeena kibari kawai muyi a lokacin da zafi mana Dadi Ko bakisan ita Yasmeen'yar Gata bace Dan haka yakamata lokacin Duniya tasan da aurenta,, zee ta fada tana kallan yasmeen. Yatsina fuska Yasmeen tayi tana hararan mubeena' Sai kuma ta Kalli Zainab tana cewa yauwa zee gayamata gaskiya to Idan ba'a Daga biki ba Sai ki gayamin ta inda abokan Abba zasu shigo qasar kinsan abbana bashida abokai dayawa anan yawancinsu ba 'yan qasa bane.. Gaskiya ne kawata suka tafa da zee' Cikin rauni

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46