Chapter 4
Chapter 4
Murguda masa baki tayi tana cewa,,lafiya Zaka Kira sunana? kiyi hakuri nijlah Bada niyya nayi Hakan ba,,kinji yarinya, Nasir ya fada Suna Hada Ido da mashkur dayayi kama besan abinda suke ba.. Yarinya Kuma,,nice ma yarinya,,to sannu babba,,dariya Nasir yayi Yana Kallan nijlah,,nidai Duk ba wannan ba,kin yafemin? Karka damu Allah yanasan me yafiya nayafema,,Nima ka yafemin batama Mota danayi" Nagode sosai Nasir ya fada Yana murmushi,,sedai Bani Zaki nema tafiyan Bata motor ba,kinga Wanda Zaki nema danba motana bane nashine,Nasir yafada Yana nuna Mata mashkur. Har qasa nijlah ta sunkuya tana kallan fuskanshi tace,,Dan birni kayi hakuri Kaji, murmushi mashkur yayi,ya Bude baki a hankali yace,Tashi kinji kanwata,,maqale kafada nijlah nan yayi murmushi danya gane nufinta yace, shikenan Na hakura Amma Karki qara zana Mota kinji,,to nijlah tace ta Tashi da gudu zatabi kawayenta mashkur yace kinga nijlah zo.. Juyowa tayi da niyyan zuwa idanta ya safka Kan Na iro daya zuba Mata su alamun tambaya" lah iro yanzu nake dubanka anan,Hade Rai iro yayi Yana hararanta,,kai iro Daga tambaya Sai harara, nikaga tafiyana.. Ke nijlah Ina kikasan wadannan ya fada Yana nuna mashkur" cike da tsoro nijlah tace yayanane Daga birni suka zo" kin tabbata eh mana nijlah ta fada tana kallan mashkur" sosai mashkur ya cika da mamakin wayo irin Na yarinya sedai abinda yake tambayan kansa shin wanene wannan yaran da nijlah tayi Karya. Nijlah Na ganin tafiyan iro ta qaraso kusa da mashkur tace gani" naira hamsin mashkur ya miqa nijlah Yana murmushi,amsa wannan Duk da Naji kince ba ciye ciye ya kawokiba,, Nagode sedai kaka ta hanani amsar kudin samari indai ba iro ba,,wanene iro mashkur ya tsinci kansa da tambaya" Iro yarone dabe wuci shekara 21 ba,,shine yake neman auren nijlah,, mashkur yaji Bello Na bashi amsa" Kai Bello kana nufin kace wannan yarinya saurayi ne da ita?? Kwarai dagaske Bello ya bashi amsa,rufe fuska nijlah tayi tana dariya" mamaki sosai ya cika mashkur Nasir ne ya qara kallan nijlah yace yanzu Ke yarinya kinsan menene soyayya,,kasa Magana nijlah tayi ganin haka yasa Bello cewa.. Kinga nijlah amsa kije ki Sai abinda kikeso nizan Gaya yakumbo,,kasa amsa nijlah tayi Duk da tanasan siyan Abu a dandali,,qara miqa Mata kudin mashkur yayi,,Kanta a qasa tace Ni biyar Zaka Bani wannan yayi yawa ta fada Kanta a qasa.. Ki amsa wannan Bani da chanji,,wannan shine qaramin kudi a jikina,,Nasir Ko kanada Goma,,ta amsa wannan Nasir ya fada alamun Babu.. Kasa amsar kudin nijlah tayi,,kanwata ki amsa mana,kefa Naji yanzu kina Gaya Wani Ni yayankine kodama Karya kike,,Kunya ce ta kama nijlah nan ta miqa hannu ta amsa kudin,, Nagode sosai Allah yasaka da alkairi,,Nima gobe Zan Baka fura da nono,, Bata jira amsar Saba ta Shiga dandali tana murna,, Bata Dade a gurin ba ta tafi,,tin Daga bakin kofa nijlah Ke Kiran kaka,,kaka! Kai wannan yarinya Ni harna fara bacci Zaki tadani,,kaka kinga wannan Dan birnin ya Bani kudi harna Sai abin biyar kinga sauran,ta fada tana miqa kaka Chanjin.. Lalala nijlah waya baki wannan kudin kaddai kicemin Wanda ya dakeki dazu,,kaka bashi bane Wanda ya riqe Yana mishi fada,,Kuma Shima yabani hakuri,,to Duk Naji Amma Daga Yau Karki qara amsar kudi ahannun Wani koba na hanaki ba,,kaka Nima ban amsaba,Ina wannan bellon na gidan Liman,eh nagane cewan kaka,to shine yace Na amsa Ze gayamiki,,to Allah ya akaimu goben zansa Malam ya tambaya. Washe gari karfe 10 na safe Malam yaje gidan liman anan sukayi magana da Bello ya tabbatarwa da Malam yaran bashida matsala,sannan hankali Malam ya kwanta. Tin asuba mashkur yake Kiran mummy sedai network ya Hana wayan Shiga,,dafe Kai yayi Yana salati,,lafiya mashkur badai wani matsala bane? Matsalane babba Nasir tin jiya nake Kiran mummy wayan yaqi Shiga gashi kasan halin mummy na tabbata yau bata rintsa ba. Ni abinda ke damuna Kenan tinda muka zo ban samu kowa a waya ba,,ance semun fita wani Dan kauye anan kusa zamufi samun network,,kaga Nasir Kai kasan da haka Ka Bari nake ta kira,tashi da sauri muje na Kira mummy" Dariya Nasir yayi yace Kai mashkur tinda muka zo banji Ka Kira Yasmeen ba sai mummy. Murmushi mashkur yayi kafin yace, Nasir bana hada mummy da kowa na tabbata yanzu Yasmeen tana daki ko bacci taba tashi ba,,mummy ko bazata iya bacci ba Dan bataji lafiya naba. Nasir be qara magana ba sabida yadda da maganan mashkur ya tashi suka fita,, Bello suka gani yazo kawo musu kayan kari,,abokaina ina zuwa,,waya mukesanyi cewan mashkur Yana miqa masa hannu,,bayan sun gaisa Bello ya ajiye kayan abincin suka nufi kauyen.. Da Malam suka hadu a hanya nan Malam yake masa godiyan kudin Daya ba nijlah,,bayan Malam ya tafi mashkur ya juya Yana kallan bello.. Bello Naga wannan mutumin sai godiya yake akan naba nijlah naira hamsin,,nawa Raina 50 take daze Namin godiya har haka??? Hmmm Kai agurinka naira 50 bata da yawa Amma Banda gurin Malam da jikarsa nijlah" au dama ba shine mahaifinta ba" Mahaifinta da maihaifiyarta sun rasu suke Kula da komai nata sedai Basu da karfi,, Dan ma suna San yarinyar kullum addu'a suke Allah ya kawo Mata mijin aure su auran da ita su huta" Aure kuma nijlah har nawa take daga ganin yarinyar bata Ida shekara 11,, murmushi Bello yace yace ai nata Kai hakabama saura wata 4 ta cika shekara Goma. Tashin hankali Amma akesan auran da ita cewan Nasir cike da mamaki,,to Nasir ya zasuyi Basu dashi kuma mu a wannan kauyen muna auradda yara shakara 13 zuwa 14.. Hira sosai suka riqa tafiya Bello Yana Basu akan labarin iyayen nijlah da rayuwarta,,tin daga nan mashkur yafara Jin tausan yarinyar jiyake dayana da yadda zeyi Daya taimaketa, akan auren da akesan yimata,,ahaka har suka Kai inda network ya hau Kan wayansu.. Hamdala mashkur yayi ya Kira layin Mummy,,bugu Daya biyu ta dauka muryanta a sanyaye" Assalamu alaikum mummy na kin tashi lafiya?? Kaima kasani ko lafiya ko akasin haka,,yanzu abinda kayi Ka kyautamin Kenan kodan kaga na damu dakai ko auta. Kiyi hakuri Mummy wallahi ba laifina bane garin me ba network yanzuma seda mukayi tattaki zuwa wani guri me nisa aka samu network. What mashkur kana nufin bazan riqa samunka a waya ba,,to wallahi kayi gaggawan baro wannan kauyen kafin naci mutumcinka,,Kako San a zaune na kwana. Pls mummy kiyi hakuri iya yaune Insha Allahu za'a gyara,,yafada haka danya kwantar Mata da hankali" Nidai nagayama kadawo kafin na Gaya daddynka tinda ni Ka rainani,,inyaso Shi yafada kaji" kiyi hakuri bata amashi ba ta katse Kiran ranta a mugun bace" yasan koya Kira ba dauka zatayi ba Dan haka ya tura Mata text massage. Layin Yasmeen ya Kira dake zaune kusa abbansu tana Shan ice cream" murmushi tayi tace lah abba kaga mashkur ya kira. Murmushi abba yayi yace dama na gayamiki ze Kira saiki dauka kafin ya katse,, dasauri ta dauka ta tashi ta koma dakinta,,hello hubby nah! Na'am baby kin tashi lafiya,,lafiya qlau sai kewanka,,baby daga tafiya harkin Fara kewa da wuri haka,,karki manta shekara guda zanyi,, Narke masa tayi tana kukan shagwaba tace,,Dan Allah Kada kayimana haka kaface 1 month zakayi Ka dawo" ah ah baby garin da nisa bazan iya wannan sintirin ba,,keya kamata kizo mu gaisa. Bata fuska Yasmeen tayi tana turo Baki,,kaima kasan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46