Skip to content

Chapter 7

Chapter 7

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,257 words 0 views Progress saved
Download Book

Liman yayi Yana cewa,,kayi daidai Malam hukuncin daka yanke yayimin Dadi.. Har mutane sun fara bita akace su dawo za'ayi wata Magana,, lah mashkur zo muje naga mutane na koma cikin masallaci,, jeka kawai nizan jiraka ana,,sabida sanin hali yasa Nasir da Bello suka barshi anan su suka dawo cikin masallacin.. Liman ne yafara magana,,to jama'a Allah ya kashe Yaba Wani,,game dukiyar aure Kuma yake sha'awar qarawa mace yazo gata,, Ko saurayin daya shirya,, charaf,,Wani tsoho yayi saurin Daga hannu.. Malam ne ya katse Liman ta hanyar cewa,, *'YAR SADAKA CE* to kunji abinda Malam yace,,yarinya sadaka ce.. Yauwa ga Wani Chan ansamu Liman ya fada Yana nuna tsohon mutumin dake rankwafe Yana murmushi,,yauwa Ala gafatta Malam matso kusa Liman yace da wannan tsoho,,matsowa tsoho yayi kafin Liman ya tambayeshi. Menene sunanka,,sunana laman ya'u,,to Malam ya'u,,ita wannan yarinya da kace kanaso sunanta nizlah.. Nijlah,, Nasir ya maimaita Sunan tare da fita aguje Yana Kiran mashkur,, Mashkur mashkur,Dan Allah mashkur kazo ka cece yarinyarnan indai soyayya na gaskiya kake yimata,,kai lafiya wacce yarinya kake Magana,,bakin Nasir Na rawa yace nijlah ce,,gata can za'a Bada sadakanta.. What kana nufin aurenta za'a Bada,,eh wallahi kayi sauri muje Kar a daura auren,,da gudu suka nufi masallacin mashkur Na tinani a cikin zuciyarsa... Yanzu Idan na Karbi auren nijlah ya zanyi da Mummy,,Waze yadda temakonta,nayi,tayaya Zan fahimtar da iyayena,, Daga zuwa bautar qasa na biqe da aure,,auren ma Na qaramar yarinya Wanda Bata wuci shekara Goma ba!!! Da wannan tinani suka Shiga cikin masallaci,sunyi sa'a baa daura auren ba,,sedai ana gab da daura wa,,ku dakata Nasir ya fada Yana nuna mashkur,, wannan shiyafi dacewa da auren nijlah indai sabida Allah za'a Bada sadakanta.. Wannan gaskiya ne, mutane suka amsa Suna goyan Bayan mashkur"" Malam ya'u Najin haka yace Sam be yadda ba.. Akan me nasamu Mata zakumin bakin ciki,, hakuri Liman ya Shiga ba Malam ya'u Amma Duk da haka ya dage Shi saiya auri nijlah.. Nasir ne yace kaga tsoho karka damu,,wannan Ze Baka naira dubu Goma kabar masa ita.. Kai yaro kalla idona Malam ya'u ya fada Yana zaro Ido waje.. Atare Nasir da mashkur suka zuba Alhaji ya'u Ido Suna sauraransa. Nan alhaji ya'u yacigaba da Magana,,wallahi Ko naira dubu hamsin zaku Bani Bazan hakura da auren nijlah ba,,Har Sai kun auramin budurwa me suffa irin ta nijlah,, What? What me kace tsoho,,to wallahi Ko ka amsa dubu Goma Ko kayi asara gaba daya,,nan Nasir ya juya inda liman Ke zaune yace.. Liman kaga wannan abokina ne dashi mukeso adaura wannan aure indai Malam ya amince. To Malam Kaji abinda yaro yace,,Liman yafada Yana Kallan Malam,, Sassanyan ajiyar zuciya Malam ya safke kafin yace,,Liman Bani da zabi kawai kayi Mata zabin daya dace,,to shikenan Liman ya fada tare da gyaran murya. A matsayina na limamanin wannan kauye Zan auran auren nijlah da wannan yaro,kai yaro Mene sunanka"" kasa Magana mashkur yayi nasir yayi saurin cewa mashkur Hussain. To Masha Allah, mashkur ka amince Zaka auri nijlah,, mashkur besan lokacin daya Daga kai alaman eh ba. Ba'a Wani bata lokaci ba aka daura auren nijlah abbakar tare da zankadeden angonta.. Nan Alhaji ya'u ya riqa zagege zagege Yana cewa an nuna bare yafisu,, ya qara da cewa Allah yasa Dan birni ya siyar da nijlah kowa ya huta,,maganganu marasa kai da gindi ya riqayi Har Saida manyan 'ya'yansa suka fiddashi a masallacin. Mashkur Na fito yaji Wani irin tashin hankali ya ziyarci zuciyarshi nan ya barsu Nasir Suna tattaunawa da Malam Dan koya tsaya Baze Iya cewa komai ba sabida tsantsar tashin hankali.. Jiyayi Idan beyi waya da mummy ba Baze samu kwanciyar hankali ba, Dan haka ya nufi inda suke waya,, Da zuwashi ya fara Kiran layin mummy sedai wayar Na Shiga mummy taqi amsawa tana me Jin haushinsa. Karin ya qara Kira wayar yaya ta shigo,,nan yayi saurin kai hannu ya dauka Yana Kiran hello yayan mashkur,,ba Wani yayan mashkur da Zaka kirani,,kasa mana uwa a tashin hankali sabida bakasan me kake ba Ko mashkur??? Kayi hakuri yaya wallahi ban tafi da fishin mummy ba Har Saida ta amince Na tafi" Karya kake mutumin banza da wufi,ahaka kakeso karatun yayima albarka? Kayi hakuri yaya mashkur yafada zuciyansa Na halbawa day sauri da sauri. Inaso ka Bude kunnanka da kyau ka saurarani" bakin mashkur Na rawa ya amsa da to yaya. Kaje yanzu ka Hada kayanka ka dawo gida Idan Har bakasan bacin ranmu" Wani irin Abu mashkur yaji ya buqi zuciyarsa Har Sai da ya dafe da hannunsa yace ,yaya Yau fa kace? Eh Yau Nace Ko bazaka iyaba Ni a gobe Na dawo qasar nazo Har inda kake,,ah ah yaya kayi hakuri Zan dawo yafada yanajin kuka Na zuwa masa,,yadau Fi kyau yaya ya fada Yana katse Kiran. Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa Na Shiga uku Ni mashkur meya kaini auren nijlah gashi Ina neman sa kaina a 100,yanzu yaya zanyi? Be Iya samun amsa ba yaji Wani Kiran Na shigowa cikin wayarsa" Yana dubawa Yana aunty ladefa,zaro Ido yayi waje Yana tinanin fadan da aunty ladeefah zata masa,sedai Baze Iya Qin daukaba sabida yasan abinda Ze biyo baya,hannunsa Na rawa ya dauka Yana Kara wayar a kunne aunty ladeefah tafara da................... Dan Allah Dan annabi Idan kinsan bazaki Iya comments ba Karki soma karantawa. Comments &share😍 *Momn sultan takuce* πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜ *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *HAJJA FATI...* 1⃣1⃣&1⃣2⃣ Ashe Baka da kirki mashkur,mahaifiyar tamu kakesan kashewa" Anya ko kanasan albarka a karatun naka" Aunty me kuma nayi,uwarka kayi Dan bantan ubanka,, mashkur ni kake tambaya abinda kayi Dan qaniyanka??? Sanin halin aunty ladeefah da fada yasashi cewa ah ah,,Amma aunty" Amma me Ka rufemin Baki, ko kanaso kagayamin karatunka da zuwa wannan mugun kauyen yafi mummy daraja,,dasauri ya Shiga girgiza Kai kama tana kallanshi... Au rainin hankalin naka harya Kai ina magana kayimin shiru" Haba aunty bafa Nina Kai kaina wannan rigar ba,kaini akayi kuma wallahi bantafi ba Saida Mummy ta amince yafada cikin sanyin murya. To yanzu tace bataso Dan haka Ka tattara kayanka Ka dawo kafin nazo har garin naci maka" Amma aunty kinsan ko rabi banyi a aikin nan ba,, sai dagamin hankali kuke"inye mashkur nikake gayama haka,,ba laifinka bane laifin mummy ne datake daure maka gindi" Kiyi hakuri aunty amma"Amma me to wallahi Ka sani a yau nakeso Ka dawo gida kafin gobe, Nima a gobe Zan zo qasar nida yaya saika gayamana dalilin dayasa kakesan dorawa uwarmu hawan jini?? Aunty yanzu yamma yayi bazan iya tafiyan dare ba,,kaika sani nidai magayama karka Bari mu riga zuwa qasar Dan jirgin asuba zamu hau..! Shiru yayi Yana sauraranta batare daya iya magana ba.. Cigaba da magana aunty ladeefah tayi tana cewa, Banda shashanci irin naka mashkur kafi kowa Sanin halin mummy tinda Kai kake zaune da ita Amma Ka take Sanin Ka tafi gurin da tafi tsana a zuciyanta" kana kallo tin muna yara mummy batasan zuwa kauye balle harta rabi Fulani,,kodan lokacin bakada wayo... Zuciyarsa na quna tare da tilin Dana Sanin zuwanshi wannan kauye yace aunty kiyi Insha Allahu goben Zan zo kafin kuzo,,ni inaga dakun hakura da zuwa nizan ba Mummy hakuri.. Bazamu fasa zuwa ba,,ok kanaso kaje ta lallabeta

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46