Skip to content

Chapter 29

Chapter 29

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,236 words 0 views Progress saved
Download Book

sedai Yasmeen ta gagara amsa Koda guda dayane.. Tashi Abba yayi ya Bude fridge" Ruwa me sanyi ya dauko tare da cup ya zuba ruwan ciki" Da kansa ya Shiga Bata Yana shafa Kanta.. Yasmeen Bata Wani sha dayawaba ta janye fuskanta tana turo baki.. Yaya Dai 'yar Lele kigayamin kodai Wani ya tabamin Ke. Cike da shagwaba Yasmeen Tace" Ba mama bane hadda cewa zata dakeni" Kuma Shima mashkur tureni ya riqayi Yana min tsawa.. Hmmmm kinga abinda nake gayamiki Ko 'yar Lele Amma Duk Da haka kin Nace kince Sai Shi Zaki aura,,Bayan Yana nuna banbanci tsakaninki da 'yar sadaka. Cike da sangarta da shagwaba Yasmeen tace" Ni Ni fa Nina sanshi,,Kuma nasan daya aureni Ze hakura da ita.. To ai shikenan ita Kuma mama ki barni da ita,,tana ma Ina banji duriyartaba tinda Na shigo? Abba naji ta Kira mashkur Daga nan ta fita,,inaga asibiti taje Duba wannan shegiyar.. Jinjina kai Abba yayi Yana cewa' kinga Tashi kije kiyi wannan ki cire wannan kayan da suka baci da jini Ko baki gani ba" Sai yanzu Yasmeen taga jinin dake jikinta. Cike da kyankyami ta Tashi tana tafiya kama batasan taka qasa ta Shiga dakinta.. Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta Hada ruwa me dumi ta fada cikin bahun wankan tana ninqaya a ciki" ta jima tana wanke jikinta kafin ta fito,,Bayan tashafe jikinta da Mai tare da turaruka masu kamshi ta Bude wardrobe,,dugawar rigar ta dauka Na material green colour me tsarin orange.. Bayan ta gama shiryawa ta dauka waya ta Hau Kan bed ta fara karanta Daga cikin littattafan momn sultan.. Ahankali mama take tuqi gabanta Na tsanan ta faduwa,,ahaka harta kai hospital,,tana zuwa ta Kira mashkur daddy yasake dauka.. Na qaraso abinda mama tace cikin sanyin murya da kunya' Nan daddy yayi Mata kwatancen inda suke.. Bata Wani sha wahala ba ta ISA inda suke tana kallan mashkur dake kwance a cinyar daddy,,Har yanzu bai Dena kuka sedai zuwa yanzu ya rage kukan Sai ajiyar zuciya yake safkewa Akai Akai.. Kasa Magana mama tayi ta nemi gefensu ta tsaya tare da rungume hannunta a qirji tana addu'a" Har wurin karfe 4 na yamma likitoci Basu fito ba,,ganin haka yasa daddy daukan waya ya Kira mummy Yana San sanar da ita.. Mummy na Daki zaune Kan bed yayinda lateefah Ke dauke Kan carpet tana shirya kayanta cikin akwati Dan gobe da sassafe jirginsu Ze Tashi,,mummy Taji wayarta Na ringin.. Mummy daddyne Dan Allah Idan kin dauka kibashi hakuri kigayamasa gobe da safe Zan tafi,,nasan Idan yadawo ya ganni Allah fada zeyimun.. Keni da Allah Bani waya kada ya tsinke,,mummy Na Daga wayan daddy yace,,hajiya Bazan Samu dawowa da wuri ba" Ok,,Amma lafiya kace haka,,kaida kake dawowa da wuri? Nan daddy ya kwashe Duk abinda ya faru ya Gaya mummy,,ai be Ida zancen ba,,mummy ta tuntsire da dariya tare da tafa hannu tana cewa.. Kai Amma Yasmeen ta birgeni"toku me kuke a hospital tinda ance ta rasu Ai shikenan kaga Nima Na yadda kwallan mangwaro Na huta da Kuda.. Ran daddy a mugun bace ya daka mummy tsawa Wanda tasa mashkur firgita ya Tashi zaune,,kafin ya tambaya daddy abinda Ke faruwa sukaga Dr ya fito Yana goge gumin fuskansa,, Tsaki daddy ya ja tare da katse Kiran suka bi Bayan Dr.. Yana Shiga office daddy yabi bayansa mama da mashkur suka tsaya a tsaye Suna sauraran abinda dr Ke Gaya daddy.. Mashkur Najin dr yace,, nijlah Na buqatar jini ya saki murmushi tare da yin sujjada a qasa Yana godewa Allah' Be jira fitowan daddy ba ya dawo Dakin da aka kwantar da nijlah ya faki idon likitocin ya fada dasaurin gaske.. Yana Shiga ya tafi bakin gadon dasauri,,fuskanshi dauke da murmushi" Kallan yadda take bacci ya Shiga yi Yana murmushi,, ahankali ya kai hannunsa Kan lallausan gashinta ya Shiga shafawa ahankali ahankali tare lumshe idansa,Wani irin yana Mai wuyar misaltuwa ya ziyarci zuciyarsa,,tare da farin ciki na ratsashi tako Ina ajikinsa. Cike da shauqin kaunarta yakai bakinsa yayi kissing lips dinta Yana cewa" raguwa daka Dan tabaki Sai langwabewa mutane kama wacce ta Mutu" Sai kuma yayi murmushi Yana shafa lips dinta.. Yana cikin haka yaji an Tura qofan dasauri ya janye hannunsa a Kanta Yana Kallan kofan,,daddyne Sai mama suka shigo Dakin.. Sallamarsu ya amsa tare da Tashi tsaye ya Tura mama kujeran,,mama Bata Iya Zama ba ta tako Har zuwa bakin gadon tana kallan yadda nijlah Ke Jan numfashi ahankali.. Girgiza kai mama tayi ganin kankantan nijlah Amma Duk Da haka Yasmeen ta Iya zage kwanjinta Akan Yar karamar yarinyar" Addu'a mama ta Shiga tofa nijlah Bayan ta gama ta juyo tana kallan mashkur,, ahankali mama ta Bude baki tana cewa.. Dan Alhaji kuyi hakuri Da abinda ya faru" yarone yanzu ka haifeshi Baka haifi bakinsaba... Babu komai cewan daddy Yana murmushi" Sai Dai mu godema Allah tinda gashi yarinya da sauran kwananta a gaba" Hakane sedai Duk da haka Ina Mai Baku hakuri musamman ma kai mashkur sabida kai akayima" Kuma nizan jamata kunne,,Na tabbata Hakan Baze qara faruwa ba.. A ciki ciki Mashkur ya amsa Yana Kallan gefe Dan tinda suka shigo be Daga kai ya Kalli kowa ba.. Idan akwai abinda Ake buqata Sai a gayamin,,inaso zanje gida Na dawo,,inyaso Saina kwana a gurinta basai kun Gaya iyayen yarinyarba??? Bakomai Nima nijlah kyatace zanyi duk abinda ya dace cewar.. Dan risinawa mama tayi tana yiwa daddy godiya tare da cewa nizan wuce tea Na taho dashi Idan ta farka Sai a Bata.. Dasauri mashkur yace" ah ah kibarshi kawai mama hakama Mun gode basai kin dawo ba.. Jikin mama a sanyaye tace kana ganin ba matsala mashkur' kai tsaye mashkur yace eh babu.. Sallama mama tayi musu ta fita a Dakin jikinta Duk a sanyaye Duba da yadda mashkur yake amsata kama bayaso,,taso ace yabarta ta zauna da nijlah Dan tana ganin zatafi kowa Bata kulawa.. Tana fita daddy ya Hau Kan mashkur da fada ta inda yake Shiga batanan yake fitaba" shidai mashkur be Iya cewa komai ba Banda baqin ciki Babu abinda kecin ransa.. Kaima kanasan Zama mara Kunya kenan' Koka manta yarta kakesan aure" Amma tana Magana kana sa baki,,kokai Zaka zabi yadda za'a Kula da nijlah.. Ahankali mashkur ya girgiza kai Yana Kallan daddy,,Sai da daddy ya gama kafin mashkur ya Bude baki a hankali yace" Daddy nibanqi mama ta zauna da nijlah ba sedai daddy abinda Baze taba yiwuwa Kenan ba,,Ina tsoro Kar cikin dare Yasmeen ta qara zuwa inda nijlah take ta illatamin ita" Gafara can ka rufemin baki,,soqoqon banza kawai,,Ina da Rana tsaka ita Yasmeen tayimata haka,,Kuma a gabanka Baka Iya tsinana komai ba Sai aikin kuka,,ka kirani kagayamin kuna hospital Baka Iya ba Sai dr Jamil ne yagayamin yaganka anan kafin Na baro office nazo.. Turo baki mashkur yayi kama qaramin yaro yace' to daddy Yaya zanyi da ita nayi nayi ta dagata taqi" Kuma kake mana kazauna da ita anan Bayan bakasan yadda zakayi da itaba ita ta sake kawomata Hari? Daddy ya tambaya" Sosa kai mashkur yayi Yana cewa Hakan Bama zata sake faruwa ba insha Allah" To Allah yasa yanzu Sai muje a gwada jininka day nawa Dan likita yace da yiwuwar a qara Mata jini danta zubda

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46