Skip to content

Chapter 14

Chapter 14

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,258 words 0 views Progress saved
Download Book

ko haryanzu bata iya cewa komai ba ahankali ta rarrafa ta qaraso kusa da mashkur,,hannu biyu tasa tana goge masa hawaye.. Kado kayi hakuri kazo muje can garinmu kaga kaka da Malam Basa yima fada irin hak..Bata rufe baki ba.. Yaya yasa qafa yayi cilli da ita nan ta zube jikin kujera tare da riqe bayanta ta saki wani marayan kuka.. Kasa dagowa mashkur yayi yanajin ze iya daukan komai Banda dukan nijlah,,sedai a yanzu bashida yadda zeyi haka ya kallo ya barta ta cigaba da kukanta Badan bayajin zafin kukan nata ba sedan ba yadda zeyi.. Kai babban Yaya Ashe baka da hankali,,matar kanin naka kayiwa haka,,Ashe bazaka iya hada zumunchinku anan gaba ba,,kana babba kana zubda girmanka,,to wallahi ku bude kunnanku da kyau kujini.. Ni din nan bana jayayya da lamarin ubangiji duk abinda tafaru Dani murna nake ina godewa Allah,,se yanzu danya ba Dana kyauta mafi muhimmamci da qima Zan qi gode masa,,Toni ba haka nakeba,, Abu guda yasa kukaga nayi shiru harna kasa magana.. Shine ganin yarinyar Karama da ita,, mashkur ta Yaya zaka iya zaman aure da wannan??? Dasauri mashkur ya dago Yana kallan daddy,,yace daddy Zan iya,,, goyan bayanku kawai nake buqata.. Kaji ko Alhaji shiyasa nake gayama yaran nan bashida lafiya Dan Allah mukaishi hospital aduba lafiyarshi,,yaro shekara 34 amma baya San aure mummy tafada tana kallan Daddy.. Mummy lafiya na qalau,,namiki alqawarin auren yarinyar da kikeso,,mummy kinsani nima inasan Yasmeen sedai ina tsoran halinta Na kyamar talaka,,nikuma gashi Allah ya hadani dasu. Hadiye kukan nijlah tayi tana kallan mashkur daga inda take tace kambu kana sontafa kace" ara ta kaddani bamemin kishiya daga zuwana,, tana gama fada ta cigaba da kukanta .. Ba mashkur ba ita kanta mummy saida tayi mamakin nijlah.. Ke Dan ubanki harkinsan wani Abu wai Kishi,,turo baki nijlah tayi tace,, Aidai malaminmu yace ba kyau zagi kuma duk Wanda ya zagi wani kan....ke rufemana baki bakida kunya,, wannan fa mahaifiyatace mashkur ya fada,, idan tana Magana kiriqa yin shiru,,Ko bakiga yadda nake ba??? Ahankali nijlah tace nagani. Ah ah ka Barta ta nuna mana halinta kafin ka fice a gidan,kinci sa'a mummy ta hanani tabaki da yanzu kingane dawa kike shegiya 'yar sadaka.. Runtse ido mashkur yayi kafin ya bude a hankali yace haba aunty lateefah,,zaro ido lateefah tayi tana kallan mummy.. Barshi lateefah,ki barshi ta gama zagina tinda Shima ya nuna ta fini daraja agurinsa.. Mummy ba haka bane kiyi hakuri,, Daddy ne yace,kaga mashkur Tashi kaje daki da ita anjima zanyi Magana dakai.. Har mashkur ya Tashi yaji daddy Na cewa.. Taci abinci kuwa?? Badai a gidana ba,, wallahi ko ruwa bazata shaba.. Girgiza kai daddy yayi yana kallan mashkur.. Kafin yace,, Mashkur zaka iya zama da matarka a saban gidana. Kanshi a qasa yace eh daddy.. Daddy be qara Magana ba ya shiga dakinsa,, cikin minti biyu ya fito da key a hannunsa,, mashkur ya miqawa Yana murmushi.. Hannun mashkur Na karkarwa ya amsa,,daddy nagode,,karka damu Dana duk abinda kake buqata ka sanar Dani,,harya fara tafiya ya juyo yace.. Ka kula da yarinyar mutane.. To yace a hankali Yana kallan mummy data hade fuska tana tinanin abinyi. Tashi yayi hannunsa Na karkarwa ya kama hannun nijlah ya miqar suka fara tafiya.. Karka sake bakina ya furta kalma mara Dadi akanka,,bazan zuba ido ka tare da wannan yarinyar ba,,tsayawa mashkur yayi yana sauraran mummy yaji daddy yace.. Kaje abinka Nina baka umarni. Daddy na gama fada ya fito a falon,,Mota ya dauka zuciyansa na quna ya tafi gurin mahaifin Yasmeen.. Tinda Yasmeen ta fito take sharara gudu a titi tana driving tana kuka akaha harta kai gida,,a fAlo ta Sami mama sedai bata Biya ta kantaba ta shiga dakinta da gudu hannunta aka,, Kan gadonta ta fada tana kuka tare dajin mahaukacin Kishin mashkur Na taso Mata.. Wacece wannan taji ana Magana da Wanda takesa ran yazama mijinta nan da wata biyu kachal,,idan ko San mashkur take tabbas itace ajalin ta. Tana cikin tinani taji mama Na Magana akanta,,ke Yasmeen lafiya kika dawo Kina kuka badai wani abu ya samu mashkur ba.. Da gudu Yasmeen ta Tashi ta fada jikin mama tana cewa mama,, Watace watace,,kimin magana kin zauna Sai Kiran wata kike,,kodai mutuwa yayi,, girgiza kai Yasmeen tayi tana cigaba da kuka,,to kodai cewa yayi yafasa aurenki???? Comments &share Momn sultan ce 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *HANNATU GALADIMA...* *Dan Allah aqara yawan pages,Dan Allah aqara yawan pages,,,Kalmar da mutane dayawa Ke ambato batare da sun tambaya abinda Ke hanani typing dayawa ba,,kusani Nida kaina Ina ganin qoqarina,,Duba da ayyukan dake gabana Amma natsaya Ina farantamuku Rai Duk Dan kuji Dadi..* *Dan Allah masu kirana a waya kusan irin abinda zaku gayamin Ko tambayana,,niba Matan aure nake fadakarwaba,,sedai Ina rubuta labari Wanda Zaki dauki darasin Zaman takewar aure da al'umma tare da gyara kuskuren da muke aikatawa,,masu min chogen Kira Dan Allah kudena kibari saikin cika waya da kudi kafin ki Kirani,,momn sultan data kawai take ajiyewa a waya Bana ajiye kudin kiranku,, nagode* 2⃣3⃣&2⃣4⃣ Cikin kuka Yasmeen ta Bude baki da kyar tana Magana" Mama mashkur ne ya kawo wata gidansu Sai kuka ya qara zuwa Mata takasa qarasa,,nan da nan hankalin mummy yaqara Tashi,,jikinta ta janyo Yasmeen tana gogemata hawaye.. Kinga Yasmeen kibude baki kigayamin abinda Ke faruwa kafin abbanki dayawo ya safkemin kwandan masifa akaina.. Mekika ji a gidan Basu?Ko Wani ya gayamiki Magana mara Dadi?? Mama ba haka bane,,tinda naje gidan Naga hankalinsu a tashe musamman ma Shi mashkur,,mama Seda daddynsu ya dawo mummy tace Wai kirana tayi koni zefi gayamin gaskiyar Magana,,Sai kuma tayi Shiru takasa qarasawa Jin Wani qatan Abu ya maqale Mata a maqogoto.. Gaskiyar Magana akan me??mama ta tambaya tana kallan yadda Yasmeen Ke qoqarin hadiye saliva yaqi tafiya sabida tsabar kishi.. Dasauri mama ta Bude fridge ta dauko Goran ruwa tafara ba Yasmeen,,Dan kadan Tasha sabida dacin dataji yayi Mata a baki ta kauda kai Ranta a bace.. Inajinki Yasmeen cigaba da Magana,,gaskiyar Magana Akan wa??? Mama Wai Akan aljanar yarinya,,Sai kuma ta fashe da kuka tana cewa,, wallahi mama banasan kowa ya kusanci mashkur menene hadinsa da wata Har mummy takesan yafadi gaskiya,,mummy Ina tsoran kada wata tace tana sanshi Dan wallahi Bazan Iya Bude Ido Naga mashkur da wata mace a matsayin budurwa ba... Ajiyar zuciya mama ta safke tana kallan yadda Yasmeen ta birkice Mata tana sumnatu,, girgiza kai tayi tana mamakin irin wannan mahaukacin Kishi da Yasmeen take Akan mashkur Duk da itama tasan soyayyar dake tsakaninsu,,Amma be kamata ta riqa irin wannan Kishin ba,,Dan kuwa namiji mijin mace hudu ne.. Gyara Zama tayi ta janye Yasmeen a jikinta tare da gyara Mata Zama ta yadda zasu fuskanci juna,, muryar mama a shaqe tace" Yasmeen,, Yasmeen Bata Iya amsawa ba Saima safke Kanta qasa datayi sabida yadda yake saramata,,cigaba da Magana mama tayi tana shafa Kanta.. Yasmeen kefa 'ya mace ne,,bekamata kina Abu irin na jahilan Mata ba,,Ko haka kikaga inayi agidanan,,kasa Magana Yasmeen tayi Saima turo Dan qaramin bakinta gaba tayi .. Nan mama tacigaba da magana saunawa kike ganin manyan Mata Suna zuwa gidannan mahaifinsu Yana Duba lafiyarsu? Shiru tayi mama ta daka Mata tsawa,,waiba dake nake Magana

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46