Chapter 36
Chapter 36
jikinta' kinga Yasmeen ki tashi ki goge wannan hawayen' indai mashkur ne gashican Yana jiranki a falo.. Dan Allah mama da gaske? Kinci gidanku ina Miki karyane? Dariya Yasmeen tayi tana goge hawayen fuskanta ta tashi ta fada toilet,,tana Shiga mama ta fito tana cewa gatanan zuwa tana can tana shirmen nata. Murmushi mashkur yayi yakasa amsawa' har mama takai qofa ta dawo tana cewa'kaga munata magana ban tambaya su mummy ba? Murmushi mashkur yayi Yana cewa'suna lafiya tace a gaisheki To alhmdllh mama ta fada tana Shiga daki. Sosai Yasmeen ta zauna ta tsara kwalliya tare da saka wasu Kaya masu shegen kyau turaruka ta feshe jikinta dasu kafin ta fito tana taku cikin nutsuwa Dan Yasmeen badaga nan ba gurin iya daukar wanka da kalamai masu dadi shiyasa ko sun Sami sabani da mashkur bata Shan wahala gurin janye hankalinsa har yaji ya hakura.. Tinda ta fito ya zuba Mata Ido Yana Yaba kyan surarta' a haka harta qaraso kusa dashi' Jitayi kama ta rungumeshi sedai bazata iya hakan ba nan ta zauna Kan hannun kujeran da mashkur ke zaune tana kashe masa ido' a hankali tasa hannu ta zagaye jikin kujeran tare da kwantar da kanta Kan hannun kujeran daidai inda hannunsa ke Kai. Ido ya zuba Mata Yana zancen zuci' wai me yarinyarnan take nufi kadafa ta susutani sabida alokacin yafara Jin wani irin Abu na tsirgawa a cikin jikinshi.. Baby fishi kake dani? Kallanta mashkur yayi Yana girgiza mata Mai Yana kallanta cike da soyayya' to Amma shine zaka sani kuka,,yanzu Dana hadiye zuciya na mutu ya zakayi? Hakan ma baze taba faruwa ba,,sedai yanzu kema kin chanza Hali shiyasa Nima nakesan chanza nawa kema kiji inda dadi. Baby ni kuma me nayi? Au Bama ki sani ba' ko? To kayi hakuri bazan qaraba' Kallanta kawai yake Yana mamakin shagwabanta,,da kyar ya bude baki Yana magana Yana kallanta" Allah yasa' Da ameen Yasmeen ta amsa tana qara narke masa. Babu Wanda ya qara magana kusan minti guda daga Baya Yasmeen tace' Baby wai har lokacin biki yayi? Ni gaskiya sonake adan qara lokaci kaga' Kinga dakata banasan wannan shirmen zancen naki,,sai ana magana na arziqi saiki tsiro da shirme, wanne irin daga biki? Nan fa mashkur ya rikice Mata Yana fada a cikin nutsuwa tare da Nuna Mata bacin ransa. Murmushi Yasmeen tayi tana dariya tare da yimasa gwalo tace' yeeeeee naji ta bakinsa,,Dama sonake naji kadena dokin bikinmu ko haryanzu kanayi? Ba qaramin sanyi mashkur yaji ba Dan yau har saida yakai hannu da niyyan bigeta ta goce,,daganan suka cigaba da hira,, mashkur be bar gidansu Yasmeen ba sai bayan sallar magrib yamata sallama ya tafi gidan abokinsa jabeer.... Tinda nijlah ta kwanta bacci ya gagara daukanta Banda juyi babu abinda take,,tin tanajin ciwo kadan kadan harta fara riqe cikinta tana yamutsa fuska,, ahankali a hankali ciwon ya riqa sauka a cikinta tare da riqemata bayanta da mara,,tin tana kuka a hankali harta fara me sauti tana Kiran sunan Allah.. A haka bacci yadan fara daukanta,,tana cikin bacci taji fitsari me shegen zafi na damunta' dakyar nijlah ta tashi zaune tanasan Shiga toilet sedai wani abun mamaki qafan yaqi daguwa ga wani irin ciwo dake damunta'Banda kuka tana kallan kofa babu abinda nijlah take.. Dakyar ta iya safka da rarrafe ta sauko akan gadon tana kuka ta rarrafa ta Shiga toilet.. Mummy dake zaune a falo tana kallo yayinda Maryam me aiki ke tsaye a kitchen tana fere doya taji suka ji kukan nijlah' tsaki mummy tayi tana kwana Kiran Maryam" Maryam ke Maryam kina ina zoki budemin dakin wannan shegiyar yarinyar Naga abinda take,,aini bansan tana gidanba nake zaune a falo,,to Allah ya kareni daga daukan Corona virus a jikinta,,nasan babu inda qafanta be kaiba' dariya Maryam ta gumtse tana tsoran Kada tayi mummy ta hauta da fada... Dagowa mummy tayi taga Maryam tsaye tana sunne Kai' Ke kuma ya haka zaki tsayamin aka saikace mara hankali' Dasauri Maryam tayi qasa da Kai tana cewa mummy kiyi hakuri.. Niba wannan na tambayeki ba,,jeki duba dakin auta kiga me wannan yarinyar takewa kuka Kada muna nan zaune ta hadamana gobara bamu sani ba,,kafin mummy ta qarasa magana nijlah ta saki wani wahalallan ihu tana Kiran Kaka.. Da gudu Maryam ta qarasa dakin tana cewa ke kina ina' Nijlah da qarasawanta toilet kenan ta cire pant da niyyan zatayi fitsari taga jini nabin jikinta pant dinta yayi kaca kaca da jini gashi jinin hadda guda guda.. Wayyo Allah na jama'a Ku taimakamin wallahi Bari nake. Dasauri Maryam ta Shiga toilet tana janyo nijlah jikinta,,jinin data gani ne yasata sakin salati tana cewa' ke dama cikine dake? Eh wallahi Dan Allah ki taimakamin Bari nake nijlah ta fada a galabaice Dan zuwa yanzu magana ma a hankali takeyinta. Mummy dake zaune taji nijlah na ambatar bari' bata Ida tsinkewa ba Saida taji Maryam na cewa Dama ciki gareki?mummy bata jira Jin amsar da nijlah Zata ba Maryam ba ta miqe tsaye tana tafa hannu tare da sakin kuka tana cewa....... Kuyi hakuri inada mara lafiya shiyasa kukaji Shiru... Comment & share *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN MUHMUD...* 5⃣4⃣&5⃣5⃣ Cikin kuka da tashin hankali mummy ke magana"Shikenan auta kajamana abun kunya' mezan gani a gidana ni hauwa? Da gudu ta qarasa dakin mashkur Bako sallama tana surutai marasa Kan gado.ita ta manta da ciwan kafanta sabida tsabar tashin hankali datake ciki. Maryam ko ta duqufa gurin yiwa nijlah sannu tare da qoqarin yadda Zata gyara Mata jiki,,sedai duk yadda maryam taso taba nijlah' nijlah taqi bata dama.. Banda kuka da Kiran Kaka babu abinda nijlah take tana riqe mara yayinda taqi Bari Maryam ta taimaka Mata. Mummy na zuwa ta fara bin jikin nijlah da kallo tana hawaye' turus tayi ganin jinin dake bin kafan nijlah" haushine ya kama mummy tayi kukan kura ta chafki wuyanta tare da zubamata rankwashi akai' Dan ubanki haka Ake Bari zaki dagamin hankali,shegiyar yarinyar kawai me suffar aljanu. Turo Baki nijlah tayi,,cikin kuka tafara magana,Allah Baba Bari nayi ki tambaya kado ai dai yace Nima Zan haihu gashi kuma cikin ya zube ta fada tana sakin wani kuka danma zuwa yanzu ciwan maran yafara sakinta. Saketa mummy tayi tana tsaki' aikin banza yarinya qarama dako kanta bata Gama sani ba yaje ya daukowa mutane wahala,,to wallahi zanga me gyara Miki jiki a gidan nan sedai ki rufe a haka,,Nina godema Allah dayasa bakimin wannan qazantar a falo ba.. Kuka nijlah tasa tana cewa" Dan Baba ki wankemin wallahi bazan iyaba. Ke Maryam tashi kifita anan kije ki cigaba da aikin Dana saki' Maryam da karkarwa tace to mummy' Nan ta fita tana tausan nijlah sedai bata da yadda zatayi,,tana fita ta fada kitchen ta cigaba da aikin ta.. Maryam na fita mummy ta maida hankalinta ga nijlah tana cewa' to ke kuma me Bari saiki jira Wanda yamiki cikin yadawo kinga Saiya wanke miki,, kafin nijlah tayi magana mummy ta fita tana murmushi. Falo ta dawo ta zauna Kan kujera ta dora qafa daya Kan daya tana dariya Saida tayi me isarta kafin tace' hmmmm gaskiya yaro yarone Banda haka ina wannan yarinyar ta isa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46