Skip to content

Chapter 43

Chapter 43

Yar Sadaka Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

ba Sai Daga masa kai tayi tana goge hawayen fuskanta'. Nijlah kisani banayin wannan abun abida Na Bata ranki sedai soyayya da tsantsar kaunata gareki' nijlah ita soyayya zurfine da ita ga Kuma fadi,,sedai bazaki fahimci Hakan ba Sai nan ba.. To to Nika sakeni' bakaji ana buga kofan ba' nijlah ta fada a shagwabe. Mummy Ko Banda Kiran mashkur Babu abinda take tana buga qofan Dakin da Iya qarfinta, yayinda takejin baqin ciki Na ruruwa a cikin zuciyanta... Ka sakeni ka Bude kofan kaji' nijlah ta fada a hankali' be Iya tashiba Saima kafeta da yayi da tsummamun idanunsa Wanda ya canza Kala Daga fari zuwa ja' sabida tsabar tashin hankalin dayake ciki. Sai da yayi kusan minti 3 ahaka kafin yayi yaqi da zuciyarsa ya Tashi a hankali ya safka Daga Kan gadon Yana kallanta' kasa kallan idanshi nijlah tayi sabida tsabar Kunya nan ta fara gyara riganta tana San zubda hawaye' Dasauri mashkur yace' shhhhhhiiiitttt Karki soma hawaye kinga Dai mummy na jirana. Zaro Ido nijlah tayi tace baba fa kace' wayyo Allah Na kado wallahi dukana zatayi kaga saita zube Akan bed tana neman inda zata buya' Duk da halin da mashkur Ke ciki Saida yayi murmushi. Kinga jeki Shiga toilet Karki Bude indai Bani Nace ki Bude ba kinji' Bata Iya amshiba ta kwasa a guje ta fada jikin toilet da zaninta a hannu,,tana Shiga tasa key ta ciki ta kulle jikinta Na rawa sabida tsabar tashin hankali.. A hankali mashkur ya soma takowa zuwa jikin kofan tamkar Wanda egg ya fashewa a ciki' hannunsa Na rawa yafasa zare key. Haryanzu mummy Bata Dena fadaba tana Kiran sunansa ahaka harya gama Bude qofan ya sauke idonshi ana mummy. Tsaye take a falon tana sababi kama Wanda aka bama gasar Cin kofin duniya' Ai tana ganin ya Bude tayi cikin Dakin Ranta a bace tana huci kama kububuwa' Ke kina Ina Dan ubanki ki fito Nace wallahi Yau sainayi maganinki 'Yar masu yawan Jeje da bakin halin tsiya wallahi Baku isaba kurwan Dana tafi karfinku matsiyata banza matsiyatan Wofi kina Ina mummy ta fada cikin ihu da amsa kuwwa, kai kace da sa'arta take fada. Jikin nijlah ne ya dauka rawa Amma Duk Da haka Bata zauna ba Saida ta tashi ta zo jikin kofan tasa jikinta ta qara turawa yayinda bakinta be bar ambatan Sunan Allah da neman dauki a gurinshi ba.. Sai yanzu take danasanin Qin bin hajiya Khadija da tayi. Sosai mummy ta Shiga zagaye Dakin tana neman nijlah Amma Bata gantaba. Takowa mashkur yayi harya qaraso inda mummy Ke tsaye yasa hannu ya riqe nata Yana Magana a hankali' mummy Wai Wa kike nema nifa kadaine a dakinnan Babu kowa.. Be kai Ida maganar ba mummy ta Daga hannu cikin fishi zata daukeshi da Mari' Dasauri mashkur ya rufe idansa Dan Baze Iya kallan wannan baqar ranar ba sedai jin Shiru yasashi budewa idon a hankali,, itama mummy sauke hannunta tayi Dan bazata taba Iya Marin autan nata ba ta zuba masa Ido cike da bacin Rai.. Mummy kiyi Allah Dan Allah' mummy kidena Daga hankalinki wallahi Babu abinda nakeso fiye da ganin farin cikin ki da kwanciyar hankalinki,,mummy Idan kina irin wannan tashin hankali Zaki dorawa kanki hawan jini kisa mu Shiga uku. Kaine Zaka doramin hawan jini auta, Sau nawa Zan gayamaka banasan tarayyarka da kusanci ka da wannan aljanar yarinyar? Cikin sanyin murya yace mummy wacce yarinya kike magana? Nijlah nake Magana Ko kanaso kace Bata cikin. Dakin nan? Bakinsa da rawa yace mummy batanan fa tana... Tana gidan ubanka ko? Kayimin Shiru,,wallahi ka qarasa Magana tam Dinka. tana Ina Ko kanaso kace ba ita Naji kuka yanzu ba, wato kai Har Zaman aure kakeyi da ita Ko? Kasa ya safke idonsa Yana cewa' eyyah Mummy bafa haka bane laifi tayimin shine na duketa kikaji kukanta yanzuma dakyar ta Samu Na saketa shine ta boye, mashkur ya qare maganar cikin rashin gaskiya. A Ina ta Boye Naga Dai ba kofan fita ta Baya? Mummy bansani bafa,, Dan Allah muje ki zauna kibar tada hankalinki akanta. To Ya kakeso nayi da rayuwata mashkur? Kodan kaga Na Dora soyayyana akanka shiyasa zakesan Bani wahala? Ah ah mummy inaso ne Dai ki fahimceni' mummy nijlah Amana aka Bani ita,Kuma matatace ta Sunna Na tabbata Idan Na zalinceta Sai Allah ya sakamata gashi marainiyace. Kayimin Shiru Ko yaya,,Sai anyi Magana kace marainiya marainiya, shin ni Ina nawa iyayen Ko ita kadai kake tausai? Ah ah Mummy nidai ki zauna Ko lemo kisha. Anqi a zauna' kaga mashkur ka kiyayeni, wallahi matuqar kanasan farin ciki saika Maida yarinyarnan garinsu'' Shidai beyi Magana ba Yaja hannunta suka zauna kan daya Daga cikin kujerun dake ajiye a falon' Tashi yayi ya kunna TV tare da daukomata ruwa da lemo masu sanyi yafara tsiyaya Mata a cup. Mummy amsa wannan Kisha nasan kin debo rana? Amsa mummy tayi tafara sha tana hararansa,,shidai mashkur hakuri kawai yake bata harta gama sha ta tashi tsaye tana cewa' Jeka nemomin ita aduk inda ta Shiga Dan wallahi Bazan barta nan ba tazo tana samaka damuwa kaga saura 3 days afara bikin nan kada azo aganka a rame Dan wannan Har jini zata Iya tsotsema.. Zaro Ido yayi cike da tashin hankali yace' mummy kibarta anan Duka zata sha Nifa Ko abincin kirki ba Bata Nike ba shiyasa kikaga ban damu da zamanta anan ba.. Ah ah Dai auta jeka kawomin ita ,,Dan gaskiya hankali Na Baze kwanta ba indai wannan ja' irar tana tare da kai.. Magana zeyi mummy ta katseshi' kaje Nace Ko. Babu yadda ya Iya haka ya Shiga Dakin Yana Kiran nijlah.zuciyansa na quna. Nijlah ki Bude nine fa, tana budewa ta saki kuka tana cewa honey ta tafi Ko? Bata tafi ba,, kinga abinda taurin kanki Yaja Miki Ko nijlah gashinan mummy tace dake zata tafi.. Wani irin takaici da haushine suka cikata tare da Dana Sani mara amfani' nan ta fara hawaye tana cewa' kado Dan Allah kace aunty Khadija ta dawo Allah Zan bita,, wallahi Bazan qara yimata musu ba,,nadena Allah nadena Nijlah ta fada cikin kuka da tausayama Kanta.. Janyota jikinshi yayi Yana cewa' kiyi hakuri Nida kaina zansa a satoki a hannun mummy kedai kawai kiyi biyayya ki bita ki Kuma Nuna Mata bakyasan Zama dani kinji? Cike da sallamawa farin ciki nijlah ta dagamasa Mai tana goge hawayen fuskanta da gefen rigarta tace' shikenan tinda haka kace, Amma tayaya za'a Iya satoni a wannan gidan naku,, nidai kawai kace mutuwa zanyi.. Kije kawai yafada yana Dagamata kai nan suka fito tare,, hankada qeyarta mummy tayi tana cewa wuce muje dangin Hau irin masifa Wanda Basu San komaiba Sai yawo a dawa. Nijlah Na kuka suka fita ahaka ta sata cikin Mota ta juyo inda mashkur yake tana cewa. Kai auta ka Kula da kanka Nina tafi sabida Yau inada manyan baki' Cikin Dakiya da nuna rashin damuwa mashkur yace' mummy wasu irin baqi kuma? Wallahi su linda ne zasu zo wadannan nake aikin a NGOs dasu na Hada musu liyafa ta gani ta fada fatan kaima Zaka zo ayi Taran dakai, tinda jiya nake nemanka Sai yanzu danazo da kaina Na ganka. Murmushi mashkur yayi Danya Samu hanyar ganin nijlah' ya

Table of Contents

Chapters

46 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46