Chapter 21
Chapter 21
lateefah kenan,,wannan har a kirashi da aure sedai ko muce wasan yara,,Kinga ni kawai ki kirashi Dan wallahi idan na Kira wannan aljanar ta dauka saina kusa kasheta a gidannan.. Waya lateefah ta dauka ta Kira layin mashkur.. Nijlah dake zaune agurin tana zubda hawaye tare da tinanin matakin da mashkur ze dauka akanta idan yaji ta amsa masa waya har tayi magana mara dadi taji waya na ringing a hannunta.. Kuka ta qara saki tana cewa,,dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan banbane ya kiraba,nayi tinanin yarinyane Irina,,kuma ai ke kika fara zagina,,da gudu nijlah tafara zagaye dakin tana kuka tare da wayar mashkur a hannnunta Sai ringing take.. Mashkur besan abinda akeba sabida baccin dake idanta,,ga bayansa Sai ciwo yake,,Dan tinda yake be taba aikin wankin kashi ko wani aiki me yawa irin Na Daren jiyaba,,Yana cikin baccin yaji kukan nijlah tare da ringing wayarsa a lokaci guda.. A firgice ya Tashi Yana lalubar inda take kwance Dan a tinaninsa fadowa tayi daga kan gadon.. Idansa a rufe yake laluba ko ina Na gadon har saida yaji hannunsa yakai qasa bejita ba,, Sannan yayi saurin bude idonsa.. Can quryar daki ya ganta ta hade kai da gwaiwa tana kuka ga waya rungume a jikinta,, dafe kansa yayi Yana addua Tashi a bacci kafin yayi qoqarin yinqurawa ya tashi,,a hankali ya diro qafafunsa har yayi nasaran ajiyesu a qasa.. Kusa da ita ya qarasa Yana tinanin abinda yasata kuka.. Hannu biyu yasa ya ruqe hannunta Yana Magana a hankali,,amarya meya sameki kike irin wannan kukan ko yinwa kikeji? A firgice nijlah ta Dago tana kallansa,,kafin ta saki wani saban kukan tana yarfa hannu,,Dan Allah kayi hakuri wallahi banzagetaba,Allah bana zagi ban ma iyaba.. Ke ki nutsu mana nifa banma gane abinda kike Gaya ba,,wakika zaga? Wallahi banzagetaba Kaji Na rantse,,ni Dai ka mayar Dani kauye gurin kaka,,bazan iya zama anan ba.. Jinjigata ya rigayi har saida tayi shiru yana shafa bayanta tare da tofa Mata adduoi Dan a tinaninsa mafarki tayi.. Mummy kinga abinda nake gayamiki ko,,ninasan baze dauka wayana ba,, ahankali mummy tace ki qara Kira mu gani.. Number aunty Lateefah ta qara dealing akaro na barkatai. na cikin yimata addua yaji waya Na ringing,,hannu yakai ze amsa taqi bashi tana kuka tana girgiza masa Mai.. Kibani nace,,ko bakiji ana kirana ba,,cikin kuka nijlah tace wallahi ban zagetaba,,ai Bata Ida Magana ba yayi saurin fizge wayar a hannunta.. Hello aunty lateefah,,ba wani aunty lateefah dazaka kirani ka kirani sa lateefah Kawai mara mutunchi,,kana kallo matarka ta zage mana uwa amma kai ko ajikinka baccinkama kake ko mashkur.. Kallan Nijlah yayi da tinda ya amsa wayar ta Tashi da gudu tayi bakin kofa hannunta biyu aka tana kuka.. Tokazo yanzun nan mummy tanasan Magana dakai,,bakinsa na rawa yace gani nan gani nan.. Yana gamawa ya Tashi a fusace yayi kan nijlah,,ai kafin ya qarasa inda take harta zube a qasa tana birgima tana bashi hakuri.. Dan Allah kayi hakuri Handi mu bani,,bazan qaraba Na tuba Dan Allah kada ka dakeni kukan da nijlah ta riqayi Kenan tana ihu.. Hannu biyu ya sarqe a qirjinsa Yana binta da kallo,, yama rasa hukuncin daze yanke akanta,,dukanta zeyi kome,,to idan ma Na daketa ba hucewa zanyi ba,,inaga amfanin dukan.. Karka daketa wata zuciyar ta fada masa kayi mata nasiha shine abinda ze shirya maka nijlah Dan da gani Bata Jin Magana.. Bebi ta kantaba ya fada toilet,,wanka yayi ya fito Yana kallanta a inda ya Barta Sai birgima take kai kace dukanta yayi.. Wardrobe ya bude ya dauko faran shadda,,cikin mintina kadan ya shirya,,wayarsa ya dauka yayi hanyar fita,,da gudu nijlah ta Tashi zata fita ya daka Mata tsawa.. Ke wallahi ki kiyayeni koni sa'ankine,,Bayan aikin kashin dakika sani saikin sakamin da wani tashin hankali ko nijlah,,ina hankalinki da wayanki suke,,to wallahi ki fita a idona.. Safke kai qasa nijlah tayi tana bashi hakuri harya gama ya fita ya Kuma kulleta ta baya.. Cikin sauri ya dauka Mota ya tafi,, restaurant ya shiga ya siyo Mata wainar shinkafa da miya ko noma be bari ansaba ya hadamata da kunun Madara me sanyi.. Dasauri ya koma gidan ya bude dakin da take ya ajiyemata kayan abincin,,gashinan ki Tashi kici kafin naje wani guri yanzu Zan dawo,,idan Kuma naji abinda kika aikata ba daidaiba saina Saba Miki.. Daga haka ya fito sedai wannan Karan be rufe ta a dakin ba,,Yana zuwa bakin get ya Kalla baba Mai gadi yace.. Baba ka tsaya akan aikinka akwai yarinya ciki,,Dan Allah karka bari ta fita,,idan Kuma ka bari wani abu ya sameta nida kaine.. to ranka ya dade cewar get man Yana gyara Zaman hularsa.. Tinda mashkur ya fito gabansa me cigaba da faduwa ahaka har ya iso gida.. A fAlo ya Sami mummy zaune ta hada kai da gwaiwa,,kusa da ita mashkur ya zaune Yana hada hannunsa.. Pls sweet mom Dan Allah kidena irin wannan tinanin,,ki dauka qaddaran da Allah ya dorawa danki,,mummy kinsani banida burun auren wata Diya mace Bayan Yasmeen,, wannan aure daga Allah yake.. Kai rufemin baki,,kana so ka gayamin Shima zagin da kabata waya tayimin daga Allah ne?? Mummy zagi kuma? Au tambaya kake,, mummy kinji shiko,,wai mu zeyiwa barikanchi,,ki rabu dashi lateefah ni wallahi gani nake kama chanzamin Shi sukayi.. Fuskar mashkur mummy ta riqa shafawa wai a tinaninta wanine suka samishi fuskar mashkur,,Babu abinda ta Ciro Dan haka tasa kuka tana cewa shine,,wallahi shine lateefah.. Dakyar mashkur ya iya hadiye saliva bakinshi,,muryanshi Na rawa yace,,pls aunty lateefah karki hadani da mummy,,kema kinsani bazan taba Bada waya a zagi mummy naba.. Kuma nijlah Bata iya zagiba,,tana da tarbiyya,,tassss tassss lateefah ta dauke mashkur da Mari tana nunashi da yatsa.. Kana nufin Karya mummy tayiwa nijlah kome,, Tafe kunchinsa mashkur yayi ya kasa magana,lokaci guda hawaye suka wanke masa fuska.. Ita kanta mummy taji Marin sedai bazata iya hanawa ba sabida komai akayi Dan ita ake masa.. Yanzu ina ita nijlah take,,mummy ta tambaya a hankali.. Yana hawaye yace,,tana gida,,wanne gidan qin Bata amsa yayi sabida Yana tsaran kada suje su daketa danyaga alamar Hakan,,tinda Shima Basu barshi ba.. Wai ba tambayarka bakeba ba auta?? Mummy tana gidan abokina ya tsinchi kansa da yimata Karya.. Toka tafi yanzu yanzu inasan Magana daku gaba daya,,kaga gobe auntynka zata bar qasar,,yayanku Shi ya tafi tin safe.. To yace ya Tashi Yana tafiya Yana hada hanya.. Seda yayi hanyar saban gida yaji qaran wayarsa.. Zuciyarsa Na tafasa ya duba number me Kiran,,abban Yasmeen ne.. Nan ya samu guri yayi parking kafin ya daga wayar zuciyarsa na cigaba da halbawa Dan idan akwai abinda ya tsana be wuci a rabashi da Yasmeen ba.. Yana dauka abban yace,, mashkur kana lafiya,,bakinsa Narawa yace lafiya qlau Abba.. Kafin mashkur yaqara Magana Abba yace.. Naji duk abinda yafaru sedai hakan dakayi ya nuna mana kai ka hakura sa auren Yasmeen,,Dan haka nakeso kazo yanzu gidana inasan Magana dakai,,idan an gama komai saika amsa kudinka ka tafi,,nafasa baka Yasmeen.. Wayyo kukane kawai mashkur beba Shima saida yayi na zuci,,ga wani irin faduwa da gabansa yake jiyake kama zuciyarsa zata tsage biyu tabar gangan jikinsa.. Abba dan Allah kayi hakuri bazan iya rabuwa da Yasmeen ba,,ta zama ni nazama ita wallahi Abba badaga ni bane,,haka Allah ya qaddara,,Abba zan riqe Yasmeen amana,,Abba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46