Skip to content

Chapter 13

Chapter 13

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,285 words 0 views Progress saved
Download Book

zauna tace ina yini,,lafiya qalau suka amsa kafin mummy tace.. Ke lateefah jekice yazo yanzu kafin ranshi ya baci,,kafin lateefah ta Tashi mashkur ya qaraso falon,,nan idansa ya safka kan Na Yasmeen Wanda tayi mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin.. Murmushi yamata tare da kashe Mata ido,,duk da yadda zuciyarta ke halbawa saida ta mayar masa na martani,,bakinta a bude a hankali tace lvu.. Kusa da mummy ya zauna Yana niyyan kwantar da kansa jikinta tayi saurin tureshi tana hararanshi,,karka soma wallahi,,shiru yayi yace,,ke kuma daga ina mashkur ya tambaya Yana kallan Yasmeen.. Kafin Yasmeen tayi Magana mummy tace,,Nina sa akiramin ita,,inaga zata fini sanin gaskiyar Magana akan wancan aljanar yarinyar.. Dasauri Yasmeen ta daga kai tana satar kallan mummy,,gabanta Na cigaba da faduwa tace,, Mashkur wacce yarinya ake Magana,,Dan Allah kada ka hada soyayyana da wata ta qare maganar hawaye cike a idanta.. Daddy dake shigowa ya bisu da kallo Yana mamakin abinda yasa gidan nasa ya zama haka kama anyi mutuwa,,kusa sa mummy ya zauna Yana kallan mashkur,,kai kuma saukar yaushe,,kafin mashkur yayi Magana daddy ya qara wata tambayan? Hajiya bakuwa kukayi,,eh kawai mummy tace tana hararan mashkur, ka tambayi danka shize gayamaka ko wacece.. Qara yin qasa dakai Yasmeen tayi tana goge hawaye Dan ko Magana bazata iya ba.. Mashkur wacece wannan ya fada Yana nuna yasmeen.. Bakinsa Na rawa yace Yasmeen ce,,budurwata,,budurwarka,,wani abune ya faru Naga tana kuka,,shiru sukayi aka rasa Wanda ze yiwa daddy bayani.. Ganin haka yasa daddy kallan Yasmeen ya Kira sunanta. Bata iya amsawaba daddy yace Tashi kije gida nizan zo muyi magana da abbanku.. Da gudu Yasmeen ta fita tana kuka.. Tana fita daddy yahau mummy da fada,,haba hajiya akan me Kina kallo yaro ze kawo yarinya har gida bazaki tsawatarba,,Nina rasa meyasa kike daurewa yarannan gindi yake abinda yaga dama.. Daddy kayi hakuri Nima bansan da zuwan Yasmeen ba anan na ganta"kai mashkur har kanada bakin Magana,,daddy aure fa yarannan yayi ga matar can ya sata adaki cewan lateefah tana huci... Sake da baki daddy yace aure kuma,,aure wanne iri" saika tambayi danka cewar mummy.. Kai mashkur dagaskene abinda suke fada?? Bakin mashkur Na rawa yace" kayi hakuri daddy haka Allah ya qaddaramin badaga ni.... Kayimin shiru mutumin banza saida kasani tambayama aure sannan zakayimin shegan taka,,bada niyya nayi wannan auren ba,,kuma banyi Danna tozar taku ba,,daddy ka fahimceni.. Amma ko kayi wauta mashkur,mena rageka dashi,,koka taba kawomin abu kanaso na hanaka,,cike da nadama mashkur ya girgiza kai.. To meyasa kayimin haka,,da wanne ido Zan kalli iyayen wannan yarinyar? Shiru mashkur yayi Yana matsar ido nan ran daddy ya baci yayi kanshi da duka,,dasauri mummy ta tare tana girgiza masa kai,,kayi hakuri Alhaji,,ba laifinsa bane,,laifin mugayen mutanan ne dasuka daura masa auren ba saninmu.. Ran daddy a mugun bace yace,,idan su Basu sa hankali shibashi Shi,,ko zaman kansa yake,,daddy kayi hakuri wallahi ban na bata ranku nayi wannan auren ba,kada kuyi fishi dani.. Zama daddy yayi Yana kallan mashkur,,nan mashkur ya safke kashi qasa Yana sauraran daddy.. Mashkur ya akayi tayi wannan auren?? Ahankali mashkur ya bude baki Yana Magana,,daddy bantaba tinanin zanyi wani abu batare da saninkuba,,sedai Hakan yafaru bisa kaddara kuma wallahi bani na nema auren yarinyar ba,,sadaka aka bani.. What what Alhaji kanaji fa wai *yar sadaka* anyako Basu zautarmin da yaro ba? Wallahi mummy karki yadda saiya saketa ta koma Inda ta fito,,tsawa daddy ya daka lateefah Hakan yasa tayi shiru tana muzurai,,Yaya ko kasa Magana yayi Yana nazari... Mashkur ka tabbata maganar daka fada gaskiya ne,,eh daddy.. Idan har ka sake Na tambaya naji ba haka ba saina sabama,, dasauri mashkur yace eh Na yadda.. Shikenan yanzu ina yarinyar take,,daddy tana daki,,jeka kawomin ita.. Kambu,,ai wallahi bazata taba sabuwa ba,,wai Alhaji me kake nufi shikenan auren ya dauru" Kiyi hakuri haka Allah ya qaddara maganar lateefah kuma ba abin damuwa bane,,nizan yiwa iyayenta Magana Sai suma suyi hakuri adaura auren kinga yanzu 2 month ya rage ayi biki.. To ai shikenan amma ku sani daga kai har Dan naka,,wallahi sedai yazabi daya ko nijlah ko Yasmeen.. Mashkur dake zuwa falon nijlah Na biye dashi yaji abinda mummy ke fada nan yaji wani irin tashin hankali,,be iya jiran nijlah ba ya qarasa da sauri ya zube gaban mummy.. Mummy Dan Allah karkice zaki rabani da Yasmeen mummy badan bana santa nayi auren nan ba,,daddy kayi Magana"turesa mummy tayi tana daga murya tace.. Nasan bakinku daya to wallahi bazan taba karbar wannan auren ba,,ka rasa Wanda zaka auro Sai yar matsiyata kuma yar fulani.. Ran daddy bace Shima yace,,amma ko kinji kunya,,kuma ina nan ina jiran yadda zakiyi damu nida Dan nawa,, mashkur ka dauki matarka kuje,,ni Zan baka gida azauna.. Tsiru nijlah tayi tana binsu da ido taji daddy yace,,nace ka kawomin matar taka naji shiru.. Kafin mashkur yayi Magana nijlah ta washe baki tace baba gani' kallan Nijlah daddy yayi kafin ya maida kallansa ga mashkur....... *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *CLASSIC FEEDOR* *Ayi hakuri da rashin Jina Akan lokaci,,tare da rashin amsa comments naku,,haqiqa Naga comments Iya comments nakuma karanta,,Hakan ya nuna labarin Yana muku Dadi,,sedai Ina me gayama fans Na 'yar sadaka 2&3 daku gyara comments naku Idan ba haka ba........ nagode sosai da kaunarku gareni....🤝😍* 2⃣1⃣&2⃣2⃣ Bakinsa na rawa yace,, mashkur kana nufin wannan jaririyar ka aura??? Sosa kai mashkur yayi Yana kallan Nijlah da haushinta ya gama cikashi yace,,eh daddy itane dan Allah ka.... Ya isa mashkur Ashe dai bakada hankali nida nakeso kayi aure nima Na samu jika,,saika Tashi ka auro wannan yarinyar dako kanta bata gama sani ba,,dariya mummy tayi tana tafa hannu tace... Au kuma,,kai da kanka zaka gayi haka?? Tini zuciyar mashkur ta gama tsinkewa bamda halbawa Babu abinda take lokaci huda yaji hawaye na neman zubomasa amma saiya riqesu Yana kallan daddy yace ,, daddy Dan Allah kada kace ah ah,,daddy ka temaka mu inganta rayuwar nijlah,,wallahi bata da kowa.. Kai dallah rufemana baki,,kabari kawai daddy ya yanke hukunci aini nasan indai yaga wannan aljanar yarinyar dole yadawo bayanmu.. Kallan lateefah nijlah tayi tana turo baki,,doke Mata baki lateefah tayi tana cewa to mayya nidai kada ki cinyeni.. Dasauri mummy tace karki qara hada jiki da wannan yarinya kai kuma ka dauketa daga nan inasan Magana da mijina" Mummy kawai kiyi magananki wannan tatsitsiyar meta sani cewan Yaya Yana hararan mashkur.. Hawayen da mashkur ke dannewa sune suka Sami damar zubomasa,,kallan daddy yayi da ranshi ke bace yace.. Shikenan madogaran Dana jingina da ita,,ta Rushe,,wayyo Allah ni mashkur,, daddy ina kaunar dakuke ikirarin kuna yimin,,kunyi alqawarin San abinda nakeso daddy kaida kanka kakemin maganan tausayi da taimako gashi yanzu nayi kunjuyamin baya.. Tabe baki mummy tayi tana cewa,,haqiqa duk cikin yarana Babu Wanda nakejinshi a Raina sama dakai mashkur tafada tana nunashi,,bawai Dan bana sansu ba kona fi sanka akansu,,ah ah ba haka bane,,kawai dai inajinka fiye da kowannensu.. Kai shaidane amma duk da haka ka rufe ido kayimin abinda nafi tsana da qi arayuwana,,kodan kana ganin yanda nake shagwabaka har banasan bacin ranka,,toka sani akan wannan aljanar yarinyar nijlah take kowa,,Zan iya batawa dakai har zuwa lokacin dazaka mayar musu da tsiyarsu.. Qasa mashkur ya safke kai Yana goge hawaye nijlah

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46