Chapter 27
Chapter 27
qara shafe fuskanta da powder ta yasha mayafi ta fito tana tafiya a hankali.. Me aikinsu ta riqa kwala Kira,,dasauri ta fito tana risinawa tace aunty gani.. kingama hada kayan abincin Dana saki,,eh angama suna can falo anshirya komai.. Yasmeen bata qara magana ba ta koma daki ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi,,dakin mama ta dawo tana cewa mama Zan shigo dashi.. ke da Baki shigo dashi tin dazu ba,, murmushi Yasmeen tayi tana boye fuska tace mama ina yimasa kwalliya.. Ke dai Allah ya shiryeki,,Bako kunya kike Bani amsa Yasmeen,,cikin dariya Yasmeen ta fita tana murnar ganin angon nata... Turus tayi ganinshi cikin mota hannunsa riqe Dana nijlah suna magana' Wani irin yawu ta hadiye me dacin gaske tana tambayar kanta.. Wacece kuma wannan me kama da 'ya'yan larabawa,,to kodai 'ya'yan yayyensane,,Kai ah ah baby be taba zuwa da wani yaro nan ba,,Kai Bama ze Zama sune ba Dan su Bama a qasar suke zaune ba.. To wacece wannan ta sake tambayar kanta" ganin hannunsu sarqe Dana juna yasata saurin qarawa jikin motar tana cewa kambu lallai yau akwai bala'i,,tana Gama fadar tafara qoqarin bude motar da dukan qarfinta,,Banda rawa babu abinda jikinta yake,duk Wanda yaganta yasan bata cikin nutsuwarta"sosai zuciyarta ke bugawa da qarfin gaske,ta dauka aniya a ranta komai zai faru sedai ya faru Amma yau ko ita ko wannan yarinyar me suffar aljanu.. Wallahi yau Sena Baka mamaki baby .. A firgice mashkur ya janye hannunsa daga na nijlah ya qaqalo murmushin dole Yana aika Mata,, bude kofan yayi Yana cewa amarya" Dole kace amarya mana'kaga baby ni duk ba wannan ba,,wacece wannan da har kake riqe Mata hannun ta fada cikin tashin hankali da zafin zuciya tana nufo inda nijlah take.. Dasauri yasa hannu ya tare ta Yana cewa" haba Yasmeen meyasa zafin kishinki yayi yawa" kifa rage ina gayamiki.. Cikin fishi tace dole zakace Kaka sabida kaci amanata Ka yaudareni da soyayayarka,,Amma duk da haka na amince da aurenka shine zaka nunamin Bani kadai kakesoba.. Kidai nutsu Saina gayamiki ko wacece" Ka gayamin yanzu indai baso kake zuciyana ta Gama bugawa yanzu ba.. Matsowa yayi kusa da ita sosai had suna jin numfashin juna da bugun zuciyar kowannesu yace"hannunta ya kama cikin masa ya riqe sosai Yana shafawa duk Dan yasamu ta dawo cikin hayyacinta da nutsuwarta,,Amma duk da haka taqi tsayuwa burinta kawai taji kowacece kafin tasan hukuncin dazata yanke akanta.. Cike da tashin hankali yake magana Yana kallan Yadda nijlah ta rikice ta gigice ta kidime tana kankame jikinta hawaye tuni sun wanke Mata fuska Banda karkarwa babu abinda take tana Kiran sunan Allah" Yace,,pls Yasmeen ki saurareni,,kinfasan da kaunarki na rayu, kuma haryanzu kina cikin zuciya na babu abinda ya chanzaki" to meyasa kike yiwa babynki haka,, wannan yarinyar kanwatace ki nutsu mana.. Ganin taqi nutsuwa sai zufa take yasashi juyawa inda nijlah take zauna yace" Nijlah ki gayamata koke ba kanwat.... Be iya qarasawa ba sabida ganin nijlah kwance a qasa Yasmeen ta hau kanta tana Duka.. Bane ni zaka yaudara ko an gayama bansan sunan *'yar sadaka* nijlah ba,,zaka ha'inceni" to wallahi yau koni ko wannan tsinanniyar yarinyar,, Dama akan wannan kake wulaqantani... Kukama nijlah kasawa tayi Banda Ido babu abinda take rabawa" ta ko ina Yasmeen ke dukanta har Saida numfashin nijlah yafara sarqewa.. Duk Yadda mashkur yayi Dan ganin ya kwaci nijlah ya kasa Dan ba ruqon Wasa Yasmeen tayi Mata ba,,tana dukanta tana surutai.. Rasa inda mashkur zesa ransa yayi Banda tashin hankali da firgice babu abinda yake ji" waiwaye ya riqayi koze Samu Wanda ze ceci nijlah ya Rasa,,sabida layin ba mutane indai ba lokacin sallah yayi kaga suna fitowa ba.. Dabarace ta fadowa mashkur yafara kwalama get man Kira Dan Shi kadai ze iya jinsu adaidai wannan lokacin.. Me gadi na zaune jikin get yasa radio a kunannsa Yana sauraran wani shiri inda yaji labarin governor ganduje ya tsige sarkin Kano Muhammad sinusi ya Dora hannu aka Yana salati,,hakan ne ya hanashi Jin kiranda mashkur ke masa. Cikin zafin Rai mashkur yayi Kan Yasmeen da Duka ganin Yadda jini ke fita ta Baki ta hanci a jikin nijlah,,Amma Duk da haka yasmeen Bata dena Dukan taba haka Kuma bakinta beyi Shiru ba.. Wallahi Ko Zaka kasheni Saina fara kashe wannan abun tsiyar Idan yaso Sai kayi abinda zakayi.. Yana hawaye yace" shikenan Ai kin kasheta saiki dagata,,kaicona Ni mashkur Dana kasa riqe amanar Dana dauka Yasmeen baki kyautamin ba,,ki dagata Nace kafin nayi qasa qasa dake yanzu.. Ganin yadda hawaye Ke fita a idanshi yasa Yasmeen Tashi Akan nijlah bakinta Na rawa tace" Baby kuka kake akan Na Daki wannan yarinyar" me Zan gani Ni Yasmeen Sai kuma ta fashe da kuka ta Shiga cikin gida da gudu tana yarfe hannu,,jikin rigarta da hannunta Duka jini ya Bata.. Tana Shiga me Gadi ya yarda radio yayi Kanta yana tambaya,,kallan waje yayi yaga motan mashkur,,dasauri ya fito Yana tambayan yallabai lafiya.. Chak numfashin mashkur ya tsaya ya Dena aiki,fa gudu yayi kan nijlah Yana kuka saikace qarami n yaro ya tattarota jikinsa Yana jinjigata tare da Kiran sunanta,,jikin Na kyarma ya saketa Yana salati.. Daidai lokacin get man ya qaraso Yana cewa yallabai lafiya" ganin mace kwance Bata numfashi yasa qarasawa Yana matsa hancinta.. Baba ta Mutu Ko,, shikenan Yasmeen kin gama da rayuwana,, nijlah naso ki girma naga yaranmu dake,,naso kema ki dandana rayuwa ta Jin Dadi Sai gashi kin rigamu gidan gaskiya" Sai kuma ya chakumi wayan rigar baba me Gadi Yana cewa, Dan Allah ka dubamin ita Bata Mutu ba Ko?? Girgiza kai baba me Gadi yayi Dan yariga ya tabbata da mutuwar nijlah sedai Baze Iya gayaba sabida Shima mashkur yaga Hakan.. Baba me gadine yayi qoqarin Tashi Ze ciccibi nijlah yasata a Mota Domin aje ayi jana'izarta. Mashkur yayi saurin Shan gabansa Yana cewa karka taba ta,,nizan sata a Mota da hannuna,,Allah yajiqanki Nijlah,,wayyo Ni mashkur wannan wacce irin ranace na riska.. Yana kuka yasata a Mota ya nufi hospital da ita,,nan likitoci suka Hau Kan Dan ceto rayuwarta,,seda sukayi kusan 30 minutes akanta kafin Naga daya Daga cikinsu yajamata mayafi ya rufe fuskanta.. Jikinsu a sanyaye suka fito. DA gudu mashkur yayi kansu Yana cewa likita Yaya Bata Mutu ba Ko? Shafa kansa dr yayi Yana cewa kayi hakuri mashkur... Be Bari yaqaraji ba ya fizge hannunsa ya Shiga Dakin,,direct Kan gadon da nijlah Ke kwance yace ya Bude ta.. Wani ihu ya saki ganin hancinta da kunnata rufe da adduga,, haryanzu jini bai Dena zuba ba.. Salati ta kurma Yana neman daidaita nutsuwarsa,,sedai be samu damar Hakan ba yayi Baya luuuuuuuu...... Idan kuka qara comments irin Na jiya,Bazan qara posting ba Sai Bayan Sallah Idan Allah yasa muna da raban gani.. Dan Allah ku riqa sharing danayi posting,,banaso ana damuna Akan Na turo,,abin dayawa Idan Na biyeku Bazan Samu lokacin kaina ba.. *Momn sultan ce*✍✍✍✍ 💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘 *STORY & WRITING BY...* *BY* *MOMN SULTAN* *DEDICATED TO.....* *MMN AMATULLAH* *SPECIAL GIFT TO...* *MMN FAREESAH....* 4⃣1⃣&4⃣2⃣ Yayi Baya luuuuuuuu,, dasauri sauran likitocin dake tsaye sukayi nasaran tare sa Suna salati.. Taimakon gaggawa suka Shiga bashi,,cikin Ikon Allah suka Sami damar dawa masa da numfashinsa,,sedai Yana farkawa ya dafe kai Yana hawaye.. Ruwan da aka dauramasa ya fizge tare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46