Chapter 34
Chapter 34
dazan dawo shine Na biya Na taho da ita Ko nijlah mashkur ya qare maganar cikin bugawar zuciya da zillimin Baran baramar da nijlah zata Iya yimasa.. Dasauri nijlah tashiga Daga kai tana cewa eh. Kaga auta banisan qarya? Cike da shagwaba Mashkur ya fada jikin mummy Yana cewa' Toba ga yarinyar nan tsayeba Ai saiki tamabayeta" to to shikenan yanzu a Ina kuka tsaya Kan batin shagalin bikin? Dariya mashkur yayi Yana Kallan nijlah da tinda ya ambaci aurensa ta hadiye kukan tana kallansa" nan ya kashe Mata Ido Yana cewa' Ai mummy ki kwantar da Hankalinki Dan munriga mungama Hada komai kedai kawai ki jira lokaci.. Dariyar farin ciki mummy tayi tana shafa Kan mashkur tace' Yau Dan albarka kaga shikenan Nima zanga auren auta Na" sosaima yafada Yana janye jikinsa. Mummy nizan Shiga daki inasan watsa ruwa a jikina' Yana dakyau Ai,,Amma Dai Idan ka shirya gurin mutuniyar zakaje? Sosa kai mashkur yayi Yana cewa' eh Mummy Shiru nijlah tayi tare tare da yin tsuru tsuru da Ido tana kallansu daya Bayan daya yayinda hawaye suka riqa zirya a idonta,, ganin yadda gaba daya mashkur ya manta da ita tsaye Saima maganar aurensa yake,, To waima yaushe aka bashi aurena dahar yafara maganar Wani auren? Nijlah ta tambaya Kanta.. Sedai abinda Bata Sani ba shine" Duk abinda mashkur yake Yana kallanta tare dajin matsanancin tausanta bashida yadda zeyi shiyasa ya zuba ido akemata yadda akaso.. Mashkur Na satar kallan nijlah ya fita a Dakin Yana addu'a Allah yasa nijlah ta biyo bayansa,, harya fita Beji alaman tahowantana Dan haka ya tsaya Daga kofa Yana leqenta... Nijlah Na ganin tafiyan mashkur ta Daga qafa a hankali tanasan binshi Taji mummy tace"dawo Nace,, Dan ubanki Ina Zaki bishi? Muryar nijlah Na rawa tace" uhmn Zan" Uhmn uhmn me" wato Kan ansaba bin Maza a gindi a gandi kuna yawo da shanu shine Zaki bishi kuyi wankan tare Ko? Shiru nijlah tayi tana wasa da hannunta.. Kibani amsa" nasan Dai babu abinda Zaki Iya a bed dadai yawan jejeni nasan anan kikafi kauri.. Tsuru tsuru nijlah tayi tana tsoran kada mummy ta doketa,,bakinta Na rawa tace" Dan Allah baba kiyi hakuri Bazan qaraba" Ah ah Wallahi Zaki qara,,indai shawan jejine Dan baki Samu gurin Zama anan ba.. Ita Dai nijlah Bata qara Magana ba Banda rawa Babu abinda jikinta yake" akankali Takai kallanta ga kofa Aiko taci sa'a idanta ya safka Kanna mashkur" hannu yasa ya yaficeta dashi tare da yimata alamar Kira.. Aida sauri nijlah tayi hanyar fita tana tafiya tana Hada hanya. Ke dawo Dan ubanki Ina zakije" hannu yasa ya rufe bakinsa Yana Mata alama da kada tayi magana nan itama tasa hannu ta rufe bakinta tana kuka a hankali" Duk abinda mashkur yake daddy Na tsaye a bayansa sedai yarasa abinda yakewa hakan danshi ba cikin Dakin yake kallo ba" hakanan jikin mashkur ya dauki rawa nan daddy yasa hannu ya janyeshi Daga jikin qofar ya Kuma sa kai ciki.. Mummy bataji zuwan daddy ba ta shigaba da zazzaga Mata masifa" sabida Ke mayyace kinkasa gane cewa ba'a sanki,,Sai liqewa yaro kike Yana guduwa,,Ni wallahi naso ace mutuwa kikayi da tinin Na huta da damuwa.. Tana leqewa yaranki Koshi Yana liqe Mata" kinga hajiya ki kiyayi kanki" Idan baso kike rabo ya kasheki ba daddy ya fada cikin daure fuska,, Kina nan kinsa masa Mata gaba kinacin zarafi Shi Kuma ya labe Yana Kiran matarsa Amma sabida tsabar San zuciya kinkasa ganewa.. Tabe baki mummy tayi tana cewa' to Wai Alhaji me nayi kawai sabida Na hanata zuwa dakinsa saika hauni da fada,,Ko Dai sokake gaba daya yarinyarnan ta tare masa a Daki Sai Abu mara Dadi yafaru azo ana zance da karkata kai? Nauyayyen ajiyar zuciya daddy ya safke Yana cewa'wanne irin Abu mara Dadi?Naga Dai matarsace ta Sunna Dan haka kibarsu suyi rayuwarsu yadda sukeso.. Hhhhhh wacce irin rayuwace za'ayi da wannan jaririyar yarinyar Ko bakaga yadda take ba" Ni wallahi bansan meyasa auta ya kwaso wannan ba,, ka dubetafa kama an daura muciya zani. Ke Tashi kije gurin mijinki,aikinsan Dakin nasa Ko? A hankali nijlah ta Daga kai Duk Da batasan ta inda zata fara neman Dakin mashkur ba. Jeki can Yana jiranki' nijlah Bata qara Magana ba ta fita da gudu tana waiwayen mummy" Harara mummy ta riqa binta dashi Har Saida nijlah ta nacewa ganinta... Kusan Cin Karo nijlah tayi da mashkur Dan tinda yaga tahowanta ya Bude Mata hannu Yana jiran zuwanta" Kamar tasan abinda yake nufi ta fada faffadan qirjinsa tana safke ajiyar zuciya. Nan ya riqa shafa bayanta Yana hura Mata iska a kunne" kiyi hakuri kinji nijlah ta,,komai yayi farko zaiyi karshe,,anjima zanje gurin abokina Naji yadda zamu bullowa lamarin.. To tace tana kuma tana qara shigewa jikinshi" ahaka har suka Shiga dakinsa nan yasa key ya rufe kofan ya kwantar da ita Kan hado Yana Mata sannu' Nijlah bata iya amsawa ba sai lumshe ido take tana kuma busheshi" ganin haka yasa mashkur tashi ya fada toilet.. Bayan yayi wanka itama ya hadamata nan ya dawo Yana kallan yadda ta harde kafa tana tinani" Kobe tambaya ba yasan abinda take tinani Dan haka yasa hannu biyu ya ciccibeta Yana cewa' Muje kiyi wanka ko kya dena warin asibiti' turo Baki nijlah tayi tana cewa Allah Bana wari sedai Kaine kakeyi. Kece dai kike nida ban kwana a gadon asibiti ba" dariya nijlah tayi mara sauti tace' Naga dai tare Muka kwana katina har kana shamin nan tafada tana Nuna boob's dinta" murmushi mashkur yayi yakai hannu Yana qara shafasu tare da cewa' ni yanzuma idan zaki Bani sonake Dama naji daddy Yana Miki huduba tazu ko ke Baki gane abinda yake nufi ba?? Dukan Wasa takai masa tana cewa ni Allah banaso Nika Bari,,kuma yau hadda kaina zaka wankemin kaga yayi datti,,tafada tana shafa yalolan gashinan kanta daya kwanta kama babu komai.. Shima hannu yasa Yana shafawa yace'saloon Zan kaiki acan Ake gyaran kai" Dan gaskiya niban iyaba. Kai kado kuma Ka iya wanka,, Naga Kaka harda wankin Kai take yimin? To idanma Baka iyaba nizan koyama.. Ah inye yarinyar dako wanka bata iyaba shine Zata koyamin wankin Kai? Rufe fuska nijlah tayi tana boyewa a jikinsa tace' ai dai yanzu na iya Kaine Baka Bani.. To so shikenan yanzu saiki tashi mu Shiga toilet ga ruwan wankanki can anan Zan gane kin iya ko Baki iyaba. Ba musu nijlah ta tashi suka fada toilet" brush yabata tayi,,Saida ta Gama yabata sosa da sabulu ya koma gefe Yana kallanta. Sosai nijlah tayi wanka takuma fita tanayi tana dariya tana cewa kado na iya ko? Eh babu laifi bayankine da kawai Baki iya wankewa ba kinga ko Baki iyaba" kukan shagwaba ta saki masa tana cewa ni Allah na iya aidai kaima Baka iya wanke nakaba.. Yana dariya Yana tsokalanta yaqarasa Mata wankan suka fito.. Kado nizan shafa Mai da kaina kaji Dan birni? Naji' Amma daga yau kada naqarajin kin kirani da kado kinaji ko? Turo Baki nijlah tayi yasa hannu ya doke bakin Yana cewa Bana hanaki wannan abun ba.. A hankali nijlah tace mantawa nayi" kuma Baka gayamin sunan dazan kiraka dashiba,,kaga mu a ruga Mai gida Ake cewa ko malam. Toni ba malam
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46