Chapter 6
Chapter 6
zauna cikin matsiyatan mutane dako Nama Sai su shekara Basu Ciba,,to wallahi Bazan taba yadda ba gwara tin farko kasan yadda zakayi da danka.. Girgiza kai daddy yayi Yana Kallan mummy yace" yanzu Ke Khadija Harkin isa ki aibata Fulani kokin manta Nima bafulatani ne,, dasauri mummy tace Amma Dai ba irinsu ba. Cikin fishi daddy yace,Koma Dai menene jinin fulani kike aure Dan haka ki kyale yaro ya qarasa karatunsa Koma menene saikiyi Daga Baya,, Turo baki mummy tayi ta Tashi dasauri ta Koma daki tana Kiran babban danta.. Hello mummyna barka da yamma,,yauwa Ibrahim,,mummy lafiya Naji muryanki haka,, mummy Ko baki da lafiya ne,,kuka mummy tasa tana cewa.. Ibrahim ka Kira wannan yaran ka gayamasa ya dawo gida, mashkur Yana neman doramin hawan jini. Eyyah Mummy meya Samu mashkur din,, mummy Ko jiya munyi waya dashi yace Yana zaune lafiya a garin dayake" toka gayamasa ya dawo gida banasan zamansa cikin wadannan mutanan indai yanasan zamana dashi lafiya. Shikenan mummy kiyi hakuri zanyi Magana dashi,,eh ka gayamasa yayi saurin neman transfer yadawo cikin gari,,to mummy kiyi hakuri insha Allahu Ze dawo,,kashe wayan mummy tayi tare da sakin tsaki.. ******* Tinda Malam ya Tashi yasa a ransa Yau Ze Bada auren nijlah gako wanne irin mutum ne indai yanada kamala Kuma Ze Iya riqe nijlah.. Yakumbo ya Samu da maganan yayi sa'a Bata bashi matsala ba ta Kuma amince tare da Tarin adduointa ga auren jikar Tata. Comments &share *Momn sultan ce*✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN MUHAMMAD* 9⃣&1⃣0⃣ Tinda Malam ya fita be qara yiwa yakumbo maganar auren nijlah ba,gashi Yau Har anyi wata guda, Dan haka yakumbo ta garzaya zuwa gidan jummai dillaliya Akan tanaso Akai nijlah birni itama tayi aikatau kosa Samu su rage zafi. Dakyar jummai ta yadda Dan acewarta nijlah 'yar shagwabace su Kuma alhazan birni Basu San shagwababbun yara indai ba nasu bane,,Seda yakumbo ta Hada da ban hakuri tare da cewa zata jama nijlah kunne.. Nijlah Najin batin aiki tayi murna tare da cewa bazata yimusu rigima ba,,nan yakumbo ta Maida hankali gurin tafiyan nijlah birni aikatau.. Yau nijlah da farin ciki ta Tashi sabida ana bikin yayar kawarta,tinda safe ta tafi Suna party, yayinda Ake al'adu irin Na Fulani. Ke kikace kinaso amarya,,da bakyaso da ba'a Baki shiba,,haka 'yammata suka riqa wucewa suna rera waqa,,gefe guda manyan matane dauke da wata yarinya 'yar qarama bisa doki,,kawunan kowacce su dauke da kwalla da fanteka sai 'yan komatsan Kaya!!! Ta ko ina suke shigewa,, wasu gada cikinsu suna rangada guda ... Tsaki mashkur yaja Yana kallan abokan nasa da sukabi tawagar Yan Kai amarya da kallo,,, washe Baki Bello yayi Yana cewa kagani fa,, aure ya tabbata,, Allah yasanya alkairi,,duka sauran Suka amsa,da ameen Banda mashkur Daya hade giran Sama data qasa... Kai dallah Malam ware,idan zaka zabo yarinya a karkaran nan ka zaba,bamusan wannan miskilancin naka,, daba kaiwa zuci yayi ba.. Allah ya sawaqe,,ni duk garin nan babu yarinya data isa aura agurina,,Dan wallahi Basu Kai Mata ba,,Zan so kuje birni Kuga inda Mata suke,, hhhhh Bello ya fada Yana kallan mashkur.. Kai kujimin Dan rainin hankalin nan to idan ba Mata bane suwaye""' yauwa tambaya mana Shi cewan Nasir dake zuwa gurin... Kwailayene,, ko nayi karya,, gaba daya suka amsa da cewa kwarai ma kuwa.. Tabe Baki mashkur yayi Yana cewa,,Ku duba yarinyar nan indo, dududu shekaranta nawa Amma har Malam ya'u ya auran da ita? eh mana kuma Ka zuba ido nan da wata Tara zata iya haihuwa,, ai mu matanmu na karkara da iya zaman aure suke ba irin naku na birni ba.. Dariya mashkur yayi Yana Sosa Dan yafisu Sanin abinda yake Gaya,,sedai su bazasu gane hakan ba,,sabida nasu al'adan suka sani... Shirune ya ratsa gurin kafin Nasir yace,, to wai Kai mashkur dama ba soyayya kake da nizlah bah'' qayataccen murmushi mashkur yayi Yana Sosa Kai yace,, Ai nizlah kanwace agareni,,ina kuma yimata so Wanda bansan irinsaba,, dan da ace ta isa aure nizan aureta na kaita can birni itama ta waye,, Dariya suka sa suna kallan mashkur Wanda tinda aka ambaci sunan nizlah bakinsa yaqi rufuwa,,, Koma dai menene munsan kana San nizlah,, Dan shaguwarku da ita abin dubawa ne, Nasir ya fada Yana kallan Bello.. Dariya Bello yayi shiko mashkur ya zuba musu Ido Yana kallansu,, be iya magana ba sabida Jin Kiran sallah da yayi.. Ni kunga tafiyana,, kafin kumin wani fassara na daban,, atare suka tashi suna qara jandada masa abinda ke zuciyarsa... Sedai Shi Babu wannan a ransa soyayyar Yasmeen kawai yakeji,sedai Yana yiwa nijlah so irin Na tausayawa Amma Bada aure ba. ******************* Uhmn uhmn,, Allah ni saikin Bani biyar naje dandali,, yaushe raban daki Bani biyar dinki,, kodan kinga Dan birni Yana Bani,,kayya nijlah,, Nima Bani dashine,da inadashi Babu abinda Ze Hana ni baki.. Turo baki nijlah tayi tana kuka tare da birgima a qasa,, kayya mezan gani haka sukaji Malam ya fada,,yakumbo kodai Wani Abu kikayiwa yarinyar nan.. Kai madai Malam Sai kace bakasan halin nijlah ba,, wannan kukan daka ga tanayi Bana komai bane illah Na naira biyar,, ita adole Saina Bata biyar ta kashe,Nace Bani dashi ta kwanta tana birgima,,kaga Idan kayan jikinta yayi datti Sai Muga inda Zan samu kudin sabulun wanki.. Girgiza kai malam yayi Bayan yagama Jin bayanin yakumbo,,nijlah Ko Bata daina birgima ba Dan Har tirken dabobi ta kai tanayi... Ahankali Malam ya taka ya isa Har inda take ya kamo hannunta"ba musu ta tashi tana turo baki,,kiyi hakuri kinji nijlah ta,,gobe Idan Allah ya kaimu naira Goma Zan baki kije dandali kisai Duk abinda kikeso.. Kawu dagaske kake,,nijlah ta fada tana kallan bakinshi,, kai nijlah meyasa wayenki yayi yawa,,kin tabaji Malam yayi Karya??sukaji yakumbo na tambaya.. Shiru nizlah tayi tana girgiza kai,,Sai kuma tace,,Naga yataba cewa Nima za'a kaini birni nayi aiki irin na jummai,Amma haryanzu be kaini ba,,Kuma Naga hajiyar tana zuwa... Bata rai Malam yayi yace,kinga nijlah banasan shirme,,kima ajiye wannan maganar Babu ita,,haba Malam ya zakayi haka,,zuwa aikin nizlah shine cigabanmu,,kana Dai kallo abinda zamu kai bakinmu,,wahala yake mana.. Yakumbo,,Malam ya Kira sunanata Har sau uku,,amsawa tayi tana kallansa,,kisani Daga Yau nafasa kai nijlah aiki,,auran da ita zanyi.. Zaro Ido yakumbo tayi tana kallan nijlah,da tinda aka Kira aure tafara rawa tana juyi,,bakin yakumbo na rawa tace Malam aure fa kace,nawa shekarun nijlah,,yake,saifa gambon wata take shekara Goma.. Ni wallahi nayi tinanin ka janye wannan maganar danaji kwana biyu Baka qara yiba. Eh, nasani,Naga Dai ba haramun bane,,damu zauna da ita,cikin wahala Ai gwara taje can gidan mijinta Kota samu ladan aure,, wannan wanne irin ladane,,nijlah fa Ko wanke wanke Bata Iya sosaiba,,balle azo maganan gyaran gida,,nidai kayi hakuri a kaita gidan aiki hakan zefimin kwanciyarsa hankali... Hmm Ni kinga tafiyana,, Naji an tada Sallah,,fita Malam yayi yabar nijlah Na rawa tana cewa yakumbo Nima Zaki saimin wannan abun da Ake dafa tuwo.. Ke dallah rufemin baki,ki Kuma Dena wannan rawan kan,,Ko an gayamiki auren Cin tuwo ne,, fari nijlah tayima yakumbo tana cewa,,eh mana nidai gwara akaini gidana,,nasan Ko Goma Zan riqa samu Ina zuwa dandali,, Acan masallaci Bayan an idar da Sallah Malam ya matsa kusa da Liman ya gayamasa Magana a hankali,, murmushi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46